TA'ASSUBANCI SHI NE HAKIKANIN HIZBIYYANCI (KUNGIYANCI ABIN ZARGI)
Sau da yawa za ka samu mutane sun ware kansu, suna bin wani malami ko wasu malamai 'yan tsiraru, suna kulla soyayya da kiyayya a kansu, amma ba sa yarda a kirasu da sunan kungiya, ma'ana a kullum suna inkari ga wanda ya siffantasu da kungiyanci, alhali a bisa hakika kungiyanci abin zargi suke yi matukar akwai TA'ASSUBANCI A TARE DA SU.
Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) ya ce:
دين المسلمين مبني على اتباع كتاب الله وسنة رسوله وما اتفقت عليه الأمة فهذه الثلاثة هي أصول معصومة، وما تنازعت فيه الأمة ردوه إلى الله والرسول، وليس لأحد أن ينصب للأمة شخصا يدعو إلى طريقته، ويوالي عليها ويعادي غير النبي صلى الله عليه وسلم
ولا ينصب لهم كلاما يوالي عليه ويعادي غير كلام الله ورسوله وما اجتمعت عليه الأمة، بل هذا من فعل أهل البدع الذين ينصبون لهم شخصا أو كلاما يفرقون به بين الأمة، يوالون على ذلك الكلام أو تلك النسبة ويعادون.
درء تعارض العقل والنقل (1/ 272 – 273)، مجموع الفتاوى (20/ 164)
"Addinin Musulmai ya ginu ne a kan Bin Littafin Allah da Sunnar Manzonsa (saw) da abin da Al'umma suka yi Ittifaqi a kansa (Ijma'i). Wadannan abubuwa guda uku (3) su ne tushen Addini wadanda suke kararru (an karesu daga kuskure). Abin da al'umma suka yi sabani a kansa to su mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa.
Babu wani da ya isa ya TSAYAR WA AL'UMMA WANI MUTUM DA YAKE KIRA ZUWA GA TAFARKINSA, YA KULLA SOYAYYA DA KIYAYYA A KANSA, WANDA BA ANNABI (SAW) BA.
Kuma babu wani mutum da ya isa ya TSAYAR WA MUTANE WATA MAGANA (RA'AYI) YANA SOYAYYA A KANTA, YANA KIYAYYA A KANTA WACCE BA MAGANAR ALLAH DA MANZONSA (SAW) DA ABIN DA AL'UMMA SUKA YI IJMA'I A KANSA BA. KAI, WANNAN YANA DAGA CIKIN AIKIN 'YAN BIDI'A, WADANDA SUKE TSAYAR WA MUTANE WANI MUTUM KO WATA MAGANA (RA'AYI) DA SUKE RABA KAN AL'UMMA DA ITA, WANDA SUKE SOYAYYA A KAN WACCAR MAGANAR (RA'AYI) KO WANCAN SUNAN (WANI SUNA DA SUKE DANGANTUWA GARE SHI) KUMA SUKE GABA A KANSU".
Ibnul Qayyim (r) ya ce:
التعصب للمذاهب، والطرائق، والمشايخ، وتفضيل بعضها على بعض بالهوى والعصبية، وكونه منتسبا إليه، فيدعو إلى ذلك ويوالي عليه، ويعادي عليه، ويزن الناس به، كل هذا من دعوى الجاهلية.
زاد المعاد في هدي خير العباد (2/ 431)
"Ta'assubanci (biyayya ido a rufe) wa Mazhabobi, ko wa Darikoki, ko wa Shehunnai, da fifita sashe a kan sashe a bisa son rai da Ta'assubanci (kungiyanci abin zargi), ko don kasancewarsa yana dangantuwa zuwa gare shi, sai yana kira zuwa ga haka, yana soyayya a kansa, yana kiyayya a kansa, kuma yana auna mutane da shi (yana yi musu hukunci), duka wannan yana cikin kiraye - kirayen Jahiliyya".
Abin lura:
1- Kungiyanci abin zargi (Hizbiyyanci) shi ne Ta'assubanci ma wani Malami ko wata Kungiya.
2- Ta'assubanci shi ne ka ware wani mutum, ko wata jama'a, ko wata kungiya kana binsa ido a rufe, kana son wanda yake sonsa, kana kin wanda ya saba masa alhali babu wani dalili na Shari'a da zai sa ka ki shi.
3- Ta'assubanci ne ka raba al'umma gida biyu, wadanda suke son malaminka ko ra'ayinka suna hanun dama kana sonsu, wadanda suka saba masa kuma suna hanun hagu kana kiyayya da su.
4- Babu wanda ya isa ya dora wa mutane bin ra'ayin wani mutum guda daya, ta yadda wanda ya bi shi shi ne abin so, wanda ya saba masa kuma ya zama abokin adawa da kiyayya.
5- Qur'ani da Sunna da Ijma'in magabata kawai su ne abin bi, haka babu wani mutum da ya wajaba a bi shi sai Manzon Allah (saw), kamar yadda babu wata jama'a da ya wajaba a bisu sai magabata na kwarai (Sahabbai da Tabi'ai).
6- Alama ce ta 'yan bidi'a tsayar wa mutane wani mutum ko wani ra'ayi da wajabta wa mutane binsa, kuma kira zuwa ga hakan, da yin ta'assubanci a kan haka yana daga cikin kiraye – kirayen Jahiliyya.
7- Ana soyayya da biyayya ne ga dukkan malaman Sunna a jumlacensu, wanda ya yi kuskure a cikinsu sai a ajiye masa kuskurensa, ayi masa gyara ta hanyar da ta dace.
8- Abin da yake faruwa a yau, na kasuwar dalibai Ahlus Sunna gida biyu, sashe yana nuna soyayya da biyayya ga wani malami, kuma yana nuna adawa ga wadanda suka saba masa, wani sashen kuma yana nuna adawa da kiyayya ma wancan sashen duka wannan yana daga cikin Kungiyanci da Hizbiyyanci da rarrabuwan kai da Allah da Manzonsa suka zargi masu aikata shi, kuma yana daga cikin al'adun Jahiliyya.
9- Wajibi ne Ahlus Sunna su hada kai, sabani da yake tsakaninsu su mayar da shi ga Qur'ani da Sunna, da nufin nasiha da gyara kuskure ta hanyar bincike na ilimi, da hanyoyi da suka dace, ba tare da gaba da kiyayya ko kaurace ma juna da rarrabuwa ba.
Comments
Post a Comment