Skip to main content

MATAKAN BIDI'O'I

 Tambaya:

"shin bid'ah akwai babba akwai karama?".
Amsa:
Bidi'a suna ne na jinsin dukkan abin da aka kirkira aka shigar da shi cikin Addinin da Manzon Allah (saw) ya zo da shi, alhali ya saba ma Qur'ani da Sunna da Ijma'i. Sawa'un wannan abin ya zama kishiyar asali daga cikin asalai na Addini, wato manyan lamuran Addini, ko kuma reshe ne daga cikin rassansa, wato kananan lamura na Addini.
Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ® ya ce:
مما ينبغي أيضا أن يعرف أن الطوائف المنتسبة إلى متبوعين في أصول الدين والكلام: على درجات منهم من يكون قد خالف السنة في أصول عظيمة ومنهم من يكون إنما خالف السنة في أمور دقيقة.
مجموع الفتاوى (3/ 348)
Sai ya nuna cewa; saba Sunna ya kasu kashi biyu:
(1) Saba Sunna a Manyan Tushen Sunna, kamar Siffofin Allah da Qaddara da Mas'alar Imani, da Khalifanci da Falalar Sahabbai.
(2) Saba Sunna a kananan abubuwa.
Saboda haka bidi'o'i da 'Yan Bidi'a ba a daraja da matsayi daya suke ba, wata Bidi'ar ta fi wata.
Shi ya sa aka tambayi Ibnu Taimiyya a kan Bidi'ar da mutum yake zama mabiyin son zuciya saboda ita, sai ya ce:
البدعة التي يعد بها الرجل من أهل الأهواء ما اشتهر عند أهل العلم بالسنة مخالفتها للكتاب والسنة؛ كبدعة الخوارج والروافض والقدرية والمرجئة
مجموع الفتاوى (35/ 414)
Sai ya ambaci manyan bidi'o'in da su ne tushen dukkan kungiyoyin 'Yan Bidi'a. wato su ne: Bidi'ar "Khawarijawa", da ta "Rafidha" da "Qadariyya", da "Murji'a". "Jahamiyya" kuma su ana ganin ba sa cikin al'ummar Annabi (saw), kuma daga gareta Mu'utazila da Asha'ira da Maturidiyya suka samo asalin bidi'arsu ta kore Soffofin Allah.
Saboda haka wadancan su ake kira Bidi'o'i masu tsanani, wadanda malamai suka yi ittifaqi a kan cewa; sun fi aiyukan zunubai muni.
Ibnu Taimiyya ya ce:
اتفق أئمة الإسلام على أن هذه البدع المغلظة شر من الذنوب التي يعتقد أصحابها أنها ذنوب. وبذلك مضت سنة رسول الله صلى الله عليه وسلم حيث أمر بقتال الخوارج عن السنة
مجموع الفتاوى (28/ 470 - 471)
Kuma ya ce:
إن البدع الغليظة المخالفة للكتاب والسنة واتفاق أولي الأمر الهداة المهتدين إنما حدثت من الأخلاف، وقد يعزون بعض ذلك إلى بعض الأسلاف، تارة بنقل غير ثابت، وتارة بتأويل لشيء من كلامهم متشابه.
جامع المسائل لابن تيمية - عزير شمس (3/ 88)
Saboda haka Bidi'o'i ba mataki daya suke ba, kamar yadda mas'alolin Addini ba mataki daya suke ba. Akwai manyan mas'alolin Addini na Aqida, kamar Tabbatar da Siffofin Allah, da kuma Imani da Qaddara, da kuma Mas'alar Imani, da kuma mas'alar Khalifanci da Matsayin Sahabbai da sauransu.
Da kuma Manyan Mas'aloli a bangaren Mas'alolin aiki, kamar Sallah, Zakka, Azumi, Hajji….
Haka kuma akwai kananan mas'alolin Addini na Aqida, kamar mas'alar shin Annabi (saw) ya ga Allah ko kuma bai gan shi ba?
Da mas'alar shin Kafirai za su ga Allah a Lahira ko kuma ba za su gani ba?
Da sauran kananan mas'aloli da suke cikin wadancan manyan mas'aloli da na ambata a sama.
Haka akwai kananan mas'aloli na aiki, kamar abubuwan da suke sunnoni ne Mustahabbai da suke cikin wadancan manyan mas'aloli na aiki.
To kamar haka Bidi'o'i ma suke, akwai Manyan Bidi'o'i, kamar Bidi'ar masu kore Sunayen Allah, kamar Jahamiyya, Mu'utazila, Asha'ira, Maturidiyya..
Da kuma Bidi'ar masu kore Qaddara, da ta masu wuce iyaka wajen tabbatar da shi.
Haka a mas'alar Imani, akwai masu cewa; aiki ba ya cikin Imani, akwai kuma masu wuce iyaka wajen tabbatar da aiki cikin Imani, har suke ganin duk wanda ya aikata zunubi to ya kafirta.
Haka a mas'alar Khalifanci, akwai wadanda suke ganin ba Abubakar (ra) ne Khalifan Annabi (saw) ba. Kamar yadda akwai masu jafa'i wa Sahabbai, da kuma masu jafa'i wa Ahlul Baiti.
TO DUKA WADANNAN MANYAN BIDI'O'I NE.
Amma sauran kananan Bidi'o'i, kamar kirkiran wasu zikirori, ko aikata wasu Salloli, ko aikata wasu ibadu da Allah bai yi izni a kansu ba, to duka kananan Bidi'o'i ne.
