*NUKHBATUL FIKR FI MUSƊAHI AHLIL ATHAR 08*
A yau mun san musɗalat kamar haka:
1. *Majhulul Ayn(مجهول العين)*: Shi ne wanda mai riwaya guda ɗaya kawai ya ruwaito shi.
2. *Majhulul haal(مجهول الحال)*: Shi ne wanda mutane biyu ko fiye da haka suka yi riwaya a wajensa. Amma ba a ce amintacce ne a karɓi riwayarsa ba kuma shi ake cema Almastuur.
3. *Mai bidi'ah mufassiqa(المبتدع بدعة مفسقة)*: Shi ne mai riwaya ɗan bidi'ah amma bidi'ar da ke maida mutum mai saɓo. Malamai sunce ana iya karɓar hadisin sa matuƙar bai ruwaito abinda ke ƙarfafa bidi'arsa.
4. *Mai bidi'ah mukaffira(المبتدع بدعة مكفرو):* Shi ne mai riwaya ɗan bidi'a wacce ke maida mai ita kafiri. Kamar bidi'ar cewa ƙur'ani halitta ne. Jumhurun malamai sun tafi akan cewa ba a karɓan riwayarsa haka Juzajaaniy malamin Nasa'i ya faɗa.
5. *Shaaz(الشاذ):* Riwayar mai mummunar hadda, a wajen wasu malamai.
6. *Mukhtaliɗ(المختلط):* Wanda lalacewar haddarsa bijiro wa tayi kamar saboda tsufa ko wata lalura.
7. *Hasanun lagairi(حسن لغيره):* Shi ne lokacin da aka samo ma mai hadda mai rauni riwayar mara rauni ta ƙarfafeshi , ko riwayar mastuuri, ko mursali ko mudallisi.
*Sannan isnadi yakan tuƙe ga Annabi S.A.W kai tsaye ko kuma a hukunce. Daga maganarsa ko aikinsa ko tabbatarwarsa.*
Kai tsaye Shine danganta zuwa ga Annabi
Hukunce: Shi ne Sahabi ya faɗi magana yace haka ake yi a zamanin Annabi S.A.W
Ko a danganta magana zuwa ga Sahabi.
8. *Sahabi(الصحابي):* Shi ne wanda yayi zamani da Annabi S.A.W kuma yayi imani dashi sannan ya mutu a musulunci koda ya taɓayin ridda bayan musuluncinsa.
Ko aka danganta zuwa ga Tabi'i
9. *Tabi'i التبع*: Shi ne wanda yayi zamani da Sahabi yana mai Imani da Annabi S.A.W kuma ya mutu a cikin musulunci.
Nukhba ta Ibn Hajr
Gabatarwa: Abu Isma'il
Markazul Wa'ayil Islamiy Tudun Jukun Zaria
9/8/1441- 2/5/2020
Comments
Post a Comment