Tushen Ilhadi shi ne kalubalantar abin da Annabi (saw) ya zo da shi na Alkur'ani da Sunna da ra'ayi da tunani da hankali da Falsafa. Wannan ya sa ba za ka taba samun wanda yake kalubalantar Hadisan Annabi (saw) da ra'ayoyinsa da yake zayyana su da sunaye kala-kala, da sunan ilimi ko zurfin tunani ko hazaka ko kaifin kwakwalwa da kaifin basira face yana kiyayya ga abin da ya saba ra'ayinsa cikin Hadisan Annabi (saw), har ya wayi gari yana fatan da Annabi (saw) bai fadi Hadisin ba. Ta yadda da zai samu daman goge Hadisin daga Sahihul Bukhari da Muslim to da zai yi.
Al-Subkiy ya ambaci maganar Ahmad bn Sinan a cikin littafinsa ya ce:
ليس في الدنيا مبتدع إلا يبغض أصحاب الحديث وإذا ابتدع الرجل نزعت حلاوة الحديث من قلبه
طبقات الشافعية الكبرى للسبكي (2/ 6)
"A Duniya babu wani dan bidi'a face yana kin Malaman Hadisi, idan mutum ya kirkiri bidi'a za a cire zakin Hadisi a zuciyarsa".
Shi ya sa wani babban gungume cikin 'Yan Bidi'a magabata ya ce: Idan sun kafa muku hujja da Hadisi to ku karyata ku ce: Hadisin zato ne, in kuma sun kafa muku hujja da Ayar Alkur'ani to ku kalubalance su ku yi tawilinta ku ce: Majaaz ne.
Wannan ya sa za ka ga kowane daya daga cikinsu ba ya so ana karanta Hadisai ana isar da su ga al'umma, kawai so suke ana boye Hadisan ana hana yada su da isar da su ga mutane, alhali Annabi (saw) ya yi umurni da isar da su. Kuma Allah ya zargi masu boye abin da ya saukar ga Manzonsa (saw) sawa'un Alkur'ani ne ko Sunna, alhali su kuma wadannan sun zabi suna boye su, kawai don kalubalantar Allah da Manzonsa da karyata maganarsu.
Wannan ya sa Sayyidina Umar (ra) ya ce: ku kiyayi mabiya ra'ayi (sawa'un ra'ayi da sunan Falsafa ko Ilmul Kalam ko Fiqhu), saboda makiya Hadisai ne. Saboda a lokacin da haddace Hadisai ya gagare su, suka kasa fahimtarsu sai suka kalubalance su da ra'ayoyinsu, suna magana a Addini da ra'ayi.
A takaice; duk wanda ka ga yana kin wani abu na Alkur'ani ko Sunna to yana da kaso na kiyayya ga Annabi (saw) gwargwadon kinsa ga Hadisan nasa. Kin Annabi (saw) kuwa aiki ne na Shaidanun Mutane da Aljanu. Don haka babu mai kalubalantar Annabi (saw) da ra'ayinsa da Falsafarsa sai Shaidanin mutum makiyin Annabawa. Allah ya ce:
وَكَذَلِكَ جَعَلْنَا لِكُلِّ نَبِيٍّ عَدُوًّا شَيَاطِينَ الْإِنْسِ وَالْجِنِّ يُوحِي بَعْضُهُمْ إِلَى بَعْضٍ زُخْرُفَ الْقَوْلِ غُرُورًا } [الأنعام: 112]
Rubutawar. Dr. Aliyu Muh'd Sani
Comments
Post a Comment