*HADISI DA SUNNAH*
*(A Fahimtar Ahlus-Sunnah Salafiyyah)*
Rubutun
Muhammad Abdullaah Assalafiy
_(Abu-Abdillaah)_
*Darasi na 06*
*Aya ta uku:*
قُلۡ إِن كُنتُمۡ تُحِبُّونَ ٱللَّهَ فَٱتَّبِعُونِی یُحۡبِبۡكُمُ ٱللَّهُ وَیَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورࣱ رَّحِیمࣱ
Ka ce: In kun kasance kuna son Allaah ne to ku bi ni. Allaah zai so ku kuma ya gafarta muku zunubanku. Kuma Allaah mai yawan gafara ne, mai yawan tausayi. _(Suratu Ali-Imraan: 31)._
Wannan Ayar ta nuna a fili cewa:
(i) Duk wata da’awa ta ƙaunar Allaah da mutum ya ke yi tana zama ta ƙarya ce kawai, kuma babu ko ƙanshin gaskiya a cikinta, matuƙar dai mai ita bai zama mabiyin Hadisi da Sunnah a fili ƙarara ba.
(ii) Alamar son Allaah da Addinin Allaah Ta’aala shi ne a ga mutum yana bin Sunnah sak, kuma yana rabuwa da dukkan nau’o’in bidi’a.
(iii) Sakamakon bin Sunnah ga mutum shi ne: Samun ƙaunar Ubangiji ga bawa, kuma da samun gafarar zunubai.
(iv) Allaah Maɗaukakin Sarki yana da Kyawawan Sunaye kamar: *Al-Ghafuur* da *Ar-Raheem* , da Maɗaukakan Siffofi kamar: Gafara da Tausayi, waɗanda babu wanda ya yi kama da shi a cikinsu.
Allaah ya ƙara mana fahimta.
*Aya ta huɗu:*
فَلَا وَرَبِّكَ لَا یُؤۡمِنُونَ حَتَّىٰ یُحَكِّمُوكَ فِیمَا شَجَرَ بَیۡنَهُمۡ ثُمَّ لَا یَجِدُوا۟ فِیۤ أَنفُسِهِمۡ حَرَجࣰا مِّمَّا قَضَیۡتَ وَیُسَلِّمُوا۟ تَسۡلِیمࣰا
Ina rantsuwa da Ubangijinka! Haƙiƙa, ba za su taɓa yin imani ba har sai sun sanya kai ne mai hukunci a cikin duk wani saɓanin da ya shiga tsakaninsu, sannan kuma ya zama ba su samu wani ƙunci a cikin ransu game da abin da ka hukunta ba, sannan kuma sai sun miƙa wuya matuƙar miƙawa. _(Suratun Nisaa’i: 65)._
Wannan ayar ta kore cikar imani ne ga dukkan mutane, sai ga wanda ya cika waɗannan sharuɗɗan:
(i) Wanda ya mayar da Sunnah ta Annabi Muhammad _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ita ce mai hukunci a cikin duk wani saɓani a tsakaninsa da ɗan’uwansa.
(ii) Wanda ya yarda ya kai ƙara da neman yanke hukunci ga Sunnah kaɗai a lokacin kowane irin saɓani, ba ga wani wurin daban ba.
(iii) Wanda ya amince da hukuncin da Sunnah ta yanke tun daga zuciyarsa ba tare da samun wani ƙunci ko wata takura a cikin ƙirjinsa ba.
(iv) Wanda ya sallama wa hukuncin da Sunnah ta yanke, ya miƙa-wuya a fili da ɓoye, ba tare da wata jayayya ko kai-kawo ba.
(v) Da zaran an rasa ɗaya daga cikin waɗannan sharuɗɗan, shikenan babu cikakken imani, domin manufar rantsuwa mai ƙarfi da Allaah ya yi tun a farkon ayar kenan!
Allaah ya kiyaye.
*Aya ta biyar:*
فَلۡیَحۡذَرِ ٱلَّذِینَ یُخَالِفُونَ عَنۡ أَمۡرِهِۦۤ أَن تُصِیبَهُمۡ فِتۡنَةٌ أَوۡ یُصِیبَهُمۡ عَذَابٌ أَلِیمٌ
Waɗanda suke saɓa wa umurninsa su ji tsoron kar fa wata fitina ta shafe su, ko kuwa wata azaba mai raɗaɗi ta shafe su! _(Suratun Nuur: 63)._
Wannan ya nuna:
(i) Da Sunnah ce ake auna dukkan maganganu da ayyukan bayi, kuma ba za a karɓi komai daga cikinsu ba sai wanda ya dace da Sunnah kawai.
(ii) Masu tsayuwa a kan Sunnah sak su suke da cikakken aminci daga dukkan fitinu a Duniya da Barzakhu da Lahira.
(iii) Su kuwa masu saɓa wa Sunnah ana ji musu tsoron hakan ya jawo musu kamuwa da cutar fitinar kafirci ko munafunci ko bidi’anci a cikin zukatansu.
(iv) Ko kuma a kama su da uƙuba mai tsanani ta kisa ko haddi tun daga nan duniya kafin Makoma Lahira!
Allaah ya kare mu.
..........................
A saurari zuwan *darasi na 07* _in shaa'al Laah._
Comments
Post a Comment