Skip to main content

TAMINAL LUSIDITI "THE SURGE"

 


TAMINAL LUSIDITI "THE SURGE"

----------------------------------------------------------------
Wannan wani yanayi ne me kamar almara dakan faru dab da mutuwa. da akanga mara lafiyar dake fama da matsananciyar jinya doguwa ko gajeruwa.... wacce dalilin ciwon ƙila ko tashi baya iya yi, ko kuwa baya iya cin abinci, ko mutum ya kasance sai ana juyasa tare da ɗaga ana canza masa kwanciya.... Ko kuwa ma baisan waye kansa ba sam, magana ma in yana yi ba'a gane abinda yake cewa saboda zafin ciwo.
To amma kwatsam sai aga canji daga yanayin wannan mara lafiya, aga sauƙi ya samu na ban mamaki, akan iya ganin ya tashi da kansa ya zauna ko ya taka batare an taru andagasa ba, ko aga yaci abinci da kansa sosai, ko ya tattaka da kafafunsa, kuma yana iya gane kowa, ana magana yana dariya ma. Kaga ƴan uwa nata murna sauƙi ya samu, ariqa wanne ai yau har abinci yaci da kansa.
-----------------------------------------------------------------
Allah sarki! amma bayan wasu awoyi, yini guda, kwana uku ko sati ɗaya zuwa huɗu kwatsam saide aji anfasa kukan wane ya rasu. A riqa mamaki bayan ga alamun sauƙi anganki saɓanin da ƙila kowa na kawo mutuwa zai to amma ganin yadda wannan sauƙin ya samu yasa yanzu mutuwarsa ta zama abin mamaki. Shine ma zaka ji Hausawa na cewa ashe wane sauƙin bana tashi bane, Allah sarki.
Ya ku ɗaliban ilimi.... wannan yanayin na ganin alamun sauki ga majinyacin da ada ba'a tunanin zai tashi haka... Amma kuma kwatsam aga ya kwanta ya mutu shi muke kira terminal lucidity ko end of life rallying ko the surge. Duk mara lafiyar da akaga irin wannan saukin ba zato ba tsammani alama ce ta mutuwarsa ta kusanto
Ga manyan likitoci munsan hakan alamun mutuwa ne, shiyasa bama ruɗuwa koda iyalan mara lafiya sun fara zancen neman sallama daga asibiti, haka koda agida mara lafiya yake abin ke kasancewa. Don haka a duk sanda kuka ga irin wannan saukin inda hali kui masa ku nemi wasicci, ku tambaye sa abinda zaku so sani, yana dab da gargara.
______________________________________
Hakazalik akwai yanayin da akanga Mara lafiya na nuni da hannu, ko aga yana ɗaga hannu sama daga kwance kamar me kokarin kamo wani abin ko karɓa ko ɗaukar wani abu. Wanda shine a masu jinya zaka ga mutum na tasowa yana tambayar me kake so? Amma sai aga mara lafiyar ya kau da kai. A riqa wani abin yake son faɗa amma ya kasa... Wannan shi muke kira "REACH OUT" da wuya mutum ya qara awa 72 a raye. Don haka wannan na daga alamun mutuwa shima. Sai ai kokarin fara bawa mutum kalmar shahada.
Shyasa wasu lokutan wani kan ga ya biya likitoci kudin aiki amma suna jan ƙafa wajen yin aikin, karshe ace mutum ya mutu basui aikin ba. Wani abin ba fitowa za ai ace muku ga abinda aka gani ba, sai ya zama rigima.
______________________________________
Allah ka jikan mu, kai mana kyakkyawan ƙarshe. A hankali zan cigaba da nusar damu alamomin gane tunkarowar mutuwa musamman don masu jinyar marasa lfy daga ilimiin da Allah ya bamu.
✍🏻
[Ibrahim Yaqub Yusuf] 🌻

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...