Skip to main content

ILIMI YA FI MULKI DA'DI!

 AL- IMAMUZ ZAHABIY YA KAWO A CIKIN "SIYAR" 'DINSA, A TARJAMAR IMAMU 'DABARANIY (MAI MA'AJIM GUDA 3):

ABUL HUSAIN, AHMAD BN FARIS AL- LUGAWIY (MAI LITTAFIN MAQAYISUL LUGHAH) YA CE:
سمعت الاستاذ ابن العميد يقول: ما كنت أظن أن في الدنيا حلاوة ألذ من الرئاسة والوزارة التي أنا فيها، حتى شاهدت مذاكرة أبي القاسم الطبراني وأبي بكر الجعابي بحضرتي، فكان الطبراني يغلب أبا بكر بكثرة حفظه، وكان أبو بكر يغلب بفطنته وذكائه حتى ارتفعت أصواتهما، ولا يكاد أحدهما يغلب صاحبه، فقال الجعابي: عندي حديث ليس في الدنيا إلا عندي، فقال: هات، فقال: حدثنا أبو خليفة الجمحي، حدثنا سليمان بن أيوب، وحدث بحديث، فقال الطبراني: أخبرنا سليمان بن أيوب، ومني سمعه أبو خليفة، فاسمع مني حتى يعلو فيه إسنادك، فخجل الجعابي، فوددت أن الوزارة لم تكن، وكنت أنا الطبراني، وفرحت كفرحه، أو كما قال.
"NA JI USTAZ IBNUL AMID (WAZIRIN RUKUNUD DAULA AL- HASAN BN BAWAIH AL- DAILAMIY, SARKIN DAULAR BUWAIHIYYA WACCE AKA YI TA A IRAQI) YANA CEWA: DA BAN TA'BA ZATON A DUNIYA AKWAI ABIN DA YA FI MULKI DA WAZIRANCI DA NAKE CIKI DA'DI BA! HAR SAI DA NA HALARCI BITAN ILMI (MUZAKARA) TSAKANIN ABUL QASIM AL- 'DABARANIY DA ABUBAKAR AL- JI'ABIY WACCE SUKA YI A GABANA. AL- 'DABARANIY YA KASANCE YANA CIN GALABA A KAN ABUBAKAR DA YAWAN HADDARSA GA HADISI. SHI KUMA ABUBAKAR YA KASANCE YANA CIN GALABAN 'DABARANIY NE DA KAIFIN K'WAK'WALWA DA HAZAK'ARSA. HAR MURYARSU TANA 'DAGUWA SAMA, AMMA BABU WANDA YAKE RINJAYAR ABOKINSA. SAI AL- JI'ABIY YA CE: INA DA WANI HADISI DA DUK DUNIYA BABU SHI A WAJEN KOWA SAI NI KA'DAI. SAI 'DABARANIY YA CE: TO KAWO SHI. SAI YA CE: ABU KHALIFA AL- JUMAHIY YA BA MU LABARI, YA CE: SULAIMAN BN AYYUB YA BA MU LABARI, SAI YA FA'DI WANI HADISI. SAI AL- 'DABARANIY YA CE: SULAIMAN BN AYYUB YA BA MU LABARI, SHI KUMA ABU KHALIFAN A WAJENA YA JI HADISIN, DON HAKA KA KAR'BI HADISIN DAGA WAJENA SAI KA SAMU 'DAUKAKAR ISNADINKA. DAGA NAN KAWAI SAI AL- JI'ABIY YA KARAYA. SAI IBNUL AMID YA CE: SAI NA SO DA ACE BAN ZAMA WAZIRI BA, NA ZAMA NI NE 'DABARANIY, NA YI FARIN CIKI KAMAR NASA".
ILIMI BABU YA KAI!!!
JAMA'A, BARKANKU DA JUMA'A.
Rubutawar: Dr. Aliyu Muh'd Sani

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...