M E N E N E
*G E N O T Y P E ?*
Insha Allahu za mu yi takaitaccen bayani akan a ma'anar da zamu iya bawa GENOTYPE cikin yaren Hausa, da fatan al'umma su gane menene tasirin saninsa kafin aure.
"Dukkan dan adam Allah Ya halicce shi ne tare da wasu kwayoyin halitta wadanda suke gudana a jikinsa, kuma wadannan kwayoyin halittar gadon su ake, yaya suna samun su ne daga irin nau'in wanda iyaye suke dashi, idan iyayen suka zama da nau'i mai kyau, zasu haifar da yaya lafiyayyu, idan aka samu akasi kuma za su haifi yaya masu rauni da matsalar Amosanin jini wadda ake cewa Sikila"
Masana sun raba genotype zuwa kaso uku da suke cewa: homozygous dominant, homozygous recessive, da kuma hetrozygous. Lura da wadanda ke bibiyar sakon zamuyi bayaninsa cikin sauki da yaren da kowa zai fahimta a takaice.
Ana sanin genotype idan anyi gwajin jini, wanda daga gwajin ake samun Genotypes a jikin mutane cikin nau'i guda 3 kamar haka, AA, AS, SS.
AA sune masu cikakkiyar kwayar halitta, AS kuma su ake cewa Carrier, akwai dan rauni a cikin kwayar halittarsu, sai kuma na ukun sune SS masu dauke da amosanin jini wato Sikila sabida raunin ita wannan kwayar halittar yakai makura.
Abu mai muhimmancin da ya kamata a lura kafin aure idan an duba genotype din sune kamar haka:
(Rukunin farko na nufin mijin, Na biyun kuma na nufin matar, sakamakon kuwa irin yayan da za a samu)
1. AA +AA = AA, AA, AA, AA (Za a samar da yaya masu cikakkiyar lafiya)
2. AA + AS = AA, AS, AA, AS, (Shima aure ne mai kyau kuma babu matsala a lafiyar yayan da za a haifa, amma bai kai na saman ba)
3. AA + SS = AS, AS, AS, AS, (Shima wannan auren ana iya yinsa duk da akwai yar matsala kadan akan yayan da za a haifa zasu zama AS ne duka, ma'ana carriers)
4. AS + AS = AA, AS, AS, SS, (Akwai matsala domin za a samu da ko ya mai cutar sikila)
5. AS + SS = AS, SS, SS, SS, (Akwai matsala sosai domin kusan kaso 80 na yaya zasu zama masu cutar sikila)
6. SS + SS = SS, SS, SS, SS, (Akwai matsala mai muni, domin dukkan yayan da iyayen sikila ne, zasu qare ne cikin tsanani da wahala na rashin lafiya)
Idan aka lura da wadannan matakan duka, ba shakka za a kawo raguwa ko karshen cutar amosanin jini wato sikila da take galabaitar da wadanda suke da ita, kuma ta wannan hanyar kadai a ke iya magantar ta kamadda tanan take samuwa. Allah ya qara mana lafiya ya kuma bawa marasa lafiyan mu lafiya. Aameen.
Don't just read, share to get others aware!
Share
Docto
Comments
Post a Comment