*NUKHBATUL FIKR FI MUSƊAHI AHLIL ATHAR 09*
A yau mun san musɗalat kamar haka :
1. *Almarfu'u (المرفوع)*: Shi ne duk abin da aka danganta zuwa ga Annabi SAW na magana ko aiki ko tabbatar wa.
2. *Almauƙuuf(الموقوف)*:Shi ne duk abin da aka danganta zuwa ga Sahabi na magana ko aikinsa.
3. *Almaƙduu'u (المقطوع)*: Shi ne duk abin da aka danganta zuwa ga Tabi'i na magana ko aiki.
ANA KIRIN MAUƘUF DA MAƘDU' ATHAR
4. *Almusnad(المسند)*: Shi ne hadisin da ya dangane ga Annabi SAW ba tare da yankewar isnadi ba.
5. *Al'aaliy- Al'luwwul Muɗlaƙ (العالي:العلو المطلق)* : Shi ne hadisi ya zo da mutane yan kaɗan in an gwada shi da wani wanda bashi ba.
6. *Al-aaliy Al'luwwul Nisbiy(العالي: العلو النسبي)*: Shi ne hadisin da ya zo da mutane kaɗan, zuwa ga ɗaya daga cikin manya malaman hadisi kamar shu'ubah.
ULUWWUN NISBIY YA KASU GIDA GIDA
7. *Almuwafaƙah(الموافقة)*: Shi ne Isnadin mutum Y kai ga malamin ɗaya daga cikin malaman da suka rubuta littafin hadisi, kamar Bukhari ko Muslim d.s
8. *Albadalu(البدل)*: Shi ne kaiwa ga malamin malamin ɗaya daga cikin marubutan.
9. *Almusawah(المساواة)*: Shi ne daidaiton adadin isnadi dana ɗaya daga cikin marubuta. Misali Tsanin Bukhari zuwa Annabi mutum 6 ne sai Shima wani ya samo isnadi mai mutane 6 a hadisi iri ɗaya.
10. *Almusafahah(المصافحة)*: Shi ne zuwa adadin Isnadi daidai da dalibin ɗaya daga cikin marubutan.
11. *Annazil(النازل)*: Shi ne kishiya Aaliy, wato hadisin daya zo da mutane da yawa a isnadinsa in an gwada shi da wani wanda matanin su ɗaya ne.
Nb. Ba a samun Aaliy da Naazil sai in suna da matani irin ɗaya sai ɗaya yafi mutane da yawa. Mai kaɗan shi ne Aaliy, mai yawa shi ne Naazil.
12. *Riwayatul Aƙran(رواية الأقران)* : Shi ne ɗalibi yayi karatu wajen ɗanuwansa ɗalibi.
13. *Almudabbaj(المدبج)*: Shi ne ɗalibai guda biyu kowa yayi karatu wajen kowa.
Nukhbah Na Ibn Hajr
Gabatarwa: Abu Isma'il
Markazul Wa'ayil Islamiy
Tudun Jukun Zaria
Ramadan Daura
10/8/1441-3/5/2020
Comments
Post a Comment