A bisa hakika babu banbanci tsakanin 'Yan Hakika da Darikun Sufaye.
Duk wanda ya san hakikanin Darikun Sufaye ya san sun kunshi Aqidar "Wahdatul Wujudi" (Aqidar komai Allah ne), da kuma Aqidar "Wahdatush Shuhudi" (Aqidar rashin ganin komai sai Allah), da kuma banbanci tsakanin Hakika da Shari'a. Hakika ita ce ta Arifai, kebantattu, Shari'a kuma ta amawa gama garin mutane. Haka kuma a cikin Sufanci akwai Aqidar "Faira", Aqidar nan ta Falsafa da take nuna cewa; komai abu daya ne, komai yana kwarara a cikin komai.
Haka kuma in ka dawo cikin wuce gona da iri a hakkin Shehunnai da Waliyyansu, duk wanda ya leka littatafan Malaman Sufaye, ya ga labarun Waliyyai da Shehunnan nasu, kamar Littafin "Jawahirul Ma'aniy", da "Rimahu" da sauransu, zai ga inda suke tabbatar da cewa; Shehunnan nasu suna da dama ta juya Duniya da gudanar da ita, ta hanyar saukar da ruwan sama, da warkas da maras lafiya, kashewa da rayarwa, da cewa; su ne suke tsaron Duniya da kare ta. Da cewa; sun san gaibi, sun san abin da ke cikin sama da kasa, da abin da zai zo a gaba, da abin da ke cikin zukata. Da kuma cewa; su Ma'asumai ne, da cewa; suna da daman shar'anta wata ibada a Shari'a. Da cewa; in an gansu za a shiga Aljanna, da Aqidar fita daga Shari'a zuwa Hakika.
Kawai banbancin shi ne, da ma suna kasa Sufayen kashi uku:
1- Kebantattun kebantattu, masu fita daga Shari'a su shiga Hakika.
2- Kebantattu.
3- Amawa gama garin mutane, masu aiki da Shari'a.
Kawai kuskure aka samu aka fara yin Tarbiyyar Darika ga matasa da wawaye, in sun yi Tarbiyyar sun yi "Wusuli", sun ga komai ya zama Allah, sai su fito suna bayyana hakikanin abin da suka gani ga jama'a. Alhali a da, abin ya takaita ne a tsakanin Kebantattun kebantattu kawai.
Saboda haka, in ma za a banbance tsakaninsu sai dai a ce; akwai jahilai akwai kuma Shehunnai a cikinsu. Su jahilai jansu kawai ake yi suna bi ido a rufe, kuma ana boye musu hakikanin Darikar.
Shehunnan kuma sun kasu kashi biyu:
1- Masu ganin dole a bayyana hakikanin Darika.
2- Da kuma wadanda suke ganin bai kamata a bayyana ba, saboda ganin hakikanin Sufancin ya saba ma hankali.
Kuma a Nigeria ne kawai ake wannan rufa-rufan, ko nan kusa Kasar Ghana in ka je za ka ga yadda suke tasu Darikar, Darika ta Hakika suke yi.
Saboda haka, bai kamata a zo ana rena wa mutane hankali, ana wasa da kwakwalensu ba, kamar yadda ake yi wa mabiyan Darikun Sufaye, ana jansu kawai suna bi kamar yadda tumakai suke bin makiyayinsu.
Saboda haka ya kamata mutane su san cewa; duk wanda zai zo ya yi kokarin yin rufa-rufa, ko kwaskwarima da kokarin banbance Taijjaniyya da Qadiriyya daga 'Yan Hakika to ya rena hankulan mutane ne bayan ya rena nasa hankalin. Ai kowa ya ga almaran da suka bayyana a jiya, na cewa; Allan nasu Barhama ya bayyana a karfen wutan kan titi. Haka kuma duka wadanda ake kira 'Yan Hakikar sun bayyana a wajen bikin Maulidin da aka yi, musamman na Kaduna.
Don haka ta yaya za a ce akwai banbanci tsakanin Darikun Sufaye da 'Yan Hakika?!
Comments
Post a Comment