Skip to main content

WANENE MALAMIN 'YAN FALSAFA (PHILOSOPHERS) NA FARKO?

 Kasancewar hakikanin Falsafa shi ne dogaro a kan hankali zalla wajen sanin hakikanin lamura da yi musu hukunci, in mun duba za mu ga Iblis shi ne farkon wanda ya fara zuwa da Nazariyyar gabatar da hankali a kan komai wajen yanke hukunci. Ya yi amfani da wannar Nazariyya ce (theory) inda ya gabatar da hankalinsa a kan maganar Allah Madaukaki ya yanke hukunci da ya saba umurnin Allah.

Shi ne farkon wanda ya fara kalubalantar maganar Allah ya rushe ta bisa dogaro ga hankalinsa, bisa Nazariyyar: hankali shi ne gaba da Nassi in an samu sabani a tsakaninsu.
Hakan ya faru ne a lokacin da Allah ya umurce shi da yin Sujada ga Annabi Adamu (as), sai ya kalubalanci Allah da wata ka'ida ta Falsafa mai doriya biyu kamar haka:
1- Ni da wuta ka halicce ni, shi kuma (Annabi Adamu) da tabo ka halicce shi, wuta kuwa ta fi tabo daraja.
2- Don haka wanda aka halicce shi da wuta ya fi wanda aka halicce shi da tabo daraja.
Natijar wannar Qadhiyya ita ce: Ni na fi Adamu daraja, don haka ni ba zan yi masa sujada ba.
Shi ne inda Allah ya ba mu labarin wannan (Logic) na Philosopher Iblisu inda ya ce:
{قَالَ مَا مَنَعَكَ أَلَّا تَسْجُدَ إِذْ أَمَرْتُكَ قَالَ أَنَا خَيْرٌ مِنْهُ خَلَقْتَنِي مِنْ نَارٍ وَخَلَقْتَهُ مِنْ طِينٍ } [الأعراف: 12]
"Allah ya ce: me ya hana ka ba za ka yi sujada ba, a yayin da na umurce ka? sai (Iblis) ya ce: Ni na fi shi daraja, saboda ka halicce ni da wuta, shi kuma ka halicce shi da tabo".
To a nan in ka lura za ka ga wannan tsohon wato Iblisu, ya gabatar da hankalinsa da ra'ayinsa a kan Nassi bisa dogaro ga Nazariyyar Falsafa.
Saboda haka, kalubalantar Allah da Manzonsa da gabatar da hankali da ra'ayi da Nazariyya ta Falsafa a kan maganar Allah da Manzonsa gado ne daga Philosopher Iblisu kakan 'Yan Falsafan farko.
Wannan ya sa Philosopher Iblisu bai gushe ba a kullum yana wahayi ga almajiransa magada Falsafarsa da cewa; ku yi jayayya ga masu riko da Aya da Hadisi, ku kure su da Nazariyyar Falsafar da na koya muku, Allah ya ce:
{وَإِنَّ الشَّيَاطِينَ لَيُوحُونَ إِلَى أَوْلِيَائِهِمْ لِيُجَادِلُوكُمْ وَإِنْ أَطَعْتُمُوهُمْ إِنَّكُمْ لَمُشْرِكُونَ } [الأنعام: 121]
Da wannan za ka fahimci cewa; lallai Falsafa gado ce daga Philosopher Iblis, wanda ya fara aiki da Nazariyyar gabatar da hankali a kan maganar Allah Madaukaki da Annabawansa. Saboda kowa ya san cewa; Falsafa ta ginu ne a kan girmama hankali da gabatar da shi a kan komai daga cikin hanyoyin sanin abubuwa da yanke musu hukunci.
Saboda haka Iblis shi ne Philosopher na farko, shi ne babban Shehin 'Yan Falsafa gaba daya, kuma kakansu.
Rubutawar: Dr. Aliyu Muh'd Sani

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...