Skip to main content

WAJIBI NE MU NISANCI DUK ABIN DA ZAI JANYO KIYAYYA A TSAKANIN AHLUS SUNNA

 WAJIBI NE MU NISANCI DUK ABIN DA ZAI JANYO KIYAYYA A TSAKANIN AHLUS SUNNA

Imamu Muslim ya ruwaito:
عن أنس، أن النبي صلى الله عليه وسلم، قال: «لا تحاسدوا، ولا تباغضوا، ولا تقاطعوا، وكونوا عباد الله إخوانا»
صحيح مسلم (4/ 1983)
Daga Anas (ra) ya ce Annabi (saw) ya ce:
"Kar ku yi Hasada a tsakaninku, kar ku yi Kiyayya a tsakaninku, kar ku yanke alaka da juna, ku zama bayin Allah 'yan uwan juna".
Shaikhul Islam ya ce:
وقرن في الحديث الأول الحسد بالبغضاء؛ لأن الحاسد يكره أولا فضل الله على ذلك الغير؛ ثم ينتقل إلى بغضه؛ فإن بغض اللازم يقتضي بغض الملزوم فإن نعمة الله إذا كانت لازمة وهو يحب زوالها وهي لا تزول إلا بزواله أبغضه وأحب عدمه والحسد يوجب البغي كما أخبر الله تعالى عمن قبلنا: أنهم اختلفوا من بعد ما جاءهم العلم بغيا بينهم فلم يكن اختلافهم لعدم العلم بل علموا الحق ولكن بغى بعضهم على بعض كما يبغي الحاسد على المحسود.
مجموع الفتاوى (10/ 127)
"Annabi (saw) ya hada tsakanin Hasada da Kiyayya a cikin Hadisin farko, saboda farko mai hasada yana kin falalar da Allah ya yi ma waninsa ne, sai kuma ya tashi daga hasada zuwa kiyayyar mutumin, saboda kin "lazimi" yana hukunta kin "malzumi", saboda idan ni'imar Allah ta kasance ta lazimci wani mutum, sai shi kuma yake so ta gushe, alhali ba za ta gushe ba sai mutumin da kansa ya gushe to zai ki shi, kuma ya so a rasa mutumin.
Haka kuma Hasada tana haifar da zalunci kamar yadda Allah ya ba da labari game da wadanda suka gabace mu, cewa; sun yi sabani bayan ilimi ya zo musu saboda zalunci a tsakaninsu, don haka sabaninsu bai kasance saboda rashin ilimi ba, a'a, sun san gaskiya amma sai sashe ya zalunci sashe, kamar yadda mai hasada yake zaluntar wanda yake yi wa hasada".
ABIN LURA:
1- Wajibi ne a kan dukkan bangarori na Ahlus Sunna da daidaikunsu su cire hasada wa juna daga cikin zukatansu.
2- Hasada ce take janyo kiyayya da zalunci a magana ko aiki, daga nan kuma sai kaurace wa juna da rabuwar kai.
3- Sabani a kan kananan mas'alolin Addini irin mas'alolin Sadalu da Qabdhu, da makamantansu, ba ya kai wa ga kiyayya da zalunci a magana ko aiki da rabuwar kai.
BA ZA MU SAMU HADIN KAI A TSAKANINMU BA SAI MUN NISANCI HASADA DA DUKKAN ABIN DA ZAI JANYO KIYAYYA DA ZALUNCI A TSAKANINMU.

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...