Gaskiyar magana fa ko, Sufanci babu yadda za a yi ya gyaru. Saboda ka taba ji an gyara kashi (Akramakumullah)?!
Ba a taba gyara wata bidi'a ko wata hanya ta bata ba. Gyaranta kawai shi ne a bar bidi'ar, a dena yinta, a bar bin hanyar.
Don haka masu harkar "Islahi" da kawo gyara a Sufanci, muna jin dadin inkari da suke yi wa 'Yan Hakika. Amma gaskiyar magana ita ce: Matukar za a yi Sufanci a Duniyar nan, to kuwa dole sai an yi Hakika. Saboda ba ka taba iya raba Sufanci da Hakika. Hasali ma Hakika ita ce kololuwar martaba a Sufanci.
Saboda haka, mafita daya ita ce: Dukkan Musulmai su yi watsi da hanyoyin bidi'a da bata da Dariqun Sufaye, su dawo kan tafarkin Sunnar Annabi (saw), tafarkin da ya shimfida ga al'ummarsa, ya rasu ya bar Sahabbansa a kai. A bi wannan tafarkin ba ragi ba kari.
Daga karshe ina fadakar da hukuma cewa; lallai rashin neman mafita ga irin wannan ta'addanci ga Addini, na zagin Allah da zagin Annabi (saw) da zagin Sahabbansa (ra) da wasu suke yi da sunan Addini zai janyo fitina a cikin al'umma, don ana samun matasa suna daukar doka a hanunsu, alhali ba haka ne ya dace ba.
Comments
Post a Comment