*HADISI DA SUNNAH*
*(A Fahimtar Ahlus-Sunnah Salafiyyah)*
Rubutun
Muhammad Abdullaah Assalafiy
_(Abu-Abdillaah)_
*Darasi na 02*
*1. MA’ANAR SUNNAH*
Asali a cikin harshen Larabci idan aka ce: *Sunnah* to kawai ana nufin: Hanya ko matafiya, kyakkyawa ko mummuna. Kamar maganar Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ cewa:
« مَنْ سَنَّ فِى الإِسْلاَمِ سُنَّةً حَسَنَةً فَلَهُ أَجْرُهَا وَأَجْرُ مَنْ عَمِلَ بِهَا بَعْدَهُ ، مِنْ غَيْرِ أَنْ يَنْقُصَ مِنْ أُجُورِهِمْ شَىْءٌ ، وَمَنْ سَنَّ فِى الإِسْلاَمِ سُنَّةً سَيِّئَةً كَانَ عَلَيْهِ وِزْرُهَا وَوِزْرُ مَنْ عَمِلَ بِهَا مِنْ بَعْدِهِ ، مِنْ غَيْرِ أَنْ يَنْقُصَ مِنْ أَوْزَارِهِمْ شَىْءٌ »
Duk wanda ya sunnata wata kyakkyawar Sunnah a cikin musulunci, to yana da ladanta da ladan duk wanda ya yi aiki da ita a bayansa, ba tare da wani abu na ladaddakinsu ya ragu ba. Haka kuma duk wanda ya sunnata wata mummunar Sunnah a cikin musulunci, to yana da zunubinta da zunubin duk wanda ya yi aiki da ita a bayansa, ba tare da wani abu na zunubansu ya ragu ba. _Al-Imaam Muslim (2240) ya fitar da shi_ .
Abin nufi da kyakkyawa ko mummunar Sunnah ita ce: Kyakkyawa ko mummunar hanya, ko matafiya. _Wal Laahu A’lam._
Amma a yaren shari’ar Addinin Musulunci kalmar *As-Sunnah* tana da mabambantan ma’anoni da gwargwadon mahangar da malamai suke kallonta:
(i) *Malaman Hadisi* suna cewa: *Sunnah* ita ce duk wani abin da aka samo daga Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ na wata magana ko wani aiki, ko tabbatarwarsa ga wani aiki ko maganar da aka yi a gabansa, ko bayanin siffarsa ta ɗabi’a ko ta halitta. _(Al-Imaam As-Sakhaawiy a cikin Fat-hul Mugheeth: 1/6 ya kawo ta._
(ii) Su kuwa *Malaman Usuulul Fiqhi* cewa suka yi: *Sunnah* ita ce duk abin da ya fito daga Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ na aiki ko magana ko tabbatar da wani aiki ko maganar da aka yi a gaban sa wanda ya cancanta ya iya zama dalili ga wani hukunci na shari’a. _Al-Imaam As-Shanqeetiy a cikin Muzakkirah Fi Usuulil Fiqhi: 95 ya kawo shi._
(iii) *Malaman Fiqhu* kuwa su cewa suka yi: *Sunnah* ita ce duk abin da ya ke akwai lada ga aikata shi, kuma akwai zargi ko suka - amma ba uƙuba ba - ga barin aikata shi. _Qaasim Al-Qawnawiy a cikin Aneesul Fuƙahaa’i: 106 ya kawo shi._
(iv) A wani lokaci malamai sukan yi amfani da lafazin *Sunnah* suna nufin dokar addinin musulunci da ta zo daga Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ amma ba a gan ta ƙarara a cikin Alƙur’ani ba. Kamar yadda sukan ce: *Dalilai na Shari’ah su ne: Littafi da Sunnah* , watau: Alƙur’ani da Hadisi. _Al-Imaam Ibn Al-Manzuur a cikin Lisaanul Arab, a Babin: (س ن ن) ya kawo shi._
(v) Akwai kuma sadda malamai sukan yi amfani da kalmar *Sunnah* suna nufin: Kishiyar Bidi’ah. Kamar yadda sukan ce: *Wane ɗan Sunnah ne* , idan yana
