Skip to main content

Bayanin abin da ake nufi da saura

 

Bayanin abin da ake nufi da saura

Saura

Shi ne abin da ya rage a cikin kwano bayan an sha

A qa’ida duk abin da aka sha aka rage mai tsarki ne, sai dai abin da dalili ya nuna cewa najasa ne.

1- Sauran abin da aka sha wanda yake mai tsarki

a) Abin da mutum ya sha ya rage

Saboda abin da ya tabbata na cewa “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana shan sauran Aisha – Allah ya yarda da ita – alhali tana cikin jinin al’ada, yana sanya bakinsa a inda ta sa bakinta ”[ Muslim ne ya rawaito shi]

Abin xan adam ya sha ya rage

b) Abin da mage ta sha ta rage

Saboda abin da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya faxa game mage yayin da ta sha ruwa daga wata kwarya, ya ce, “Lallai ita ba najasa ba ce, ita tana cikin masu kai-kawo a cikinku” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

Abin da mage ta sha ta rage

c) Abin da dabbar da ake cin namanta ta

sha ta rage, da abin alfadari da jakuna da namun daji da tsuntsaye suka sha suka rage mai tsarki ne, saboda qa’ida dukkan abubuwa masu tsarki ne, babu wani dalili da ya nuna najasar wannan abun, saboda kuma Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana hawan jakuna, kuma ana hawansu a zamaninsa.

Abin da Jakuna suka sha suka rage
Abin da dabbar da ake ci ta sha ta rage
Abin da tsuntsaye suka sha suka rage
Abin da dabbobi masu farautar dabbobi suka sha suka rage

2- Abubuwan Da Aka Sha Aka Rage Waxanda Suke Najasa Ne

a) Sauran Kare

Saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Tsarkin kwanon xayanku idan kare ya yi lallage [ Lallage : shi ne kare ya sanya harshensa a cikin kwano ya jujjuya shi, ko ya sha abin da yake ci ko bai sha ba.] a cikinsa, ya wanke shi sau bakwai, na farko da qasa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

b) Abin Da Alade Ya Sha Ya Rage

Qiyasi a kan kare, saboda alade da kare dukkansu najasa ne.

Abin da alade ya sha ya rage
Abin da kare ya sha ya rage

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...