fassarar waqen بداية السول في تفضيل الرسول صلى الله عليه وآله وسلم للشيخ العلامة العز عبد العزيز بن عبد السلام السلمي"
HIMMA BATA GA RAGO!
Waƙe kenan na Littafin:
"بداية السول في تفضيل الرسول صلى الله عليه وآله وسلم للشيخ العلامة العز عبد العزيز بن عبد السلام السلمي".
Wanda wani ɗalibi cikin ɗalibai na Markazul Wa'ayil Islamiy Tudun Jukun Zaria, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria ya tsarasu a matsayin ta shi gudumuwar; don bada kariya ga Manzon tsira (S.A.W).
Ɗalibi mai suna: Imrana Hamza 👳🏻♂️
1. Ya wanda ba shi da kishiya,
Mata kaza ɗa bai da shi.
2. Shi ke da mulkin duniya,
Al'arshi shi ɗai ke da shi.
3. Tsira, Aminci, ɗaukaka,
Gun wanda babu awa ya shi.
4. Alai da matayensa duk,
Har mai biyar su ka sa da shi.
5. Ka daɗan basira Rabbana,
Waƙe na ɗan rera wa shi.
6. Shi ne ka aiko gunmu duk,
Ɗa'a ka ce mu yi yo ga shi.
7. Ka ba shi duk matsayan da ba,
Wani wanda yai dai dai da shi.
8. Ya zarce kowa duniya,
Har Lahira an san da shi.
9. Aikensa ya game ko'ina,
Ba wanda zai ce ban da shi.
10. In za a ceto Lahira,
Tilas a dangantaka da shi.
11. Shi ke da Tutar godiya.
A cikinta har Adam da shi.
12. Zunubi idan ma za ya yi,
Tuni Rabbi yai Afuwa ga shi.
13. Ƙaunarsa wadda yake mana,
Ta zarce nasa da kansa shi.
13. Har addu'a aka ba shi ma,
Amma tunani ne da shi.
14. Ya ƙi yi wa kansa ya bar mana.
Ya san nufar da yake da shi.
15. Sai ran da rana za ta ɓa-,
Ci, ya ce a ɗan amsa wa shi.
16. Domin ya sam cetonmu duk,
Aljanna duk mu shige da shi.
17. Kuma Rabbana na ji da shi,
Domin ko bai da awa ya shi.
18. Rayuwarsa ya rantse da shi,
Albarkacin da take da shi.
19. Kuma bai kiran sunansa sam,
Haka girmamawa ce ga shi.
20. Haka nan da Ƙur'aninsa ma,
Har gobe na aiki da shi.
21. Ya zam mafi girman abin,
Gasar da kaf ba mai ya shi.
22. Dutse yana masa sallama,
Sannan yana gaishe da shi.
23. Yatsunsa sun tsatso ruwa,
Har an yi alwalla da shi.
24. Haka ya mayar da idaniya,
Bayan fitar ijiya a shi.
25. Ya raya dubban jikkuna,
Zucinsu sam ba rai a shi.
26. Zai sami sakamako na duk,
Ladaddakin da muke da shi.
27. Duk ayyukanmu da munka yi,
Sanadinsa ne muka san da shi.
28. Duk Annabin da ya zo a da,
Jama'arsa ɗai suka san da shi.
29. Shi ko gamewa anka yi,
Duka duniyar aka bai wa shi.
30. Musa da yai zance da shi,
A kwarin Ɗtuwa aka yo da shi.
31. Shi sanda an ka yi yo da shi,
Ai can Sama'u a kai da shi.
32. Jama'arsa ce ƙarshen zuwa,
Amma Ƙiyama fari shi.
33. Mu za a fara kira a can,
Farkon shiga Aljanna shi.
34. Duka Annabawa za su so,
Da ma a ce su ne a shi.
35. Shi za ya fara fita ƙasa,
Domin Hisabi sai da shi.
36. Haka ma Wasila tashi ce,
Ya Rabbana ka isar ga shi.
37. Jama'a dubu saba'in ku san,
Aljanna za su shige da shi.
38. Kuma ba hisabi ko kaɗan,
Ba zai Uƙubantar da shi.
39. Tafkinsa shi ɗai ke da shi.
Alkauthara aka bai wa shi.
40. Haka an halasta mai gani-,
Ma, don irin matsayinsa shi.
41. An bar ƙasa mu yi Taimama,
Salla ya ce mu yi yi a shi.
42. Kyawun ɗabi'a ke da shi,
Har Jalla ya yi yabo ga shi.
43. Allahu yai magana da shi,
Da dukan salon da yake da shi.
44. Wahayi da Ilhama duka,
Busa, mafarki yai da shi.
45. An ba shi littafin da ba-,
Bu, irinsa wanda yake da shi.
46. A cikinsa kwai Taura da In-,
Jila, Zabura kwai a shi.
47. Ya ƙunshi nasu gaba ɗaya,
Su nasu bai tsara da shi.
48. Aikinmu ya zam ɗan kaɗan,
Ladansa ba dai dai da shi.
49. An ba shi zaɓi don ya zam,
Sarkin da babu awa ya shi.
50. Ko ko ya zamto Annabi,
Bawan da babu irin sa shi.
51. Jibrilu sai yac ce da shi,
Ce ka zame Bawa ga shi.
52. Haka sai ya ba shi Tagomashi,
Ya zamo mutum mai Arashi.
53. Sai Rabbi yai masa lamuni,
In an yi Imanin da shi.
54. Halaka ba zai riske mu ba,
Matuƙar muna ɗa'a ga shi.
55. In za ka san shi haƙiƙani,
Je duba Ƙur'aninsa shi.
56. Sauƙin hali ne ke da shi,
Ba wanda ke kuka da shi.
57. Kaushinsa ya fi ga Kafirai,
In sun ƙi amsa kiransa shi.
58. Bai son tsanantawa ga mu,
Don ya fi sonmu a kansa shi.
Shukran
ReplyDeleteNagode
ReplyDeleteSlm Dan allh mlm atemakamin da maganin bugun jini na kwakwalwa nagode
ReplyDelete