MAGANIN BASIR Ciwan Basir Kala Kala ne Sannan kowanne da maganin sa, abin da mafi yawan Mutane basu gane ba shine da zarar Mutum ya fuskanci wannan larura sai kaji yana cewa a bashi maganin basir ba tare da tantance irin wanda yake fama da shi ba, Saboda haka yana da kyau mu rinka bancewa dan gudu shan magani daban cuta daban, Allah yasa mu dace. Ga Wasu cikin rabe raben sa, 1. Akwai basir mai Sanya Kumburin Ciki, 2. Akwai Wanda yake Sanya kaikayin dubura ko matse matsin Mutum, 3. Akwai mai Sanya Atini wani lokacin har da jini, 4. Akwai Wanda yake Sanya Rashin Kuzari da Kan-kancewar al aura, 5. Akwai mai Sanya fitar baya, ************************************* 1. Basir mai sanya Kumburin ciki, Idan mutum yana yawan fama da kumburin ciki ko yawan magwas, da daurewar mara ga mata Sai a sami abubuwa kamar haka: a. Danyen Zogale, b. Saiwar Ararrabi, c. Jar Kanwa, A hada a rinka tafasawa ana sha, Za'a semi lafiya Insha Allah.
Karatuttukan addinin musulunci da harshen Hausa