*NUKHBATUL FIKR FI MUSƊAHI AHLIL ATHAR 05*
A yau zamu san musɗalat kamar haka:
1. *Al-muhkam(المحكم):* Shi ne hadisi ingantacce da ba wanda ya inganta yake cin karo dashi.
2. *Mukhtaliful hadis(مختلف الحديث):* Su ne hadisan da suke cin karo da juna a zahiri amma za a iya haɗa kansu ayi aiki dasu.
3. *Nasikh da Mansukh(الناسخ و المنسوخ):* Su ne hadisai guda biyu su ke cin karo da juna. Amma ɗaya na goge hukuncin ɗayan. Wanda aka fara faɗa shi ne Mansukh wanda aka faɗa daga baya shi ne Nasikh.
4. *Attarjeeh(الترجيح):* Shi ne a lokacin da hadisai suke cin karo da juna kuma ba a gano wanda ya goge wani ba. Sai abi wasu qa'idoji domin rinjayar da wanda yafi ayi aiki dashi.
5. *Tawaqqufi(التوقف):* Shi ne a daka game da aiki da wasu hadisai lokacin da aka kasa gane wanda ya goge waniba. Kuma anbi qa'idoji na tarjeehi ba a samu yadda za ayi tarjeehinsa ba.
6. *Mu'allaq(المعلق):* shi ne hadisin da aka share isnadinsa daga farko ko kuma gaba dayansa aka ambaci Sahabi kawai.
7. *Mursali(المرسل):* Shi ne hadisin da aka cire Sahabi a isnadinsa. Ya zama daga tabi'i sai aka ambaci Annabi S.A.W
8. *Mu'udal(المعضل):* Shi ne hadisin da aka cire mutane biyu ko fiye da haka a jere a isnadinsa ba a farko ba ba a qarshe ba.
9. *Munƙadi'i(المنقطع)* : Shi ne hadisin da aka cire mutum ɗaya ko fiye da haka, ba a farkon isnadinsa ba a a ƙarshe ba.
Nukbatul Fikr na Ibn Hajr
Gabatarwa: Abu Isma'il
Markazul Wa'ayil Islamiy Tudun Jukun Zaria
6/9/1441- 29/8/2020
Comments
Post a Comment