Skip to main content

Hadisi da Sunna 007

*HADISI DA SUNNAH* 
 *(A Fahimtar Ahlus-Sunnah Salafiyyah)* 

Rubutun 

Muhammad Abdullaah Assalafiy
 _(Abu-Abdillaah)_ 

 *Darasi na 07* 

 *SUNNAH A CIKIN HADISI* 

A cikin Hadisai Sahihai Annabin Rahama _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya bayyana kyakkyawan matsayin da *Sunnah* take da shi a cikin addinin nan, ta yadda ba zai yiwu a yi shi ba sai da ita. A nan ga misalin guda ɗaya kawai daga cikinsu, kamar inda ya ce: 

 *Riwaya ta ɗaya:* 

« أَلاَ إِنِّى أُوتِيتُ الْكِتَابَ وَمِثْلَهُ مَعَهُ ، أَلاَ يُوشِكُ رَجُلٌ شَبْعَانُ عَلَى أَرِيكَتِهِ يَقُولُ : عَلَيْكُمْ بِهَذَا الْقُرْآنِ ، فَمَا وَجَدْتُمْ فِيهِ مِنْ حَلاَلٍ فَأَحِلُّوهُ ، وَمَا وَجَدْتُمْ فِيهِ مِنْ حَرَامٍ فَحَرِّمُوهُ » « أَلاَ وَإِنَّ مَا حَرَّمَ رَسُولُ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - مِثْلُ مَا حَرَّمَ اللَّهُ »
Ku saurara! Haƙiƙa, an ba ni Alƙur’ani da wani misalinsa a tare da shi. Ku saurara! Ya yi kusa a samu wani mutum ƙosasshe a kan karagarsa yana cewa: Ku riƙe wannan Alƙur’anin: Duk abin da kuka gani na halal a cikinsa ku halatta shi, kuma duk abin da kuka gani a cikinsa na haram ku haramta shi. Ku ji da kyau! Duk abin da Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya haramta daidai ya ke da abin da Allaah Ta’aala ya haramta. _(Abu-Daawud (4604) da At-Tirmiziy (2664) da Ibn Maajah (12) suka riwaito shi daga Sahabi Al-Miƙdaam Bn Ma’adee Karib (Radiyal Laahu Anhu), kuma At-Tirmiziy ya ce: Wannan Hadisin kyakyawa ne mai hanya ɗaya ta wannan fuskar)._ 

Wannan ya nuna:

(i) Nau’in wahayi biyu ne Allaah Ta’aala ya yi wa Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam):_ Alqur’ani da Sunnah.

(ii) Alqur’ani da Sunnah a haɗe su ke, kamar yadda ya faɗa a wata riwaya, ba za su rabu ba har zuwa ranar Qiyama.

(iii) Tun tuni Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya yi bayanin zuwan maƙiya Sunnah masu kira ga a riƙe Alqur’ani shi kaɗai. 

(iv) Masu kira ga cewa a rike Alqur’ani kaɗai a rabu da Sunnah ba a kan gaskiya su ke ba, domin Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya tsoratar da al’umma game da su.

(v) Tabbatar da gaskiyar Annabicin Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ yadda ya bayar da labarin zuwan irin waɗannan mutanen tun kafin zuwan su.

(vi) Ba a cikin Alqur’ani ne kaɗai ake samun Halal da Haram ba, Sunnah ma tana da ikon yanke irin wannnan hukuncin.

(vii) Duk abin da Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya halatta ko ya haramta wajibi ne a karɓe shi a yi aiki da shi, ko da kuwa ba a gan shi ƙarara a cikin Alqur’ani ba.

 *Riwaya ta biyu:* 

Al-Imaam Abu-Daawud da Al-Imaam At-Tirmiziy sun sake riwaito wani hadisi makamancin wannan daga Abu-Raafi’i _(Radiyal Laahu Anhu)_ da wannan lafazin:

« لاَ أُلْفِيَنَّ أَحَدَكُمْ مُتَّكِئًا عَلَى أَرِيكَتِهِ ، يَأْتِيهِ أَمْرٌ مِمَّا أَمَرْتُ بِهِ أَوْ نَهَيْتُ عَنْهُ فَيَقُولُ : لاَ أَدْرِى ، مَا وَجَدْنَا فِى كِتَابِ اللَّهِ اتَّبَعْنَاهُ »
Kar fa in samu waninku yana kishingiɗe a kan karagarsa, wani al’amari daga cikin abin da na yi umurni da shi ko abin da na yi hani a kansa ya zo masa, sai kuma ya riƙa cewa: Ni fa ban sani ba! Abin da dai muka samu a cikin Alƙur’ani shi ne kaɗai za mu bi!! _(Abu-Daawud (4605) da At-Tirmiziy (2663) suka riwaito shi, kuma At-Tirmiziy ya ce: Wannan hadisi ne kyakkyawa ingantacce)._ 

Wannan ya nuna:

(i) Gaskiyar annabtar Annabin Rahama _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ yadda ya bayar da labari tare da siffata irin waɗannan mutanen tun kafin bayyanarsu a zamunan nan.

(ii) Ya siffata su da siffar mawadata masu nuna isa, da girman-kai, da ƙin karɓar gaskiya, da nuna wulaƙanci ga malaman Sunnah masu karantar da Sunnah.

(iii) Wajibi ne a bi duk abin da Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya yi umurni da shi ko ya yi hani a kansa, ko da kuwa ba a gan shi a fili a cikin Alqur’ani ba.

(iv) Ɓacewa daga Hanyar Gaskiya ce musulmi ya mayar da Sunnah Sahihiya, ya ƙi karɓarta, ya ƙi yin aiki da ita don wai bai ga abin da take bayanin sa a cikin Alqur’ani ba!

(v) Kafa hujja da cewa: Abin da muka gani a cikin Alqur’ani shi ne kaɗai za mu bi, babban kuskure ne, ɓacewa daga Hanyar Gaskiya ce, kuma hanyar hallaka ce. Shiyasa ya ambace shi a nan don nasiha.

..........................

 A saurari zuwan *darasi na 08*  _in shaa'al Laah._

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...