Skip to main content

MANUFAR SHAR'ANTA IBADOJI A CIKIN JAM'I.

 MANUFAR SHAR'ANTA IBADOJI A CIKIN JAM'I.

AL- SHAIKH ABDURRAHMAN BN NASIR AL- SI'IDIY YA CE:
"YANA DAGA CIKIN UMURNIN ALLAH MAFI GIRMA, DA SHARI'O'I SAUKAKKU DAGA SAMA, DA WASIYOYIN ANNABI (SAW); MUTANE SU HADU A KAN RIKO DA IGIYAR ALLAH CIKIN HADIN KAI, DA HADUWAR KALMAR MUSULMAI WAJE DAYA, DA HADIN KANSU DA DUNK'ULEWARSU WAJE GUDA".
YA CE:
"YANA DAGA CIKIN NASIHA MAFI GIRMA WA MUSULMAI YIN KOKARI WAJEN HADA ZUKATANSU, DA HADA KANSU DA KUMA HANASU RARRABUWA".
YA CE:
"ALLAH DA MANZONSA SUN YI UMURNI DA HADUWAR MUSULMI CIKIN JAM'I A IBADOJI MASU YAWA, KAMAR A AIKIN HAJJI DA SALLAR IDI DA SALLAR JUMA'A DA SALLAR JAM'I (SALLOLIN FARILLA 5), SABODA A CIKIN HADUWAR TASU ZA A SAMU SOYAYYA A TSAKANINSU DA SADA ZUMUNCI DA RASHIN KAURACE MA JUNA. KUMA ALLAH DA MANZONSA SUN YI HANI A KAN GIBA (CIN NAMA) DA ANNAMIMANCI DA GULMA DA KAURACE MA JUNA DA HA'INCI DA HASADA DA RIK'O DA MAKAMANTANSU, DUKA SABODA HAKAN ZAI KAWO BARNA A CIKIN BAYI DA KUMA RABUWAR KAI A TSAKANINSU. KUMA YA YI UMURNI DA GYARA TSAKANIN MUTANE MASU GABA DA JUNA TA KOWACE HANYA, HAR YA HALATTA YIN KARYA DON GYARA TSAKANIN MUTANE, SABODA ALHERIN DA KE CIKINSA".
¤ ALLAH YA SHAR'ANTA MANA YIN IBADOJI CIKIN JAM'I, YA HANA MU WASU MUNANAN HALAYE A TSAKANINMU DUKA DON MU HADA KAI DA JUNA KADA MU RARRABA.
¤ ALLAH YA WAJABTA MANA TAUHIDI (BAUTAR ALLAH ABIN BAUTA GUDA 'DAYA), YA AIKO MANA DA MANZO GUDA 'DAYA, YA SAUKAR MASA DA LITTAFI GUDA 'DAYA, DUKA DON MU HADA KAI MU ZAMA AL'UMMA GUDA 'DAYA MASU RIKO DA IGIYAR ALLAH CIKIN HA'DIN KAI, KUMA DON MU NISANCI RARRABUWA.

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...