YADDA AKE YIN MAN KWAKWA
Da kuma amfaninsa.
Daga shafin Sunnah Medicine masu yin
Ruq'yah da harhada Magungunan Musulunci.
https://www.facebook.com/sunnahmedicinepage/
Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Yadda ake hada Man Kwakwa:-
Ababe da za’a bukata
•Kwakwa
•Ruwa
Yadda za a hada.
A samu Kwakwa mai kyau, sai a 6are 6won a
kankare bayan kwakwar ya rage farin kawai, sannan a yayyanka ta kanana saboda ta yi saukinmarkadawa.
A zuba ruwa da dan dama a cikin blandar sai ahada da yankakkiyar kwakwar sai a markada har sai markaden ya yi laushi sosai.
A sami a bin tatar kamu a tace ruwan kwakwarsosai, za a ga ruwan kamar madara.
Za’a iya ajiye markadadden ruwan kwakwa nakwana daya ga wadda ba ta da firinji ko kuma asaka shi a firinji domin ruwan ya hadu sosai.
Bayan kwana daya za a ga madarar kamarkindirmo a saman kwano.
Sai a kwashe wannan madarar da aka tace a zuba
ta a cikin tukunyar suyar sai a dora tukunyar a kan wuta, haka za a yi tajuyawa da cokali har sai wannan madarar ta komakamar ruwan kasa mai dan duhu.
Sai a sauke a sake tacewa.
Za a ga man kwakwar ya fito tsaf.
Sai a sami kwalba a ajiye ana amfani da shi yadda
ake so.
Sunnah Medicine.
https://www.facebook.com/sunnahmedicinepage/
08162600700.
AMFANIN MAN KWAKWA
Ga kadan daga cikin ayyukansa:
1- Taushin fata – Ana iya shafawa kamar man jiki
a shafa a ko’ina har wuya. Wannan zai sa fata tay
laushi da taushi.
2- Man fuska – ana shafawa a zagage kwayar
ido da shi yana maganin bakin da ke fitowa
zagayen fatar ido.
3- Maganin tamushewar
fata na tsufa. Idan ana shafa man kwakwa yana
maganin wannan.
4- Kwantar da fata yayin aski – Man Kwakwa
yana gyarawa masu aski, kamar maza masu
yawan yin kurajen fuska, sakamakon gyaran
fuska da sauransu, yana warkar da kuraje.
5- Man goge hakora – akwai magungunan
wanke baki dayawa amma wannan na daban
ne ku hada man Kwakwa a
gauraya dan kadan a sa a ‘Brush’ a goge baki
da shi.
6- Ana shafa man Kwakwa kadan a jikin auduga a
goge fuska da shi yana gagawan cire kwalliyar da
ta dankare a fuskar mata.
7- Yana hana fashewar lebe, musamman alokacin sanyi.
8- Man Kwakwa yana gyara jikin jarirai,
musamman ma irin masu yin ciwon Ella din
nan har cikin gashin kansu, ana ganin kokon
kai yana yi kaman Amosani fari fat, to uwa ta
dage da gogawa yaro man Kwakwa inshaAllahu zai warke.
8- Yana gyara gashin mata, yana sawa ya karakarfi da yawa da laushi.
9- yana kashe amosani sannan yana kashe kwarkwata.
10- Yana maganin cututukan fata da dama,kamar su Eczema, kunan wuta, kyasbe da daisauran cuttukan fata.
11- Ana iya hada man Kwakwa da sugar a murza
a fata, sannan a wanke da ruwa da sabulu yana sa
fata ya yi laushi lukwi-lukwi.
12- Maganin Nankarwa. Idan mace tana da
nankarwa to se ta dinga shafa Man kwakwa. Za ta
6ace insha Allah.
Daga shafin Sunnah Medicine.
Comments
Post a Comment