*HADISI DA SUNNAH*
*(A Fahimtar Ahlus-Sunnah Salafiyyah)*
Rubutun
Muhammad Abdullaah Assalafiy
_(Abu-Abdillaah)_
*Darasi na 01*
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَـٰنِ ٱلرَّحِیمِ
*DA FARKO*
Godiya ta tabbata ga Allaah: Muna gode masa, muna neman taimakonsa, muna neman gafararsa, kuma muna roƙon Allaah ya tsare mu daga sharrorin kawunanmu da munanan ayyukanmu.
Wanda Allaah ya shiryar babu mai ɓatar da shi, wanda kuma ya ɓata babu mai shiryar da shi.
Ina shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allaah shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad _(Sallal Laahu ’Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ Bawansa ne kuma Manzonsa ne.
یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ ٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ حَقَّ تُقَاتِهِۦ وَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنتُم مُّسۡلِمُونَ
Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku ji tsoron Allaah haƙiƙanin jin tsoronsa. Kuma kada ku mutu sai a halin kuna musulmi. _(Surah Al-Imraan: 102)._
یَـٰۤأَیُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُوا۟ رَبَّكُمُ ٱلَّذِی خَلَقَكُم مِّن نَّفۡسࣲ وَ ٰحِدَةࣲ وَخَلَقَ مِنۡهَا زَوۡجَهَا وَبَثَّ مِنۡهُمَا رِجَالࣰا كَثِیرࣰا وَنِسَاۤءࣰۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ ٱلَّذِی تَسَاۤءَلُونَ بِهِۦ وَٱلۡأَرۡحَامَۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَیۡكُمۡ رَقِیبࣰا
Ya ku mutane! Ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicce ku daga rai guda ɗaya, kuma daga gare shi ya halitta masa matarsa, kuma daga gare su ya yaɗa mazaje masu yawa, kuma da mata. Ku ji tsoron Allaah wanda kuke roƙon juna game da shi, kuma ku kiyayi yanke zumunci, haƙiƙa Allaah ya kasance mai tsaro ne a kanku. _(Surah An-Nisaa’i: 1)._
یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ ٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَقُولُوا۟ قَوۡلࣰا سَدِیدࣰا . یُصۡلِحۡ لَكُمۡ أَعۡمَـٰلَكُمۡ وَیَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡۗ وَمَن یُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَقَدۡ فَازَ فَوۡزًا عَظِیمًا
Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku ji tsoron Allaah, kuma ku faɗi magana madaidaiciya. Zai gyara muku ayyukanku kuma zai gafarta muku zunubanku, kuma wanda ya yi wa Allaah da Manzonsa ɗa’a, to tabbas ya rabauta da rabo mai girma. _(Surah Al-Ahzaab: 70-71)._
Bayan haka, haƙiƙa! Mafi gaskiyar magana ita ce Littafin Allaah, kuma mafificiyar shiriya ita ce shiriyar Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam),_ kuma mafi sharrin al’amura su ne ƙirƙirarrunsu, kuma dukkan wata ƙirƙira bidi’a ce, kuma dukkan wata bidi’a ɓata ce, kuma dukkan ɓata tana cikin wuta.
Waɗansu mutane ne suka bayyana a cikinmu a ’yan shekarun nan, suna ta suka da warware karantarwar Sahihiyar Sunnah, da sukar yin aiki da ita a cikin al’ummarmu. Abin da manyan malamai sanannu kuma kafaffu a kan Sunnar suka daɗe da karantarwa da koyar da yin aiki da ita! Waɗanda wasunsu sun rayu kuma har sun rasu ne a kan wannan aikin, kuma jama’a da dama na-kusa da na-nesa sun san su, kuma sun yi musu shaida da shi.
