Nukbatul Fikr na Ibn Hajr
Gabatarwa: Abu Isma'il
Markazul Wa'ayil Islamiy Tudun Jukun Zaria
6/9/1441- 29/8/2020
*NUKHBATUL FIKR FI MUSƊALAHI AHLIL ATHAR 06*
A yau zamu san musɗalahat kamar haka:
Ana gane Munƙadi'i idan aka gano masu ruwa basu haɗu ba akwai tazara tsakanin su. Shi yasa ake buƙatar sanin tarihi
1. *Mudallasi المدلس*: Shi ne hadisin da mai ruwaya ya tsallake malamin shi ya ambaci malamin malamin shi da lafazi mai ruɗarwa kamar: da
2. *Al-mursalul khafiyyi(المرسل الخفي)*: Shi ne mai ruwaya ya danganta hadisin sa ga wani malami da zamanin su ɗaya amma basu haɗu ba.
Sannan game da suka ga me ruwaya takan kasance saboda: Ƙarya, Tuhumarsa da Ƙarya, mummunan kuskure, fasiƙanci, ruɗu, saɓama wanda suka fishi, rashin sanin waye shi, bidi'arsa,
3. *Maudu'i (الموضوع)*: Shi ne hadisin da aka yi Ƙarya aka danganta zuwa ga Annabi S. A. W
4. *Matruuki(المتروك)*: Hadisin wanda ake Tuhumarsa da ƙarya
5. *Munkari a wajen wasu malaman(المنكر على رأي)*: Hadisin mai mummunan kuskure, ko lalatacciyarhadda ko kuma fasiƙi.
6. *Al-Mu'allal(المعلل)*: Hadisin wanda ke da ruɗu, in akayi bibiya ta wasu dalili da tattaro irin hadisan.
Akwai qarin bayani a audio ku saurara.
Nukhbatul Fikr Na Ibn Hajr
Gabatarwa: Abu Isma'il
Markazul Wa'ayil Islamiy Tudun Jukun Zaria
Ramadan Daura
7/8/1441- 30/04 /2020
*NUKHBATUL FIKR FI MUSƊAHI AHLIL ATHAR 07*
A yau mun san musɗalaht kamar haka:
1. Mudrajul Isnaad(مدرج الإسناد): Shi ne hadisin da aka canza isnadinsa
2. Mudrajul Matn(مدرج المتن): Canza hadisin da aka danganta zuwa Sahabi zuwa ga wanda aka danganta zuwa ga Annabi
3. Al-maqlub(المقلوب): Shi ne hadisin da aka canza hadisi da kai gaba baya.
4. Al-mazid fi muttasilil asaneed(المزيد في متصل الأسانيد): Shi ne qara mutum a ruwaya. Kamar daga mutane biyar ya koma shida.
5. Almudɗarib(المضطرب): Shi ne canza isanadin wani hadisi da wani na daban.
Akan yi hakan da gangan.
6. Almusahhaf da Almuharraf(المصحف و المحرف): Shi ne canza harafi ko digo ko wasali a hadisi.
7. Riwayatul Hadisi bil ma'ana(رواية الحديثباد بالمعنى):Baya halasta da gangan a canza lafazin hadisi saɓani yadda yazo sai ga Malami masani da cikakkiyar ma'anar hadisin
8. Idan hadisi yazo da kalmar da ma'anarta bata fito fili ba, sai ayi sharhin kalmar da bayanin abu da ke da ruɗarwaشرح الغريب و بيان المشكل.
9. Jahala(الجهالة): Ya zamanto an faɗi wani wanda ba'a sanshi ba a isnadi. Sababinta yakan kasance saboda sunayensa suna da yawa, sai a ambace shi da sunan da bai shahara dashi ba saboda wata manufa. An rubuta littafai akan haka, Almuwaddih(الموضح). Ko kuma bashi da ruwaya da yawa, shi kuma an rubuta Alwuhdan(الوحدان). Ko kuma a faɗi sunansa a taƙaice, akanshi an rubuta Almubhamat(المبهمات). Ba a karban hadisin da aka ɓoye mai riwaya koda an kira shi da lafazin shi na kirki ne.
Nukhbatul Fikr Na Ibn Hajr
Gabatarwa : Abu Isma'il
Markazul Wa'ayil Islamiy Tudun Jukun Zaria
8/8/1441-1/05/2020
*NUKHBATUL FIKR FI MUSƊAHI AHLIL ATHAR 08*
A yau mun san musɗalat kamar haka:
1. *Majhulul Ayn(مجهول العين)*: Shi ne wanda mai riwaya guda ɗaya kawai ya ruwaito shi.
2. *Majhulul haal(مجهول الحال)*: Shi ne wanda mutane biyu ko fiye da haka suka yi riwaya a wajensa. Amma ba a ce amintacce ne a karɓi riwayarsa ba kuma shi ake cema Almastuur.
3. *Mai bidi'ah mufassiqa(المبتدع بدعة مفسقة)*: Shi ne mai riwaya ɗan bidi'ah amma bidi'ar da ke maida mutum mai saɓo. Malamai sunce ana iya karɓar hadisin sa matuƙar bai ruwaito abinda ke ƙarfafa bidi'arsa.
4. *Mai bidi'ah mukaffira(المبتدع بدعة مكفرو):* Shi ne mai riwaya ɗan bidi'a wacce ke maida mai ita kafiri. Kamar bidi'ar cewa ƙur'ani halitta ne. Jumhurun malamai sun tafi akan cewa ba a karɓan riwayarsa haka Juzajaaniy malamin Nasa'i ya faɗa.
5. *Shaaz(الشاذ):* Riwayar mai mummunar hadda, a wajen wasu malamai.
6. *Mukhtaliɗ(المختلط):* Wanda lalacewar haddarsa bijiro wa tayi kamar saboda tsufa ko wata lalura.
7. *Hasanun lagairi(حسن لغيره):* Shi ne lokacin da aka samo ma mai hadda mai rauni riwayar mara rauni ta ƙarfafeshi , ko riwayar mastuuri, ko mursali ko mudallisi.
*Sannan isnadi yakan tuƙe ga Annabi S.A.W kai tsaye ko kuma a hukunce. Daga maganarsa ko aikinsa ko tabbatarwarsa.*
Kai tsaye Shine danganta zuwa ga Annabi
Hukunce: Shi ne Sahabi ya faɗi magana yace haka ake yi a zamanin Annabi S.A.W
Ko a danganta magana zuwa ga Sahabi.
8. *Sahabi(الصحابي):* Shi ne wanda yayi zamani da Annabi S.A.W kuma yayi imani dashi sannan ya mutu a musulunci koda ya taɓayin ridda bayan musuluncinsa.
Ko aka danganta zuwa ga Tabi'i
9. *Tabi'i التبع*: Shi ne wanda yayi zamani da Sahabi yana mai Imani da Annabi S.A.W kuma ya mutu a cikin musulunci.
Comments
Post a Comment