Skip to main content

'YAN UWA, YAU QISSAR IMAMU ABU HANIFA (R) ZAN BA KU

 'YAN UWA, YAU QISSAR IMAMU ABU HANIFA (R) ZAN BA KU

Kowa ya san Imamu Abu Hanifa shi ne Limamin Fiqhu na farko a jerin Limaman Fiqhu guda hudu ma'abota Mazhabobin Fiqhu mafi shahara a Duniyar Muslunci.
Ya kasance a zamaninsa akwai wani babban Malamin Fiqhu kuma Alkali, wato Muhammad bn Abdirrahman Ibnu Abi Laila. Ya kasance Malamin Fiqhu ne amma Dan Makarantar ra'ayi ne ba Makarantar Hadisi ba.
Wannan malami rashin jituwa ta shiga tsakaninsa da Imamu Abu Hanifa, rashin jituwa irin wacce take shiga tsakanin Malamai, saboda sabanin Ijtihadi a wasu Mas'aloli na Addini.
To, Ibnu Abi Laila ya kasance a Masallaci yake zama yake yin alkalancinsa, wato a babban Masallacin Kufa. To an ruwaito cewa; wata rana bayan ya tashi daga alkalanci, har ya fita daga Masallacin sai ya ji wata mata tana ce ma wani mutum: "Ya dan Mazinata biyu (babansa da mamarsa)".
Wato ta nuna cewa; babansa mazinaci ne, mamarsa ma mazinaciya ce. To sai Alkali Ibnu Abi Laila ya sa aka kira ta. Sai ya koma Masallaci kan kujuran alkalancinsa ya zauna, sai ya yi mata Shari'a, ya yanke mata hukuncin kazafi saboda ba ta da shaidu hudu (4) a kan abin da ta fada. Sai ya sa aka yi mata haddin kazafi guda biyu, wato bulala dari da sittin (160), bulala tamanin a kan kazafi wa baban mutumin, bulala tamanin kuma a kan kazafi wa mamarsa.
To, sai labarin abin da ya faru ya riski Limamin Fiqhun Iraqi, wato Imamu Abu Hanifa, kawai sai Abu Hanifa ya ce: Wannan Alakilin ya tafka kurakurai guda shida (6) a cikin wannan hukunci:
1- Ya koma majalisin alkalanci bayan ya tashi, alhali bai kamata Alkali ya koma majalisin alkalanci bayan ya tashi ba.
2- Ya zartas da haddi a Masallaci, alhali Annabi (saw) ya yi hani a kan haka.
3- Ya yi bulala wa matar a tsaye, alhali su mata a zaune ake yi musu haddi, kuma cikin sutura da tufafi wadatacce.
4- Yi mata haddi har guda biyu, bulala 80 sau biyu, alhali idan mutum ya yi kazafi wa jama'a masu yawa cikin magana daya to haddi daya kawai za a yi masa.
5- Haka kuma ko da haddi biyun ne ya hau kanta to ba lokaci daya za a yi mata su ba, a'a, za a yi mata na farko, sai kuma a barta sai ta warke sai a zo a yi mata na biyun.
6- Ya tsayar da haddi a kan mai kazafin alhali masu hakkin kazafin ba su nemi hakan ba (wato ba su kawo kara ba).
Haba! ai da labari ya isa ga Alkali Ibnu Abi Laila kawai sai ya garzaya wajen Gwamnan Kufa ya ce masa: Akwai fa wani Matashi ana ce masa Abu Hanifa, yana kalu-balanta ta a cikin alkalancina, yana bayar da Fatawa sabanin hukuncin da na yanke, yana nuna cewa; ina yin kuskure a hukuncin nawa. Don haka ina so ka tsawatar masa don ya fita hanyata.
Sai kuwa Gwamna ya aika aka zo da Abu Hanifa, sai ya hana shi yin Fatawa gaba daya.
To sai ake ba da labarin cewa:
Wata rana Abu Hanifa yana gidansa tare da matarsa da dansa Hammadu da 'yarsa, sai 'yar tasa ta ce masa: Baba, ina Azumi, kuma jini ya fito daga tsakanin hakorana, amma na yi ta tofarwa har sai da yawuna ya dawo fari tas, gaba daya jinin ya dena fita. To shin Azumina zai karye idan na hadiyi yawun?
Sai Babanta Imamu Abu Hanifa ya ce mata:
سلي أخاك حمادا فإن الأمير منعني من الفتيا.
"Ki tambayi Dan uwanki Hammadu, saboda ni Gwamna ya hana ni yin Fatawa".
Duba cikin Littafin "Wafiyyaatul A'ayaan" na Ibnu Khallikan (4/ 180)
Allahu Akbar!
Lallai akwai darusa da ilmomi masu yawa a cikin wannar Qissah. Abin da ya ja hankalin Ibnu Khallikan daga cikinta shi ne:
Ka duba girman da'a ga Allah a umurninsa da ya yi na da'a ma Shugabanni, Abu Hanifa ya kasance hatta a sirrance a cikin gidansa tsakaninsa da iyalansa yana da'a ma shugabansa don kar ya saba umurnin Allah Madaukakin Sarkin.
Allah ya jikan Imamu Abu Hanifa ya yi masa gafara da rahama.
To jama'a, kun ga fa irin halin Faqaha'u Malaman Fiqhu magabata, suna da'a ma Shugabanninsu sau da kafa saboda da'a ma Allah Madaukaki.
A yau, da a ce: za a hana wani Malami yin Wa'azi ko bayar da Fatawa to da sai an tayar da zaune tsaye, alal akalli ko da a kafafen sadarwa ne.
No photo description available.
All reactions:
7

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...