Skip to main content

IBNU TAIMIYYA YA FI KOWA RADDI WA 'YAN BIDI'A, AMMA KUMA DUK DA HAKA YA FI KOWA YI MUSU UZURI DA ADALCI

 Abu ne sananne Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) yana daga cikin Imaman Ahlus Sunna wal Jama'a, wanda a bayansa har zuwa yau ba a samu wanda ya kai shi girmamawa da bin Nassoshin Al- Qur'ani da Sunna da Tafarkin Salaf (magabata) ba.

Wannan ya sa ba a samu wanda yake kare Sunna da tafarkin magabata kamarsa ba, shi ya sa ya fi kowa raddi ma wadanda suka saba tafarkin Annabawa, tun daga kan 'Yan Falsafa, Mulhidai, Mushrikai da Majusawa, Yahudawa da Kiristoci da dukkan dangogin kungiyoyin 'yan bidi'a.
Amma abin mamaki, duk da haka ya kasance mutum ne mai adalci saboda binsa ga Al- Qur'ani da Sunna da tafarkin Salaf, shi ya sa ba ya yin kudin goro wajen yanke hukuncinsa ga 'yan bidi'a, a'a, kowa yana yi masa hukunci ne gorgodon girman bidi'arsa da halinsa na bin son rai ko kuskure, wanda kuma yake bukatar azuri yana yi masa uzuri tare da yi masa fatan samun gafara a kan kuskuren nasa.
Ibnu Taimiyya yana magana a kan wadanda suka hada ra'ayin "hululi" (Allah ya shiga cikin halitta) da rabuwansa da halittan (الذين يجمعون بين الحلول والمباينة) a cikin maganarsu a game da Allah (T), sai yake yin uzuri ma wasu daga cikin Shehunai Sufaye masu ilimi da suka yi kuskure aka samu irin wadannan munanan maganganu a cikin maganganunsu, sai ya ce:
لكن شيوخ أهل العلم الذين لهم لسان صدق وإن وقع في كلام بعضهم ما هو خطأ منكر فأصل الإيمان بالله ورسوله إذا كان ثابتا غفر لأحدهم خطأه الذي أخطأه بعد اجتهاده
الصفدية (1/ 265)
"Sai dai Shehunai masu Ilimi, wadanda suke da kyakkyawan ambato a cikin al'umma, ko da an samu abin da yake mummunan kuskure ne da ya faru a cikin maganganun wasu daga cikinsu, to asalin Imaninsu da Allah da Manzonsa, idan ya kasance tabbatacce (a cikin addininsu), Allah zai gafarta ma kowane dayansu kuskurensa da ya yi a bisa Ijtihadinsa".
Wannan shi yake nuna mana cewa; Shugabanni a cikin Sunna, sun fi kowa Ilimi da Adalci, suna banbance wanda ya afka cikin bidi'a bisa son rai, suna banbance wanda ya yi bidi'a da kuskure, balle kuma wanda ya yi a bisa Ijtihadi, shi kam ana yi masa fatan samun lada a kan Ijtihadin nasa.
Lallai hukunci da bidi'a wa mutane yana da wahala, sabanin yadda a yau abin ya zama a hanun dukkan wanda ya ga dama.
Allah ya yi mana afuwa, ya kiyayemu.
Rubutawar: Dr. Aliyu Muh'd Sani

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...