Idan da waɗannan sabbin fitowa a cikin garuruwanmu suna daga cikin waɗanda aka san su da ƙyamar Sunnah da Hadisi da Ahlus-Sunnah ne tun farko, to da babu wata damuwa ko wata matsala, domin sai a faɗa, kamar yadda masu iya magana suke faɗa cewa: *Inna ta gai da Aisha,* domin abin sai ya zama kamar yadda ake cewa ne: *Za ni ce ta tarar da mu je mu!*
To, amma abin mamaki! Sai ya zamana waɗannan mutanen sun fito ne daga cikin gidan Sunnah, ko kuma ma gidan da kowa ya san shi ne gidan da ya ɗaga tuta na koyarwa da karantar da Sunnah a cikin ƙasar nan da wajenta. Shiyasa wasu da yawa suke cewa: *Tir! Amma dai albasa ba ta yi halin ruwa ba!* Ko kuma: *Ɗan malam dai bai yi halin malam ba!*
Sannan kuma idan da maganganun irin waɗannan mutanen ba su samu karɓuwa a wurin jama’a ba, to a nan ma da abubuwan sun yi sauƙi. Amma kuma abin takaicin shi ne: Ana samun daga cikin dajjitai da wasu matasa ma suna sauraren maganganun waɗannan mutanen, suna halartan wuraren darussansu, suna ƙara zuga su da kambama su, da yi musu kabbara!
Wannan shi yake ƙara musu ƙaimi da ƙarfin gwiwa, ya ƙara sa su dogewa a kan cigaba da sukan Hadisai da Sunnah da mabiya Sunnah, kuma wai duk da sunan karantar da Sunnah!!
Haka kuma in da su kaɗai ne suke yin taɓargazarsu a saƙo ba tare da sanin sauran jama’a ba, da a nan ma an samu sauƙi. Amma kuma sai ya zama duk irin wannan ɓarna da taɓargazar da shirmen da suke tafkawa, ana samun kafafen yaɗa bayanai - ba ma na zamani a cikin _‘social media’_ kaɗai ba - har ma da wasu tashoshin rediyo da talbijin na Hukuma ko na masu-zaman-kansu suna ɗauko waɗannan abubuwan suna yaɗawa a cikin jama’a, musamman a cikin matasa da matan aure da sauransu!
لِیَحۡمِلُوۤا۟ أَوۡزَارَهُمۡ كَامِلَةࣰ یَوۡمَ ٱلۡقِیَـٰمَةِ وَمِنۡ أَوۡزَارِ ٱلَّذِینَ یُضِلُّونَهُم بِغَیۡرِ عِلۡمٍۗ
Domin su ɗauki nauyin zunubansu cikakku a Ranar Qiyama, kuma da nauyin zunuban waɗanda suke ɓatar da su ba da ilimi ba. _(Surah An-Nahl: 25)_
_Inaa Lil Laahi Wa Innaa Ilaihi Raaji’uun._
To, domin sauke nauyin da Allaah Maɗaukakin Sarki ya ɗora a kan *‘waɗanda suka sani’,* na yin bayanin gaskiya ga al’umma, domin duk wanda zai ɓata ya ɓace a kan hujja, wanda kuma zai shiryu shi ma ya shiryu a kan hujja, sai na tsayu da rubuta wannan ɗan littafin wanda na kalato shi daga maganganun manyan malaman Sunnah managarta na-da da yanzu. Allaah ya saka musu da dukkan alkhairi, kuma ya tabbatar da mu a kan tafarkinsu har zuwa ƙarshenmu.
Ina fatar ya zama mabuɗin alkhairi kuma fitila mai haskaka hanya gare ni da farko, sannan ga al’ummarmu, musamman matasa da mata waɗanda maganganun waɗancan mutanen suke burge su, kuma suke ba su sha’awa.
Allaah Ta’aala nake roƙo da Sunayensa Kyawawa da Siffofinsa Maɗaukaka da ya shiryar da su har su gane irin ɓarnar da suke yi wa da’awar sahihin musulunci a duniya, ba wai ga jama’armu ta *Ahlus-Sunnah* ba kaɗai a ciki da wajen ƙasar nan.
Haka su ma waɗanda ake ta yaudara, Allaah ka sa su gane gaskiya, kuma su samu daman sauka daga motar hallaka da ta kwashe su a duk tashar da ta tsaya domin hutawa ko domin shan mai, kafin ta gangara da su a cikin kwarin hallaka.
Ya Allaah! Tsarki ya tabbata gare ka haɗe da Godiyarka. Ina shaidawa babu wani abin bautawa da gaskiya sai dai kai. Ina neman gafararka, kuma ina tuba gare ka.
Muhammad Abdullaah Assalafiy
_Markazu Ahlil-Hadeeth_ ,
Kaduna.
18/8/2016
10: 21am.
A saurari darasi na *02* _in shaa'al Laah_
Allah ya saka da alkhairi
ReplyDeleteAllah ya karba
ReplyDelete