*NUKHBATUL FIKR FI MUSƊAHI AHLIL ATHAR 03*
Hadisi maƙbuuli yakan fa'idantar da ilimi na nazari a maganar da tafi wajen malamai.
Sannan sai hadisi gareebi, zata iya kasancewa a tushen isnadi ku kuma sabanin haka.
Na farko shi ne Alfardul Muɗlaƙ, na biyun shi ne Alfardul nisbiy.
Sharuddan Ingancin Hadeethi Aahaad
1. عدل الراوي: Adalcin mai riwaya
2. ضبط الراوي: Cikar haddar mai riwaya
3. اتصال السند: Haduwar isanadi
4. خلوه من الشذوذ :Kubutarsa daga sabama sauran
5. خلوه من العللة: Kubutarsa daga aibi boyayye.
Duk hadisin da ya cika sharuddan nan guda biyar shi ake cema Cikakken ingantaceصحيح لذاته.
A cikin nau'insa wank yafi wani daraja gwargwadon wanda yafi kiyaye sharuddan da kyau. Tuntuni ana gabatar da Saheehul Bukhaari, sai Muslim, sai wanda yazo bisa sharadinsu amma basu fitar dashi ba.
In hadisi yazo daga wanda haddarsa bata cika ba, ana kiran hadisin da cikakken hadisi mai kyau الحسن لذاته.
In irin wannan yazo ta hanyoyi da yawa, ana kiransa Ingantacce da haduwa da wasunsa صحيح لغيره.
A dunqule mun koyi naukan hadisi kamar haka
Alfardul mudalaq
Alfatdun nisby
Saheeh lizatihi
Saheeh Ligairihi
Hasanun Lizatihi
Anan zamu dakata sai kuma darasi na gaba InshaAllah.
NUKBATUL FIKR
Na ibn Hajr Al-asqalaniy
Gabatarwa: Abu Isma'il
Markazul Wa'ayil Islamiy Tudun Jukun Zaria
Ramadan Daura. 3/9/1441- 26/4/2020
Comments
Post a Comment