Nukhba ta Ibn Hajr
Gabatarwa: Abu Isma'il
Markazul Wa'ayil Islamiy Tudun Jukun Zaria
9/8/1441- 2/5/2020
*NUKHBATUL FIKR FI MUSƊAHI AHLIL ATHAR 09*
A yau mun san musɗalat kamar haka :
1. *Almarfu'u (المرفوع)*: Shi ne duk abin da aka danganta zuwa ga Annabi SAW na magana ko aiki ko tabbatar wa.
2. *Almauƙuuf(الموقوف)*:Shi ne duk abin da aka danganta zuwa ga Sahabi na magana ko aikinsa.
3. *Almaƙduu'u (المقطوع)*: Shi ne duk abin da aka danganta zuwa ga Tabi'i na magana ko aiki.
ANA KIRIN MAUƘUF DA MAƘDU' ATHAR
4. *Almusnad(المسند)*: Shi ne hadisin da ya dangane ga Annabi SAW ba tare da yankewar isnadi ba.
5. *Al'aaliy- Al'luwwul Muɗlaƙ (العالي:العلو المطلق)* : Shi ne hadisi ya zo da mutane yan kaɗan in an gwada shi da wani wanda bashi ba.
6. *Al-aaliy Al'luwwul Nisbiy(العالي: العلو النسبي)*: Shi ne hadisin da ya zo da mutane kaɗan, zuwa ga ɗaya daga cikin manya malaman hadisi kamar shu'ubah.
ULUWWUN NISBIY YA KASU GIDA GIDA
7. *Almuwafaƙah(الموافقة)*: Shi ne Isnadin mutum Y kai ga malamin ɗaya daga cikin malaman da suka rubuta littafin hadisi, kamar Bukhari ko Muslim d.s
8. *Albadalu(البدل)*: Shi ne kaiwa ga malamin malamin ɗaya daga cikin marubutan.
9. *Almusawah(المساواة)*: Shi ne daidaiton adadin isnadi dana ɗaya daga cikin marubuta. Misali Tsanin Bukhari zuwa Annabi mutum 6 ne sai Shima wani ya samo isnadi mai mutane 6 a hadisi iri ɗaya.
10. *Almusafahah(المصافحة)*: Shi ne zuwa adadin Isnadi daidai da dalibin ɗaya daga cikin marubutan.
11. *Annazil(النازل)*: Shi ne kishiya Aaliy, wato hadisin daya zo da mutane da yawa a isnadinsa in an gwada shi da wani wanda matanin su ɗaya ne.
Nb. Ba a samun Aaliy da Naazil sai in suna da matani irin ɗaya sai ɗaya yafi mutane da yawa. Mai kaɗan shi ne Aaliy, mai yawa shi ne Naazil.
12. *Riwayatul Aƙran(رواية الأقران)* : Shi ne ɗalibi yayi karatu wajen ɗanuwansa ɗalibi.
13. *Almudabbaj(المدبج)*: Shi ne ɗalibai guda biyu kowa yayi karatu wajen kowa.
Nukhbah Na Ibn Hajr
Gabatarwa: Abu Isma'il
Markazul Wa'ayil Islamiy
Tudun Jukun Zaria
Ramadan Daura
10/8/1441-3/5/2020
*NUKHBATUL FIKR FI MUSƊALAHI AHLIL ATHAR 10*
A yau mun san musɗalat kamar haka.
1. *Riwayatul Akaabir anil asagir( رواية الأكابر عن الأصاغر)* :Riwayar da manya suke samowa daga wanda basu kaisu ba a shekaru.
2. *Riwatul Abaa'i anil abna'i( رواية الآبآء عن الأبناء)*: Riwayar da iyaye daga 'ya' yansu.Wasu kuma daga iyaye har zuwa kakanni.
3. *Almuhmal (المهمل)*: Shi ne mutane biyu suyi riwaya daga mutum ɗaya kuma sunansu irin ɗaya. To in aka gano wanda yafi lizmtar malamin sai a rinjayar da Riwayar sa shi kuma ɗayan ya zama muhmal.
4. *Man haddasa wa nasiya(من حدث و نسي)*: Wanda ya bada hadisi ya manta ya bayar. In ya tabbatar bai bayarba sai a mayar da riwayar. In kuma yayi kokonto sai a karɓa.
5. *Musalsali (المسلسل)* : Hadisin da yazo da wata siffa iri ɗaya wacce taita maimaitawa a isnadinsa.
Sai sigogin yadda ake karɓar riwaya.
Wanda yaji shi kadai daga malamin sa zai ce سمعت أو حدثني. Wannan itace sigar da tafi fitowa fili. Kuma tafi ɗaukaka.
Wanda yaji shida wasu ɗaliban zai ce. حدثنا
Wanda ya karanta ma malamin da kansa zai ce أخبرني أو قرأت عليه
In kuma bashi ya karanta ba, wani ya karanta shi kuma yana ji sai yace:
قرأ عليه و إنا أسمع
Sai kuma akwai: انبإني shi kuma ma'anarsu ɗaya da أخبرني sai dai malaman zamani suna banbanta wa da cewa Anba'aniy ga hadisi kawai Akhbarani ga duk labari ko na Annabi Koba na Annabi ba.
Sauran sun haɗa da: ناولني ga wanda aka bashi littafin hadisi, sai شافهني ga wanda aka bashi baki da baki, sai كتب إلي ga wanda aka rubuto masa hadisai aka aiko masa dasu, sai kuma عن و قال ga wanda bai haɗu da wanda yake bada hadisin sa ba ko bai karɓa daga gareshi ba kai tsaye.
Nukhbatul Fikr Na Ibn Hajr
Gabatarwa: Abu Isma'il
Markazul Wa'ayil Islamiy Tudun Jukun Zaria
Ramadan Daura
11/8/1441- 4/5/2020
Comments
Post a Comment