Skip to main content

ZABEN SHUGABAN DA YA FI DACEWA

 Zaban shugaba a cikin mutane yana da matukar muhimmanci a rayuwarsu ta Addini da rayuwarsu ta Duniya.

Rayuwar mutane ta Addini ba ta cika sai da kyakkyawan shugabanci da zai kare manufofin Shari'a, na kare Addini ta hanyar umurni da kyakkyawa da hani ga mummuna da tsayar da haddi da tsayar da adalci da mayar da hakkoki ga ma'abotansu da Jihadi saboda Allah, da kare rayuka da hankulan mutane.
Haka in ka dawo bangaren rayuwar Duniyar mutane, rayuwar ba ta inganta sai da ingantaccen shugabanci da zai samar da tsaro da cigaban kasa ta hanyar inganta harkar ilimi da bunkasa harkar noma da kasuwanci da habaka tattalin arziki da samar hasken wutan lantarki da makamashi da kuma bunkasa harkar kimiyya da fasaha da zai inganta harkar kiwon lafiya da kere-kere, da samar da kayan more rayuwa da duk abin cigaban rayuwa yake bukata.
To shi shugabanci yana bukatar manyan siffofi guda biyu:
1- Karfin iko
2- Rikon amana.
Sai kuma ka kara da wanda zai kare maka Addininka da rayuwarka.
Don haka wannan zabe da ya dawo hanun gama-garin mutane yana da matukar muhimmanci, don haka ya kamata ka fita ka zabi wanda kake ganin shi ya fi dacewa ya zama shugaba a kasarka, wanda yake da karfi da rikon amana, wanda zai kare maka Addininka ya inganta maka rayuwarka ta Duniya.
Ya Allah ka damka shugabancinmu a hanun masu rikon amana, wadanda za su yi kokarin samar da tsaro a kasa da bunkasa tattalin arziki, don mu samu nitsuwa da daman bauta maka, da tsayar da Shari'arka a kan kanmu.
Rubutawar: Dr. Aliyu Muh'd Sani

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...