Wani tunani ya watsu a cikin mutane cewa; Manhajin Ahlus Sunnati wal Jama'a ba ruwansa da hankali wajen kafa hujja a kan Mas'alolin Addini da tabbatar da Aqidar Ahlus Sunna, don haka Ahlus Sunna ba sa ba da muhimmanci ga hankali da tunani, kawai makauniyar biyayya suke yi wa magabata ido rufe, kamar masu bin Addinin iyaye da kakanni.
Wadanda suke dauke da wannan tunani bangare biyu ne:
1- Wadanda suka saba Manhajin Salaf, mabiya hanyoyin Falsafa cikin 'Yan Boko Aqida, wadanda suka rudu da rayuwar Turawa, mabiya Ilmul Kalam; Mu'utazilawa da Asha'ira, da masu ta'assubanci cikin mabiya Fiqhu da Qiyasi, wadanda suke sukan Ahlus Sunna da rashin tunani da fahimta da rashin aiki da hankali wajen kafa hujja, da siffanta su da rashin Fiqhu.
2- Wasu daga cikin masu bin Mazhabar Salaf, wadanda suka yi zaton hanya daya ce kawai ta kafa hujja a Mazhabar Salaf a kan Mas'alolin Addini, wato hanyar Nassi da Naqali kawai, don haka suka yi watsi da hanyar kafa hujja da dalilan hankali, da watsi da Littatafan Fiqhun Addini, saboda a zatonsu ba hanya ce ta Shari'a ba, har ya kai ga bidi'antar da masu kafa hujja da dalilai na hankali ingantatu.
To alal hakika wannan tunani kuskure ne, kuma kowane bangare daga cikin wadannan bangarori biyu yana da kaso mai tsoka na jahiltar hakikanin Manhajin Ahlus Sunna wajen kafa hujja a Addini.
Shaikhul Islami yana raddi ga wannan tunani sai ya ce:
دلالة الكتاب والسنة على أصول الدين ليست بمجرد الخبر؛ كما تظنه طائفة من الغالطين من أهل الكلام والحديث والفقهاء والصوفية وغيرهم بل الكتاب والسنة دلا الخلق وهدياهم إلى الآيات والبراهين والأدلة المبينة لأصول الدين وهؤلاء الغالطون الذين أعرضوا عما في القرآن من الدلائل العقلية والبراهين اليقينية صاروا إذا صنفوا في أصول الدين أحزابا حزب: يقدمون في كتبهم الكلام في النظر والدليل والعلم...
والحزب الثاني: عرفوا أن هذا الكلام مبتدع وهو مستلزم مخالفة الكتاب والسنة...
والطائفتان يلحقهما الملام؛ لكونهما أعرضتا عن الأصول التي بينها الله بكتابه فإنها أصول الدين وأدلته وآياته
مجموع الفتاوى (19/ 160 - 161)
"Dalalar Al-Kur'ani da Sunna a kan ginshikan Addini ba kawai ta hanyar ba da labari ba ne kamar yadda wasu bangarori na masu kuskuren fahimta suke zato, cikin mabiya Ilmul Kalam da Malaman Hadisi da Fiqhu da Sufaye da wasunsu, a'a, Alkur'ani da Sunna sun yi nuni wa mutane zuwa ga dalilai da hujjoji na hankali da suke bayyana ginshikan Addini. Don haka wadannan masu kuskuren fahimta da suka kau da kai daga abin da ke cikin Alkur'ani na dalilan hankali da hujjoji na yakini idan za su wallafa littatafai a kan ginshikan Addini sai suka zama kungiyoyi daban - daban:
Masu bin ilmul kalam da hankali zalla...
Masu kaurace ma dalilan hankali...
Wadannan bangarori guda biyu abin zargi ne, saboda sun kawar da kai daga ginshikan Addini da Allah ya yi bayaninsu da littafinsa, saboda ginshikan Addini ne da dalilansu da hujjojinsu".
A takaice, Aqidar Ahlus Sunna ta tabbata da dalilai na hankali ingantattu bayan sun tabbata da dalilai na Nassi da Naqali, amma sai dai dalilin Naqalin shi ne asali. Kuma ingantacce dalili na hankali ba ya cin karo da tabbataccen Nassi na Naqali, don haka wanda ya yi zaton haka to ya tuhumi hankalin nasa ba Nassi da Naqalin Alkur'ani da Sunna ba.
Comments
Post a Comment