Masu Kananan Bidi'o'i ba su kai masu Manyan Bidi'o'i laifi ba, saboda Kananan Bidi'o'i ba sa warware asalin Sunna na mutum, amma manyan Bidi'o'i suna warware Sunnar mutum, su fitar da shi daga cikin Ahlus Sunnati wal Jama'a.
Saboda haka, abin da muke so mu nuna a nan shi ne; Bidi'o'i mataki – mataki suke ba a daraja daya suke ba, akwai manya akwai kuma kanana, akwai wadanda suka fi kusa da Sunna a kan sauran da su kuma suka fi nisa da ita. Wasu sun fi wasu tsanani.
Haka su ma 'Yan Bidi'ar, wasu sun saba da Sunna ne a kan Manyan abubuwa, wasu kuma a kanana, don haka wasu sun fi wasu kusa da Sunna, wasu kuma sun fi nisa da ita.
Alal hakika sanin wannan asali yana da muhimmanci ga duk wanda zai yi magana a kan ra'ayoyi da Aqidun mutane, da yi musu hukunci don ya zama mai adalci cikin hukuncinsa.
SABODA HAKA, DUK DA CEWA; DUK WANDA YA SABA SUNNA DAN BIDI'A NE, TO AMMA KOWA ZA A MU'AMALANCE SHI NE GORGODON BIDI'AR TASA.
Ibnu Taimiyya ya ce:
فكل من خرج عن اتباع الرسول فهو ظالم بحسب ذلك. والمبتدع ظالم بقدر ما خالف من سنته
مجموع الفتاوى (4/ 129)
Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ® ya ce:
أهل السنة والجماعة يقولون ما دل عليه الكتاب والسنة والإجماع وهو أن المؤمن يستحق وعد الله وفضله والثواب على حسناته ويستحق العقاب على سيئاته، وإن الشخص الواحد يجتمع فيه ما يثاب عليه وما يعاقب عليه وما يحمد عليه وما يذم عليه وما يحب منه وما يبغض منه
مجموع الفتاوى (11/ 16)
"Ahlus Sunnati wal Jama'a suna fadin abin da Qur'ani da Sunna da Ijma'i suka yi nuni a kansa ne (suna fadi a matsayin Aqida), wato shi ne; Lallai Mumini yana cancantar alkawarin Allah (na Lada) da falalarsa da sakamakon lada a kan kyawawan aiyukansa, kuma yana cancantar uquba a kan munanan aiyukansa. Kuma lallai mutum guda, za a iya samun haduwar abin da zai sa ayi masa sakamako na lada da abin da zai sa ayi masa uquba a tare da shi, kuma za a iya samun haduwar abin da zai sa a yabe shi a kansa, da abin da zai sa a zarge shi a kansa a tare da shi, kuma za a iya samun haduwar abin da zai sa a so shi saboda shi, da abin da zai sa a ki shi saboda shi a tare da shi".
Kuma ya ce:
إذا اجتمع في الرجل الواحد خير وشر وفجور وطاعة ومعصية وسنة وبدعة: استحق من الموالاة والثواب بقدر ما فيه من الخير واستحق من المعادات والعقاب بحسب ما فيه من الشر فيجتمع في الشخص الواحد موجبات الإكرام والإهانة فيجتمع له من هذا وهذا كاللص الفقير تقطع يده لسرقته ويعطى من بيت المال ما يكفيه لحاجته. هذا هو الأصل الذي اتفق عليه أهل السنة والجماعة وخالفهم الخوارج والمعتزلة ومن وافقهم عليه
مجموع الفتاوى (28/ 209)
Sai ya ce: ya cancanci jibinta (soyayya) gorgodon abin da yake tare da shi na sharri.
A wani wajen kuma ya ce:
كان من أصول أهل السنة التي فارقوا بها الخوارج: أن الشخص الواحد تجتمع فيه حسنات وسيئات فيثاب على حسناته ويعاقب على سيئاته. ويحمد على حسناته ويذم على سيئاته. وأنه من وجه مرضي محبوب ومن وجه بغيض مسخوط. فلهذا كان لأهل الإحداث هذا الحكم.
مجموع الفتاوى (27/ 476)
"Daga cikin Usul da Ahlus Sunna suka banbanta da Khawarijawa, shi ne; Mutum guda za a iya samun kyawawan aiyuka tare da munana a tare da shi. A so shi ta wata fiskar, kuma a ki shi ta wata fiskar, ya ce: "saboda haka ne MA'ABOTA KIRKIRA ('Yan Bidi'a) suke da wannan hukunci".
SABODA HAKA WANNAN SHI NE MUWAZANA, KUMA SHI NE MAZHABIN AHLUS SUNNA, A SO MUTUM GORGODON IMANINSA DA DA'ARSA GA ALLAH, A KI SHI GORGODON SABONSA DA BIDI'ARSA. IN BABBAR BIDI'A YAKE DA ITA, AYI MASA BABBAR KIYAYYA, IN KUMA KARAMA CE AYI MASA KARAMAR KIYAYYA. IN YANA DA AIYUKA NA IMANI DA DA'A MA ALLAH A SO SHI GORGODON HAKA, IN KUMA BA SHI DA AIYUKAN DA'A MA ALLAH, BA ZA A SO SHI BABBAN SO BA, SAI DAI AYI MASA SOYAYYAR DA ZA A YI MA MUSULMAI MASU SABO. WATO KIYAYYAR TA FI RINJAYE, KIYAYYAR DA BA ZA TA HANA A JIBINCE SHI BA, A BA SHI HAKKOKINSA NA MUSLUNCI, KAMAR AMSA SALLAMA, TAIMAKONSA IN YA BUKATA, ZUWA A GAISHE SHI IN BA SHI DA LAFIYA, DA SAURAN HAKKOKI NA MUSLUNCI.

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...