*NUKHBATUL FIKR FI MUSƊAHI AHLIL ATHAR 04*
*قول الترمذي : حسن صحيح*
*Lafazin da Tirmidhi yake cewa Hasanun Saheehun*
Idan aka hada Lafazin guda biyu(حسن صحيح).
Ko dai mai ruwaya yana shakka ne(Kodai hadisin ya zama Hasanun ko ya zama Saheehi)
ko kuma ya lura da isnadi biyu ne (Isnadi ɗaya Hasan ne isnadi ɗayan kuma Saheehi).
*زيادة راويهما مقبولة مالم تقع منافية لمن هو أوثق*
*Ziyadul Thiƙah(ƙarin Amintacce a hadisi)*
Idan yayi ƙari ana karɓan ƙarin matuƙar bai sabama wanda ya fishi ba ana karɓa.
Hadisin wanda yafi aminci (الثقة)sunansa ALMAHFUUZ (المحفوظ), shi kuma na wanda aka fi shi ake kira SHAZHI (الشاذ).
Idan kuma mai rauni ya saɓa mawa ana kiran na amintaccen MA'ARUF (المعروف)shi kuma na mai raunin sunansa MUNKAR (المنكر).
*Mutaba'ah:* Bibikon hanyoyin hadisai domin a samo ma hadisin FARD wanda zai goya masa baya.
In aka samu FARD NISBY ya samu irinsa yana goyon bayansa shi ake kira TABI'I (التابع). in kuma matani aka sama wanda yake kama dashi ana kiran sa SHAHID (الشاهد).
Mutaba'ah: A samo hadisi yana kama da wani a lafazi da ma'ana.
Mushahadah: A samo hadisi yana kama da wani a lafazi banda ma'ana.
Bincike domin a gano haka, shi ake kira I'itibari (الإعتبار).
Yau mun koyi Musɗalat:
1. Hasanun Saheehun
2. Mahfuuz
3. Shaazh
4.Ma'aruf
5. Munkar
6. I 'itabaar
7. Mutaba' ah
8. Mushahadah
Nukbatul fikr na ibn Hajr
Gabatarwa: Abu Ismail
Markazul Wa'ayil Islamiy
Tudun Jukun Zaria
Ramadan Daura
5/9/1441- 28/4/2020
Comments
Post a Comment