Yin abubuwan da suka dace da yadda Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya yi su ko ya karantar da su. Haka kuma sukan ce: *Wane ɗan bidi’a ne* , idan yana yin abubuwan da suka saɓa wa na farkon. _Al-Imaam As-Shaatabiy a cikin Al-Muwaafaqaat: 4/3-4 ya zo da shi._
(vi) Wani lokaci ma ana amfani da lafazin Sunnah da manufar abin da Sahabbai _(Radiyal Laahu Anhum)_ suka gudana a kansa, ko da kuwa ba a ga wata ayar Alƙur’ani ko Hadisi ƙarara a kan abin ba. Domin Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya riga ya ce:
« عَلَيْكُمْ بِسُنَّتِى وَسُنَّةِ الْخُلَفَاءِ الرَّاشِدِينَ »
Na hore ku da bin Sunnata da Sunnar Halifofin nan Shiryayyu. _Al-Imaam Ahmad (4/126-7) da Al-Imaam Abu-Daawud (4607) da Al-Imaam At-Tirmiziy (2676) da Al-Imaam Ibn Maajah (96) suka riwaito shi, kuma At-Tirmiziy ya ce: Kyakkyawa ne ingantacce._
*‘Halifofin nan’* kuwa, a haɗuwar dukkan malaman da ake yarda da maganganunsu a Musulunci, su ne:
1. Abubakar As-Siddeeq
2. Umar Bn Al-Khattaab
3. Uthman Bn Affaan
4. Aliyyu Bn Abi-Taalib _(Radiyal Laahu Anhum, Wa Anis Sahaabati Ajma’een)._
A taƙaice dai, malamai sun ce:
Idan aka saki kalmar *As-Sunnah* , musamman a babin *Aqeedah* , to ta zarce yadda malaman Hadisi da *Usuulul Fiqhi* da malaman *Fiqhun* suka fassara ta. Domin ta haɗe dukkan addini ne gaba ɗaya.
Al-Imaam Ibn Rajab Al-Hambaliy _(Rahimahul Laahu Ta’aala)_ ya ce:
*As-Sunnah* ita ce: Hanyar bi, wadda ta ƙunshi maƙalƙalewa ga abin da Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya tabbata a kansa, shi da Halifofinsa Shiryayyu _(Radiyal Laahu Anhum),_ a cikin aƙidoji da ayyuka da maganganu da sauransu. _Jaami’ul Uluumi Wal Hikam, shafi: 262._
Wannan ita ce maganar dukkan malaman *Sunnah Salafiyyah* . Dubi Al-Ustaaz Ad-Doktor As-Saheemiy a cikin: _Kun Salafiyyan Alal Jaadah, shafi: 29._
Hadisi kuma shi ne asali ko tushen da ake ciro Sunnah daga cikinsa.
Wani muhimmin abin lura a nan shine: waɗannan nau’ukan na *Sunnah* ba a iya samunsu sai ta hanyar Sahabbai _(Radiyal Laahu Anhum)_ su kaɗai kawai. Don haka duk wanda ya ajiye Sahabbai _(Radiyal Laahu Anhum)_ a gefe, kuma ya yi ƙoƙarin samo Sunnar shi da kansa kai-tsaye ko ta hanyar waninsu, to ya sani cewa ya karya gadar da ta sada shi da Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ne kawai, kuma ya kama buɗaɗɗiyar hanyar hallaka ce kawai ga kansa da duk wanda ya bi shi! Saboda haka sai ya yi gaggawan komowa kafin zuwan ɗan saƙon Ubangijinsa. Allaah ya tsare mu.
Bin Alƙur’ani da Sunnah kamar yadda Sahabbai _(Radiyal Laahu Anhum)_ suka fahimta, kuma suka gudanu a kai, shi ake kira *Salafiyyah* . Kuma babu wata hanyar tsira sai ita. Allaah ya taimake mu).
A saurari zuwan *darasi na 03* _in shaa'al Laah_ .
Comments
Post a Comment