Skip to main content

Hadisi da Sunnah 003

*HADISI DA SUNNAH* 
 *(A Fahimtar Ahlus-Sunnah Salafiyyah)* 

Rubutun 

Muhammad Abdullaah Assalafiy
 _(Abu-Abdillaah)_ 

 *Darasi na 03* 

 *SUNNAH DAIDAI DA ALƘUR’ANI TA KE* 

Sanannen abu ne a wurin dukkan *Ahlus-Sunnah* cewa Alƙur’ani maganar Allaah ne, saukakke daga wurinsa ba halitacce ba ne, wanda kuma Allaah ya bautar da bayi da karatunsa. Shi wata wanzajjiya kuma tabbatacciyar mu’ujiza ce da ta gagari dukkan halittu a kan su zo da irinta! 

Ta wannan fuskar Alƙur’ani a sama ya ke, kuma ya fi falala da daraja a kan dukkan maganganun da ba shi ba, har da Sunnar Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)._ 

Amma ta fuskar kafa hujja ko fitar da dalili a kan wani hukuncin shari’ah, Sunnah Sahihiya daidai ta ke da Alƙur’ani, babu fifiko a tsakaninsu. Domin dai dukkansu wahayi ne daga wurin Allaah Maɗaukakin Sarki wanda ya faɗa game da Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam):_ 

وَمَا یَنطِقُ عَنِ ٱلۡهَوَىٰۤ .  إِنۡ هُوَ إِلَّا وَحۡیࣱ یُوحَىٰ
Kuma ba ya yin furuci daga sha’awar rai, (maganarsa) ba komai ba ce sai dai wahayi kawai da ake yi masa. _Suratun Najmi: 3-4_ 

Kuma malamai sun nuna cewa:
 
كَانَ جِبْرِيلُ عَلَيْهِ السَّلَامُ يَنْزِلُ عَلَى النَّبِيِّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ -  بِالسُّنَّةِ ، كَمَا يَنْزِلُ عَلَيْهِ بِالْقُرْآنِ
Mala’ika Jibril _(Alaihis Salaam)_ yana sauka ga Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ da wahayin Sunnah, kamar yadda yake sauka gare shi da wahayin Alƙur’ani. 
 _(Al-Imaam Ad-Daarimiy (lamba: 608) ya riwaito shi daga Hassaan Bn Atiyyah. Kuma Hussain Salim Asad Ad-Daaraaniy mai tahaƙiƙin littafin, bayan ya kawo riwayoyinsa da yawa daga Hassaan sai ya ce (1/474): Isnadinsa Sahihi ne)._ 

Don haka, babu shakka! Babban kuskure ne, kuma ko kaɗan ba daidai ba ne: Abin da waɗansu malamai suka gudana a kansa na fifita Alƙur’ani a kan Sunnah a wurin kafa hujja, ko fitar da wani hukuncin shari’a. 

Babban dalilinsu a kan hakan kuwa shi ne: Hadisin Mu’azu Bn Jabal _(Radiyal Laahu Anhu)_ cewa wai: 

A lokacin da Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya aiki shi Mu’azun zuwa ƙasar Yamen sai ya ce da shi: Da me za ka yanke hukunci idan aka kawo maka ƙara? 

Sai Mu’azu ya ce: Zan yi hukunci ne da abin da yake cikin Littafin Allaah! 

Ya ce: Idan kuma ba ya cikin Littafin Allaah fa? 

Sai ya ce: Sai in yanke da Sunnar Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)!_ 

Ya ce: In kuma ba ya cikin Sunnar Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ fa? 

Sai ya ce: Sai in yi ijtihadi da ra’ayina, kuma ba zan yi sakaci ba! 

A nan ne wai sai Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya dafa ƙirjinsa, kuma ya ce:
 
« الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِى وَفَّقَ رَسُولَ رَسُولِ اللَّهِ لِمَا يُرْضِى رَسُولَ اللَّهِ »
Godiya ta tabbata ga Allaah Wanda ya datar da ɗan saƙon Manzon Allaah ga abin da Manzon Allaah yake yarda da shi. 
 _(Hadisi ne Da’eef. Manyan Malaman Hadisi irin su Al-Bukhaariy da At-Tirmiziy da Al-Uqailiy da Ad-Daaraqutniy da Ibn Hazm da Ibn Taahir da Ibn Al-Jawziy da Az-Zahabiy da As-Subkiy da Ibn Hajr duk sun raunana shi. Lallai ka karanta Silsilah Da’eefah: 2/273-286 domin samun natsuwa, ka rabu da hayaniyar waɗanda ba su gama nuna ba)._ 

Sai dai kuma tun tuni malamai muhaƙƙiƙai sun tabbatar da cewa wannan ba hujja ba ce!

Saboda me?

Domin da farko dai wannan hadisin da’eef ne mai rauni, wanda kuma ba a iya kafa hujja da shi *ittifaaqan* , musamman a kan al’amarin addini mai girma irin wannan: Watau al’amarin fitar da hukuncin Fiqhu daga cikin nassoshi.

Sannan kuma kamar yadda malamai suka faɗa, yin amfani da koyarwar da ke cikinsa yana sanyawa a tafka mummunan kuskure a wurin yanke hukunci a cikin mas’aloli masu yawa. 

Alal misali: Idan aka yi fatawa ga mutumin da yake tafiya a kan koyarwar wannan hadisin cewa: Menene hukuncin mataccen kifi? 

Abin da zai fara tunowa a cikin Alƙur’ani ita ce Ayar da ta ce:
 
حُرِّمَتۡ عَلَیۡكُمُ ٱلۡمَیۡتَةُ وَٱلدَّمُ وَلَحۡمُ ٱلۡخِنزِیرِ 
An haramta muku cin mushe da jini da naman alade. _Suratul Maa’idah: 3._ 

Har zuwa ƙarshen Ayar.

A kan haka zai iya yanke hukunci da cewa: Mataccen kifi ma haram ne! 

Daga nan, ka ga sai ya tafka mummunar ɓarna!! Ya haramta wa musulmi daddaɗan nama mai lafiya wanda Allaah Ta’aala bai haramta musu ba! 

Me ya kai shi ga haka? 

 A saurari zuwan *darasi na 04*  _in shaa'al Laah_ .

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...