GWARGWADON HALAYENMU GWARGWADON SHUGABANNINMU
Al-Imam Ibnul Qayyim yana bayanin hikimar Allah a cikin halittarsa da gudanarwarsa sai ya ce:
وتأمل حكمته تعالى في أن جعل ملوك العباد وأمراءهم وولاتهم من جنس أعمالهم، بل كأن أعمالهم ظهرت في صور ولاتهم وملوكهم، فإن ستقاموا استقامت ملوكهم، وإن عدلوا عدلت عليهم، وإن جاروا جارت ملوكهم وولاتهم، وإن ظهر فيهم المكر والخديعة فولاتهم كذلك، وإن منعوا حقوق الله لديهم وبخلوا بها منعت ملوكهم وولاتهم ما لهم عندهم من الحق وبخلوا بها عليهم، وإن أخذوا ممن يستضعفونه ما لا يستحقونه في معاملتهم أخذت منهم الملوك ما لا يستحقونه، وضربت عليهم المكوس والوظائف، وكلما يستخرجونه من الضعيف يستخرجه الملوك منهم بالقوة، فعمالهم ظهرت في صور أعمالهم.
وليس في الحكمة الإلهية أن يولى على الأشرار الفجار إلا من يكون من جنسهم.
ولما كان الصدر الأول خيار القرون وأبرها كانت ولاتهم كذلك، فلما شابوا شابت لهم الولاة. فحكمة الله تأبى أن يولي علينا في مثل هذه الأزمان مثل معاوية وعمر بن عبد العزيز فضلا عن مثل أبي بكر وعمر، بل ولاتنا على قدرنا وولاة من قبلنا على قدرهم، وكل من الأمرين موجب الحكمة ومقتضاها
مفتاح دار السعادة ومنشور ولاية العلم والإرادة (1/ 253 - 254)
"Ka lura da hikimar Allah Madaukaki ta sanya Shugabannin talakawa da Sarakunansu da Gomnoninsu gwargwadon halayen talakawan. Kai, kamar ka ce: aiyukan talakawa suna bayyana ne a kamannin Shugabanni da Gomnonin nasu. Idan talakawan sun tsayu a kan Addini sai Shugabannin su tsayu a kan dadai. In talakawan sun zama masu adalci a tsakaninsu sai shugabannin su yi musu adalci a cikin mulkinsu, in talakawan sun zama masu zalunci a tsakaninsu sai Shugabanni da Gomnonin nasu su zama masu zalunci. In makirci da yaudara sun bayyana daga talakawan sai shugabannin ma su zama haka. In talakawan sun ki bayar da hakkokin Allah da yake kansu (kamar Zakka da Sadaka) suka yi rowansu sai Shugabanni da Gomnonin nasu su hana su nasu hakkokin, kuma za su yi rowansu gare su. In talakawan suka yi kwacen abin da ba su cancanta ba daga masu rauni a cikinsu a cikin mu'amalolinsu, sai shugabannin nasu su kwace musu abin da shugabannin ba su cancance shi ba, su dora musu haraji (tax) da aiyukan bautar kasa. Dukkan abin da talakawan za su karba daga masu rauni daga cikinsu haka shugabannin za su karba da karfi daga wajen talakawan. Gomnonin talakawan sun bayyana ne bisa kamannin aiyukan talakawan.
Ba ya daga cikin hikimar Allah ya dora shugabanni ga mutanen banza fajirai face irinsu.
Yayin da farkon Muslunci suka kasance mafiya alherin al'umma mafi biyayya ga Allah sai shugabanninsu suka kasance irinsu. Amma yayin da suka jirkice sai shugabannin suka jirkice tare da su. Saboda haka hikimar Allah ta ki yarda shugabanni irin su Mu'awiya (ra) da Umar bn Abdil'Azeez (r) su zama shugabanninmu a wannan zamani, balle kuma irinsu Abubakar (ra) da Umar (ra)!
Kai, shugabanninmu za su kasance ne gwargwadon yadda muke. Haka shugabannin magabatanmu sun kasance ne gwargwadon yadda magabatan suke, duka wadannan nau'uka biyu shi ne abin da hikimar Allah take hukuntawa".
Da ma Allah ya ce:
{إِنَّ اللَّهَ لَا يُغَيِّرُ مَا بِقَوْمٍ حَتَّى يُغَيِّرُوا مَا بِأَنْفُسِهِمْ } [الرعد: 11]
"Allah ba ya canza abin da ya samu mutane (na bala'i) har sai sun gyara abin da ke tare da su (na laifuka)".
In muna so shugabanninmu su zama masu adalci to mu ma mu zama masu adalci a tsakaninmu!
In muna so shugabanninmu su zama masu gaskiya da rikon amana to mu ma mu zama haka a cikin mu'amalolinmu na yau da kullum!
In muna so shugabanninmu su zama masu tausayin talakawa to mu ma mu zama masu tausayin raunananmu!
In muna so shugabanninmu su zama masu kyautata talakawa to mu ma mu kyautata wa junanmu!
Sai mun gyara kafin Allah ya canza mana.
Comments
Post a Comment