Akwai wata magana ta Ibnu Taimiyya wacce wasu suka samo, suke yadawa don daure gindi ma wata mummunar Akidar 'yan bidi'a, ta Guluwwi game da Annabi (saw), ta cewa an halicci Duniya ne don Manzon Allah.
To, asali 'yan bidi'a suna kafa hujja a kan wannar Akida ta Bidi'a ne da Hadisan da duka Hadisan karya ne, kamar yadda yake sananne a wajen Malamai, har shi Ibnu Taimiyyan ya tabbatar da haka.
Don haka sai suka samo wata magana ta Ibnu Taimiyya ake yada ta a matsayin shubuha, don a yi ilzami ma Wahabiyawa da ita. Alhali duk wanda ya yada wannar magana bisa wancan Maqsudi na 'yan bidi'a, to bai fahimci maganar Ibnu Taimiyya ba. Don abin da maganarsa take nufi shi ne:
Ibnu Taimiyya ya danganta hikimar halittar Duniya ne ga Annabi (saw) a babin FALALARSA A KAN MUTANE (الأفضلية), BA A BABIN KHUSUSIYYA (الخصوصية) BA. WATO BA ABU NE DA YA KEBANTA DA ANNABI (SAW) SHI KADAI BA. Ma'ana; bisa nazari cikin Ayoyin Alkur'ani za a ga cewa: Allah ya halicci halittu ne saboda mutane gaba daya, Annabi (saw) kuwa shi ne mafificin mutane. Don haka za a iya daukar maganar Sufayen bisa wannar ma'ana, saboda Annabi (saw) shi ne number one (1) a cikin mutane.
Don haka ma'anar maganar Ibnu Taimiyya ita ce: AN YI DUNIYA NE DON MUTANE GABA DAYA, amma Annabi (saw) shi ne a gaba. Don haka Annabi (saw) ne a gaba a cikin wannar hikima ta halittar Duniya, amma bai KADAITA DA ITA BA, sauran mutane ma sun yi tarayya da shi a cikin asalin hikimar, duk da cewa shi ya fi samun kamalarta. Ga maganar tasa kamar haka:
((ويمكن أن يفسر بوجه صحيح كقوله: {سخر لكم ما في السماوات وما في الأرض} وقوله: {وسخر لكم الفلك لتجري في البحر بأمره وسخر لكم الأنهار وسخر لكم الشمس والقمر دائبين وسخر لكم الليل والنهار وآتاكم من كل ما سألتموه وإن تعدوا نعمة الله لا تحصوها} وأمثال ذلك من الآيات التي يبين فيها أنه خلق المخلوقات لبني آدم...
...إذا كان أفضل صالحي بني آدم محمد وكانت خلقته غاية مطلوبة وحكمة بالغة مقصودة أعظم من غيره صار تمام الخلق ونهاية الكمال حصل بمحمد صلى الله تعالى عليه وسلم)).
مجموع الفتاوى (11/ 96 - 97)
Ya ce:
((وأمثال ذلك من الآيات التي يبين فيها أنه خلق المخلوقات لبني آدم...)).
((Da irin wadannan Ayoyi da Allah yake bayyanawa a cikinsu cewa: YA HALICCI HALITTU NE SABODA BANI-ADAM)).
Dalilai a kan haka su ne dukkan Dalilai da suke nuni ga DALILIN "INAYA" (دليل العناية), ma'ana; Allah yana kula da mutane, yana halitta musu ababen da suke bukata a cikin rayuwarsu, don su samu daman bauta ma Allah shi kadai.
Allah ya ce:
{الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الْأَرْضَ فِرَاشًا وَالسَّمَاءَ بِنَاءً} [البقرة: 22]
Ya ce:
{وَهُوَ الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ النُّجُومَ لِتَهْتَدُوا بِهَا فِي ظُلُمَاتِ الْبَرِّ وَالْبَحْرِ} [الأنعام: 97]
Ya ce:
{هُوَ الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ اللَّيْلَ لِتَسْكُنُوا فِيهِ وَالنَّهَارَ مُبْصِرًا} [يونس: 67]
Ya ce:
{الَّذِي جَعَلَ لَكُمْ مِنَ الشَّجَرِ الْأَخْضَرِ نَارًا} [يس: 80]
Ya ce:
{اللَّهُ الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الْأَنْعَامَ لِتَرْكَبُوا مِنْهَا وَمِنْهَا تَأْكُلُونَ} [غافر: 79]
Ya ce:
{أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللَّهَ سَخَّرَ لَكُمْ مَا فِي الْأَرْضِ وَالْفُلْكَ تَجْرِي فِي الْبَحْرِ بِأَمْرِهِ } [الحج: 65]
Ya ce:
{أَلَمْ تَرَوْا أَنَّ اللَّهَ سَخَّرَ لَكُمْ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ وَأَسْبَغَ عَلَيْكُمْ نِعَمَهُ ظَاهِرَةً وَبَاطِنَةً } [لقمان: 20]
Ya ce:
{وَسَخَّرَ لَكُمُ الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ دَائِبَيْنِ وَسَخَّرَ لَكُمُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ} [إبراهيم: 33]
Duka wadannan Ayoyi suna nuna cewa Allah ya halicci Duniya ne don mutane gaba daya.
Shi ya sa Ibnu Rushd ya ce: Alkur'ani ya yi nuni a kan cewa Allah ya halicci dukkan halittu ne don mutum:
((الطريق التي نبه الكتاب العزيز عليها، ودعا الكل من بابها، إذا استقرئ الكتاب العزيز وجدت تنحصر في جنسين: أحدهما: طريق الوقوف على العناية بالإنسان وخلق جميع الموجودات من أجله، ولنسم هذه دليل العناية)).
مناهج الأدلة في عقائد الملة (ص: ١٥٠)
Ya ce:
((... طريق الوقوف على العناية بالإنسان وخلق جميع الموجودات من أجله)).
((Hanyar sanin ba da kulawa da Allah yake yi wa mutum, DA HALITTAR DUKKAN HALITTU DON SHI)).
Kuma Ibnu Taimiyya ya nakalto wannar magana ta Ibnu Rushdi a litatafansa guda biyu, amma bai kore ta ko ya ci gyaranta ba. Saboda ya yarda da ita, don ta dace da Alkur'ani. Duba:
درء تعارض العقل والنقل (9/ 321)، بيان تلبيس الجهمية في تأسيس بدعهم الكلامية (2/ 160)
Saboda haka duk wanda ya kalli "Dalilul Inaya", wanda ake tabbatar da samuwar Allah Mahalicci da shi, da tabbatar da Rububiyyarsa zai ga cewa; ALLAH YA HALICCI DUNIYA NE DON MUTANE GABA DAYA. Saboda haka ba za a ce an halicci Duniya don Annabi (saw) shi kadai ba. Sai dai a ce an halicci Duniya ne don mutane gaba daya, Annabi (saw) kuma ya fi samun kaso mai girma, saboda ya fi sauran mutane falala da daraja.
Saboda haka, da wannan za ka fahimci cewa; ba dadai ba ne a kafa hujja da maganar Ibnu Taimiyya ba tare da bayanin cewa; bisa maganar Ibnu Taimiyya, sauran mutane ma don su Allah ya halicci Duniya.
Comments
Post a Comment