MENENE HAKIKANIN MUSLUNCI, KUMA WANENE MUSULMI NA HAKIKA?
Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) ya ce:
الإسلام هو أن يستسلم لله، لا لغيره؛ فيعبد الله ولا يشرك به شيئا، ويتوكل عليه وحده، ويرجوه، ويخافه وحده، ويحب الله المحبة التامة، لا يحب مخلوقا كحبه لله، بل يحب لله، ويبغض لله، ويوالي لله، ويعادي لله. فمن استكبر عن عبادة الله لم يكن مسلما، ومن عبد مع الله غيره لم يكن مسلما. وإنما تكون عبادته بطاعته؛ وهو طاعة رسله؛ فمن يطع الرسول فقد أطاع الله
النبوات لابن تيمية (1/ 417)
"Muslunci shi ne mutum ya mika wuya ga Allah ba ma waninsa ba, sai ya bauta ma Allah kar ya yi masa shirka ya hada shi da komai, ya dogara ga Allah shi kadai, ya yi fatan alheri a wajensa, ya ji tsoronsa shi kadai, kuma ya so Allah cikakkiyar soyayya, kar ya so wani halitta kamar sonsa ga Allah, a'a, ya so halittan don Allah, ya ki shi don Allah, ya jibince shi don Allah, ya yi gaba da shi saboda Allah.
Duk wanda ya yi girman kai ga bautar Allah to bai zama musulmi ba, haka duk wanda ya bauta ma wanin Allah tare da Allah to bai zama musulmi ba. Kuma bautar Allah tana kasancewa ne kawai ta hanyar yi masa da'a, kuma shi ne da'a wa Manzanninsa, duk wanda ya yi da'a wa Manzon Allah to hakika ya yi da'a ma Allah ne".
Abin lura:
1- Muslunci shi ne mika wuya ga Allah ta hanyar bauta masa shi kadai, da yi masa da'a a umurninsa na farillai da wajibai da nisanta haninsa, a bisa cikakkiyar soyayya gare shi da jin tsoronsa da fatan alheri a wajensa tare da tawakkali gare shi, da nisantar shirka.
2- Ana soyayya da kiyayya da jibinta da adawa ma wani mutum ne duka saboda Allah ba don wani abu ba, ga wanda ya cancanci hakan.
3- Duk wanda ya yi girman kai ya ki bauta ma Allah, ya ki yi masa da'a shi ba Musulmi ba ne, kamar wanda ba ya aikata farillai, kamar wanda ba ya yin Sallah amma kuma yana kiran kansa musulmi.
4- Duk wanda yake Shirka ma Allah ba musulmi ba ne, komai yawan Sallarsa da Azumi da Aikin Hajji, kamar wadanda suke bauta ma kabarbura da rokonsu biyan bukata da neman taimako a wajensu.
5- Muslunci shi ne kawai Addini a wajen Allah, Addinin da Manzanni suka zo da shi daga wajen Allah, wanda ya yi da'a wa Manzon Allah to ya yi da'a ma Allah ne.
Ya Allah muna rokonka ka dauki rayukanmu da imani muna musulmai na hakika.
Masha Allah
ReplyDelete