Haƙiƙanin Ilimi shi ne Jin Tsoron Allah
Asali ilimin Shari'a aiki ne na ibada ma Allah Maɗaukaki da hanyar neman yardarsa. Wannan shi ne abin da Nassoshin Alƙur'ani da Sunna suka yi nuni a kansa, kuma a wannan matsayi magabatan al'umma Sahabbai da Tabi'ai da Limman ilimi da Addini suka ɗauki ilimin.
Don haka mu ma a wannan matsayi ya kamata mu ɗauki ilimin na Shari'a, a matsayin aiki na ibada da neman kusaci a wajen Allah da neman yardarsa.
{وَاتَّقُوا اللَّهَ وَيُعَلِّمُكُمُ اللَّهُ } [البقرة: 282]
"Ku ji tsoron Allah sai Allah ya ba ku ilimi".
Ya ce:
{إِنَّمَا يَخْشَى اللَّهَ مِنْ عِبَادِهِ الْعُلَمَاءُ } [فاطر: 28]
"Lallai Malamai ne kaɗai suke jin tsoron Allah a cikin bayinsa".
Saboda haka ilimi ba ya rabuwa da tsoron Allah. Don haka mai karatun da ba ya jin tsoron Allah shi ba Malami ba ne.
Saboda haka abin mamaki ne a yau yadda wasu suka mayar da ilimin Shari'a ya zama abin ado da alfahari da neman girma da neman suna da shahara da neman abin Duniya. Alal haƙiƙa duk wanda ya mayar da ilimin Shari'a abin neman wata alfarmar Duniya, to ba ya cikin haƙiƙanin waɗanda Allah ya siffanta su da ilimin, kuma ya yabe su da shi a cikin Littafinsa Alƙur'ani Mai girma.
Rubutawar Dr. Aliyu Muhammad Sani
Comments
Post a Comment