Skip to main content

SA'BANI A TSAKANIN AHLUS SUNNA A KAN K'ANANAN MAS'ALOLIN ADDINI BAI KAI YA ZAMA SANADIN RABUWAN KAI BA!!!

 IBNU ABIL IZZ AL- HANAFIY (R) YA FA'DA A CIKIN LITTAFINSA "SHARHU'D 'DAHAWIYYA", INDA YAKE MAGANA A KAN HUKUNCIN BIN FAJIRI KO 'DAN BIDI'A SALLAH:

إن مصلحة الجماعة والائتلاف، ومفسدة الفرقة والاختلاف، أعظم من أمر المسائل الجزئية.
YA CE:
"LALLAI MASLAHAR DA KE CIKIN HA'DA KAI DA JAMA'A, DA KUMA 'DINKE 'BARAKA, DA 'BARNAN DA KE CIKIN RABUWAR KAI DA SA'BANI YA FI GIRMA FIYE DA LAMARIN K'ANANAN MAS'ALOLI".
* WANNAR MAGANAR TA SHAIKHUL ISLAM IBNU TAIMIYYA (R) CE A CIKIN "JAMI'UL MASA'IL 5/ 274".
A CAN K'ARSHEN MAGANARSA SAI YA CE:
إن الاجتماع والائتلاف مما يجب رعايته وترك الخلاف المفضي إلى الفساد.
"LALLAI HA'DIN KAI DA 'DINKE 'BARAKA YANA DAGA CIKIN ABUBUWAN DA YA WAJABA A KIYAYE SHI A KULA DA SHI, KUMA A BAR SA'BANIN DA ZAI KAI ZUWA GA 'BARNA".
WANNAN SHI YAKE NUNA MANA CEWA; BAI KAMATA AHLUS SUNNA SU MAI DA K'ANANAN MAS'ALOLI (MAS'ALOLIN AIYUKAN IBADA, WA'DANDA ANA IYA YIN SA'BANI A CIKINSU, DA K'ANANAN MAS'ALOLIN AQIDA) SU ZAMA SANADIN RABUWAN KAN AHLUS SUNNA BA. BABBAN KUSKURE NE MUTANE SU MAI DA SA'BANIN DA KE TSAKANINSU A KAN; JIYARWAN LADANI A SALLA, KO RIK'E SANDA A HU'DUBA DA MAKAMANTANSU SU ZAMA SANADIN RABUWAN KAI. HAR YA KAI GA WASU SUNA ZARGIN WANI 'BANGARE DA RASHIN RIK'O DA SUNNA. WANNAN BA KOMAI BA NE YA KAWO HAKA, SAI RASHIN SANIN BANBANCIN DA KE TSAKANIN SUNNAR DA IN MUTUM YA SA'BA MATA YA ZAMA 'DAN BIDI'A, DA KUMA SUNNAR DA IN MUTUM YA SA'BA MATA BAI FITA A CIKIN SUNNA BA, WATO WACCE TA SHAFI MUSTAHABBAN AIYUKAN IBADA DA KANANAN MAS'ALOLIN AQIDA, WA'DANDA AKA SAMU MANYAN MALAMAN SUNNA MA SUN YI SA'BANI A CIKINSU.
DUKA MAGANIN WANNAN GABA 'DAYA SHI NE NEMAN ILMI A GABAN MALAMAI.
ALLAH YA SA MU DACE.
Rubutawar: Dr. Aliyu Muh'd Sani

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...