Skip to main content

Nassin Shari'a ba ya cin karo da zamani

 Nassin Shari'a ba ya cin karo da zamani, saboda Shari'ar Muslunci ta zo ne da samar da amfani da kawar da cuta, duk wani abun da akwai Maslaha da amfani a cikinsa to Shari'a ta zo da shi, kuma tana umurni da shi. Haka duk wani abu da a cikinsa akwai barna da cutarwa to Shari'a tana hani a kansa.

Don haka duk lokacin da wani ya yi zaton cewa; Nassin Shari'a ya yi hani a kan wani abu da yake akwai Maslaha da amfani na rayuwar Duniya a cikinsa ko ta yi umurni da abin da akwai barna ko cutarwa a cikinsa to lallai bai fahimci Nassin ba ne, saboda ka'ida ce: Nassin Shari'a ba ya cin karo da Maslaha ko abu mai amfani da aka same shi daga baya cikin wannan zamani, bayan saukan Nassin na Shari'a.
Don haka ababen da aka samar a wannan zamani masu amfani da wadanda akwai Maslaha mai rinjaye a cikinsu ba sa cin karo da Nassin Shari'a, kuma Shari'a ba ta hani a kansu. Hasali ma umurni take yi da samar da su. Saboda abin da Shari'a ta zo samarwa kenan, wato Maslaha da amfanin bayi a cikin rayuwarsu ta Duniya da ta Lahira.
Allah ya ce ga Annabi (saw):
{وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِلْعَالَمِينَ } [الأنبياء: 107]
"Ba mu aiko ka ba face rahama ga talikai".
Izzuddeen bn Abdissalam ya ce:
اعلم أن الله شرع لعباده السعي في تحصيل مصالح عاجلة وآجلة...
وكذلك شرع لهم السعي في درء مفاسد في الدارين أو في أحدهما...
وكل ذلك رحمة بعباده ونظر لهم ورفق
قواعد الأحكام في مصالح الأنام (2/ 161 - 162)
"Ka sani cewa; lallai Alla ya shar'anta ma bayinsa kokarin samar da Maslaha ta kusa ko ta nesa...
Haka kuma ya shar'anta musu kokarin kawar da barna a Duniya da Lahira ko a daya daga cikinsu...
Duka wannan saboda rahamarsa ne ga bayinsa da dube gare su da rangwamensa gare su".
Saboda haka Nassin Shari'a ba ya cin karo da abubuwa masu amfani na zamani.
No photo description available.
All reactions:
5

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...