ALQUR’ANI BABBAR NI’IMA.
ALQUR’ANI BABBAR NI’IMA.
Daga Mustapha Musa Abu Aisha.
Hakika Babu wata babbar ni’ima da Allah yayiwa wannan al’ummar bayan Ni’imar aiko da Annabi s.aw kamar bamu alqurani mai girma,mu riqe alqurani domin roqo da shi alkhairine duniya da lahira.
-Allah ya saukar da Alqurani ta hanyar daya daga cikin Mala’iku wato Mala’ika Jibrilu zuwa ga Annabi s.a.w
Sai Mala’ika Jibril ya zama mafi alkhairi kuma mafi falala da matsayi a cikin sauran Mala’iku saboda falalar saukar da alqurani ta wajansa shi kadai.
-Kuma Allah ya saukar da Alqurani mai a cikin watan Ramadana,sai watan Ramadana ya zama wata mafi girman alkhairi da falala akan sauran watan nin shekara baki daya.
Shiyasa Allah ya shar anta mana yin azumi awannan watan saboda falalar saukar da alqurani acikinsa.
-An saukar da alqurani acikin daren Lailatul Qadri,sai daran ya kasance mafi alkhairin dare a cikin sauran dararen shekara baki daya, saboda saukar da alkhairi da akayi acikinsa.
-An saukar da alqurani mai girma ga Annabi mafi girma Annabi Muhammad s.a.w
Sai Annabi s.a.w ya zama mafi alkhairi da falala akan sauran dukkan Manzannin Allah baki daya.
-An saukar da alqurani ga wannan al’ummar ta musulmai sai sanadiyyar hakan ta zama mafi alkhairi da falala akan sauran dukkan al’umma baki daya,saboda da falalar saukar da alqurani mai girma akanta.
Wallahi babu wanda alqurani zai sauka a zuciyarsa face ya wayi gari ya zama mafi alkhairin mutane sanadiyyar saukar alqurani a zuciyarsa.
Shiyasa Manzon Allah saw yake cewa;
(Mafi alkhairi acikin ku shine wanda ya koyi alqurani kuma yake koyar dashi).
Mafi hanyar godewa Allah akan ni’imar alqurani a garemu shine;-
-Yin imani da shi akan maganace ta Allah kuma siffar Allah ce ba Halittaba
-Imani da shine littafin Allah na karshe wanda ya shafe sauran dukkan littattafai baki daya.
-Koyan karatunsa da sanin ma’anoninsa da aiki dashi.
-Koyar da shi da yada shi.
Allah ka sanya ni da sauran ya uwana musulmai cikin ma’abuta alqurani.
Comments
Post a Comment