Hakikanin Salafiyya shi ne bin Mazhabar Salaf, na bin Qur'ani da Hadisi da abin da suka yi Ijma'i a kansa na lamuran Addini, musamman a babukan Aqida; na Tauhidi da Imani da Allah da tabbatar da Siffofinsa, da Babin Qaddara da sauran Rukunnan Imani, da kuma Babin Mas'alolin Imani; na sunayen Addini; Mumini da Kafiri da Mai aikata Kaba'ira da hukunce - hukuncensu, da Babin Matsayin Sahabbai da Da'a ma Shugabanni.
Duk wanda yake bin Qur'ani da Sunna da Ijma'in Salaf a wadannan babuka da sauran babukan Addini, kuma ya saba wa tafarkin 'Yan Bidi'a; Rafidha 'Yan Shi'a, Khawarijawa, Sufaye da Mabiya "Ilimul Kalam" (Jahamiyya, Mu'utazila, Asha'ira da Maturidiyya) da sauransu, to shi Dan Salafiyya ta hakika ne ko da bai kira kansa Dan Salafiyya ba. Don haka dukkan Mabiya Aqidar Salaf Ahlus Sunnati wal Jama'a 'Yan Salafiyya ne.
Saboda haka, duk wanda yake rarrabe tsakanin Ahlus Sunna da sunan Salafiyya, yana ware tsakaninsu; wadannan 'Yan Salafiyya ne, wadancan ba 'Yan Salafiyya ba ne, to ko shakka babu raba kai yake yi da kira zuwa ga "Tahazzub" da Kungiyanci abin zargi, da kira zuwa ga Kungiyarsa da ya rada mata suna "Salafiyya".
Saboda haka, akwai Salafiyya ta hakika, akwai kuma Salafiyya ta Kungiya.
Comments
Post a Comment