Skip to main content

Bayanin Kwanuka

 

Bayanin Kwanuka

Kwanuka

Abubuwan da ake ajiye ruwa ko wani abu a cikinsu

Amfani da kwanon zinare da na Azurfa

1-Amfani Da Kwanon Zinare Da Azurfa Wajen Ci Da Sha

Haramun ne a yi amfani da su, saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) : “Kada ku sha da kwanon zinare da azurfa, kada ku ci a cikinsu, saboda ta su ce (kafirai) a duniya, a lahira kuma tamu ce” [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Da faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Wanda yake shan wani abu a cikin kwanon azurfa to yana kwankwaxar wutar Jahannama ne a cikinsa” [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Sha da kwanon Azurfa
Ci a cikin kwanon zinare

2-Amfani Da Kwanon Zinare Da Azurfa Ba A Wajen Ci Ko Sha Ba

An halatta a yi amfani da su ba a wajen ci ko sha ba, kamar yin alwala da sauransu, saboda hadisin da ya gabata ya taqaita hanin a kan ci da sha, kuma ya tabbata cewa “ Ummu Salama Allah ya yarda ita tana da wani [ Wani xan qaramin kwano ne kamar qararrawa] asusu na azurfa, a cikinsa akwai gashin kan Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ” [ Bukhari ne ya ruwaito shi].

Butar azurfa saboda yin alwala

Amfani Da Kwanon Da Aka Liqe Shi Da Azurfa

Ya halatta a yi amfani da kwanon da aka liqe shi da ‘yar azurfa kaxan don wata buqata, saboda abin da ya tabbata cewa “akushin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya fashe, sai a ka sanya wata sarqa ta azurfa a wurin da ya fashe xin” [ Bukhari ne ya rawaito shi].

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...