Skip to main content

 AHLUS SUNNA A TSAKIYA SUKE A GAME DA HANKALI

A game da hankali, tafarkin Ahlus Sunna Mabiya Salaf matsakaici ne tsakanin masu wuce iyaka game da shi, da kuma masu sakaci da wofintar da shi.
'Yan Falsafa (Philosophers) da kuma da yawa daga cikin mabiya "Ilmul Kalam" da 'Yan Boko Aqida (Intellectuals) suna fifita hankali suna kai shi matsayin da bai kai ba, ta yadda suke sanya shi a matsayin tushen daukan ilmukansu, ta yadda suke mayar da Qur'ani da Sunna da Imani a matsayin mabiya ga hankalin.
A daya hanun kuma, 'Yan Darikun Sufaye sun saba ma wadannan, ta yadda suka wulakanta hankali, suka zarge shi suka aibanta shi, ta yadda suke ganin cewa; ba a samun matsayi da daukaka sai ta hanyar jefar da hankali. Shi ya sa Sufayen suke tabbatar da abubuwan da hankali yake karyatawa. Suke yabon maye da hauka da sauran yanayi na gushewar hankali, saboda a wajensu sai mutum ya isa wani matsayi na gushewar hankali kafin ya isa zuwa ga Hakika ko "Fana'i" da sauran matsayi da halaye da su ne kololuwar daraja a wajensu.
To su Kungiya ta farko sun wuce gona da iri ta yadda suka tabbatar da wajibcin abubuwa ko yuwuwarsu ko koruwansu ta hanyar hujjoji na hankali tsantsa, suka kudurta cewa su ne gaskiya alhali bata ne, sai suka kalubalanci abin da Manzo (saw) ya zo da shi daga wajen Allah.
Su kuma Kungiya ta biyu, sun yi sakaci da lamarin hankali har suka tara gaskata karya da aikata munanan aiyuka a tafarkinsu, sai suka fita daga fagen hankali da Allah ya fifita 'Yan Adam da shi a kan sauran dabbobi.
Sai Allah ya shiryar da Ahlus Sunna Mabiya Salaf zuwa ga tafarki mikakke matsakaici, da hanya madaidaiciya.
Don haka wadancan Kungiyoyi guda biyu dukkansu abin zargi ne, saboda hankali sharadi ne na sanin ilmuka da cika da gyaruwan aiyuka. Da hankali ilimi da aiki suke cika. Amma kuma hankalin ba cin gashin kansa yake yi ba, wajen sanin ilmuka da aikata kyawawan aiyuka.
Don ka fahimci wannan, ga bayani kamar haka; Shi hankali wani karfi ne da yake cikin rai, kamar karfin kallo a cikin ido. Idan hasken Imani da Qur'ani da Sunna ya hadu da hankali to zai kasance ne kamar karfin kallo da yake cikin ido idan ya hadu da hasken rana ko wuta. Ta yadda idan an bar idon da karfin kallonsa kawai da ba zai iya ganin komai shi kadansa ba.
Shin idan ka shiga daki mai duhu za ka iya ganin wani abu?
To kamar haka ne, in hankali bai hadu da hasken Imani da Qur'ani da Sunna ba, to ba zai isa ga ingantattun ilmuka da kyawawan maganganu da aiyuka ba.
Kamar haka kuma in an cire hankalin daga cikin maganganun mutane da aiyukansu sai su zama aiyukan dabbobi.
Da wannan za ka san girman zalunci da ake yi wa Ahlus Sunna Mabiya Salaf ake cewa; -wai- ba sa nazari da aiki da hankali, kawai makauniyar biyayya suke yi, har ake cewa; -wai- suna inkarin Dalilai na hankali. Lallai wannan ba dadai ba ne, kuma zaluntar Ahlus Sunnan ne. Saboda Mabiya Salaf sun yarda da abin da Qur'ani ya zo da shi na umurni da nazari da lura da tadabburi a cikin Ayoyi masu yawa, kuma suna aiki da su. Su dai abin da ba su yarda da shi ba shi ne gabatar da hankalin a kan abin da Allah ya saukar, da ba shi 'yancin cin gashin kai, saboda in dai hankali lafiyayye ne to babu yadda za a yi ya wuce gaban abin da Mahallicinsa ya saukar. Saboda komai girman kunne ba zai wuce kai ba.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...