Skip to main content

Hadisi da Sunnah 005

*HADISI DA SUNNAH* 
 *(A Fahimtar Ahlus-Sunnah Salafiyyah)* 

Rubutun 

Muhammad Abdullaah Assalafiy
 _(Abu-Abdillaah)_ 

 *Darasi na 05* 

 *SUNNAH A CIKIN ALƘUR’ANI* 

A cikin Ayoyi masu yawa na Alƙur’ani Allaah Mabuwayi Mai Girma ya bayyana matsayin Sunnah a cikin Musulunci, kamar inda ya ce: 

 *Aya ta ɗaya:* 

وَأَنزَلۡنَاۤ إِلَیۡكَ ٱلذِّكۡرَ لِتُبَیِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَیۡهِمۡ وَلَعَلَّهُمۡ یَتَفَكَّرُونَ
Kuma mun saukar da Alqur’ani a gare ka ne domin ka yi wa mutane bayanin abin da aka sassaukar musu, kuma domin ko sa riƙa yin tunani. _(Suratun Nahli: 44)._ 

Wannan aya ta nuna:

(i) Babban aikin da Allaah _(Subhaanahu Wa Ta’aala)_ ya ɗora wa Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ shi ne yin bayanin Alqur’anin da ya saukar masa.

(ii) Haƙiƙa! Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya bi wannan umurnin na Allaah _(Subaanahu Wa Ta’aala):_ Ya yi cikakken bayanin Alƙur’anin har na tsawon shekaru ashirin da uku. 

(iii) Ya bi hanyoyi uku wurin wannan bayanin: Ta hanyar bayanin da bakinsa, da hanyar yin aiki da gaɓoɓinsa, da kuma hanyar tabbatarwa ga ayyuka ko maganganun da Sahabbansa _(Radiyal Laahu Anhum)_ suka yi a gabansa.

(iv) Kuma wannan bayanin shi ne malaman Sunnah da Hadisi - Allaah ya saka musu da mafi kyawun alkhairinsa - suka tattara a cikin Littaffan da ake kira *Littaffan Sunnah* ko *Hadisi* .

Watau: Littaffai irin su: *Sihaah* da *Jawaami’* da *Sunan* da *Masaanid* da *Ma’aajim* da *Mustadrakaat* da *Mustakhrajaat* da *Ajzaa’* da sauransu na nau’ukan wallafe-wallafe masu daraja da ƙima da girma na manyan Malaman Hadisi da Sunnah. _(Dubi Makaanatu Ahlil-Hadeeth)._ 

(v) Kuma idan ba ta bin Sunnah ba ta yaya saƙon Allaah da ke cikin Alƙur’anin zai bayyana ga al’umma har su iya haɗuwa a kan yin aiki da shi kamar yadda Allaah yake so?! 

Allaah ya ƙara mana shiriya.

 *Aya ta biyu:* 
 
وَمَاۤ ءَاتَىٰكُمُ ٱلرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَمَا نَهَىٰكُمۡ عَنۡهُ فَٱنتَهُوا۟ۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِیدُ ٱلۡعِقَابِ 
Kuma abin da Manzon ya ba ku sai ku karɓe shi, kuma abin da ya hane ku sai ku hanu, kuma ku ji tsoron Allaah. Lallai Allaah mai tsananin uƙuba ne. _(Suratul Hashri: 7)_ 

Wannan ya nuna:

(i) Allaah Maɗaukaki Mai Girma doka yake ba mu bayinsa, yake yi cewa: Duk mu maƙalƙale wa Sunnar Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)._ 

(ii) Ana bin Sunnar ce kuwa ta kama yin aiki da abin da Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallaam)_ ya kawo, da barin duk abin da ya hana.

(iii) Allaah yana tsawatar da mu cewa: Kar mu yarda mu ƙi bin Sunnah a cikin komai, kar kuma mu kuskura mu yi ƙoƙarin yin watsi da ita.

(iv) Sannan masu irin wannan tunanin na ƙin bin Sunnah a cikinmu: Su ji tsoron Allaah, kar su yi sakaci har Allaah ya kama su da laifin saɓa wa umurninsa ko haninsa.

(v) Domin kuwa shi mai tsananin uƙuba ne ga dukkan wanda ya yi ƙarfin halin saɓa masa, ya aikata abin da ya hana shi aikatawa a kan harshen Manzonsa _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)._ 

..........................

 A saurari zuwan *darasi na 06*  _in shaa'al Laah._

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...