*NUKHBATUL FIKR FI MUSDALAHI AHLIL ATHAR 02*
Muqaddimah: Yabo ya tabbata ga Allah da bai gusheba masani kuma mai iko. Allah yayi salati da aminci ga shugaban talikai S.A.W da alayensa da sahabbansa da wanda suka bisu da kyautatawa.
Bayan haka, lalle rubuce rubuce a fannin Musdalahul hadeeth sun yawaita. Wasu sun fada, wasu kuma sun yawaita, wasu rubutun zube wasu a waqe. Daya daga cikin dalibai ya nemi da in rairayo masu wasu muhimman abubuwa daga cikin wanann ilimi. Sai na amsa ma roqonsa da fatan za a amfana.
*Hadisi yana zuwa da ma'anoni guda hudu (الحديث ،السنة،الأثر،الخبر،النبأ)Duka ma'anarsu a dunqule yana nufin abinda aka danganta zuwaga Annabi S.A.W na magana ko aiki ko tabbatarwa.*
Hadisi yana kasancewa kodai mutanen da ba adadi su ruwai to shi, ku mutane uku su ruwaito ko biyu, ko kuma mutum daya ya ruwaito shi.
A. Wanda mutane suka ruwaito da yawa shi ake kira *ALMUTAWATIR المتواتر:* Shi ne hadisin da mutane da yawa suka ruwaito yawansu ya wuce su hada baki suyi qarya. Ya kasu gida biyu(اللفظي و المعنوي). Misali: من كذب علي متعمدا فليتبوء مقعده من النار. Wanann hadisin an ruwaito shi daga sahabbai saba'in da wani abu. Yana da sharudda. Kuma yana fa'idantar da ilimin yaqini.
B. Wanda mutane uku suka ruwaito. Shi ake cema *ALMASH HUUR المشهور* An kirashi mash huuri saboda yadda ya shara a bakin mutane. Misalinsa: من دل على خير فله مثل أجر فاعله.
Wasu suna kiransa da Almustafeed.
C. Wanda mutane biyu suka ruwaito: Shi kuma sunanshi *ALAZEEZ العزيز* Kuma ba sharadi bane kafin hadisi ya inganta sai mutane biyu sun ruwaito shi. Misali: لا يؤمن أحدكم حتى أكون أحب إليه من والده و ولده
D. Wanda mutum daya ya ruwaito shi. Ana kiranshi *ALGAREEB الغريب*: Misalinsa: إنما الأعمال بالنيات
Dukkansu in banda na farko (A) ana ce musu Ahaad الآحاد.
NB. Hadisi ya kasu gida biyu:
1. Mutawatir: Wanda mutane da yawa suka ruwaito
2. Aahaad: Wanda mutane yan kadan suka ruwaito
Sannan hadisi ya kasu gida biyu(ta fuskar inganci ko rashin inganci) sune:
A. Karbabbe المقبول: Wanda ya qunshi Saheehi da Has an
B. Wanda bai inganta ba المردود: Shima ya kasu gida gida da yawa
Ana kasa hadisi gida haka ☝🏻 ne saboda dalikin qa'idojin da ake daura hadisin akansu da kuma bincike game da halayyar masu ruwaya.
Amma banda Al-mutawatir, Saboda yawan wanda suka ruwaito shi sun wuce ayi bincike akansu kuma hakan yana baiwa hadisi inganci fiye da wanda bai kaisa ba.
Anan zamu dakata sai kuma darasi na gaba.
Nukhbatul Fikr
Ibn Hajr Alasqalaniy
Gabatarwa: Abu Isma'il
Markazul Wa'ayil Islamiy Tudun Jukun Zaria
Ramadan Daura
3/9/1441- 26/4/2020
Comments
Post a Comment