BURIN MANYAN MUTANE DA HIMMA MA'DAUKAKIYA A RAYUWA
Abu Nu'aim ya ruwaito a cikin "Hilya", da Ibnu Asakir a cikin "Tarikh", daga Abdurrahman Ibnu Abiz Zinad, daga babansa ya ce:
اجتمع في الحجر مصعب وعروة وعبد الله بن الزبير وعبد الله بن عمر، فقالوا: تمنوا، فقال عبد الله بن الزبير: أما أنا فأتمنى الخلافة، وقال عروة: أما أنا فأتمنى أن يؤخذ عني العلم، وقال مصعب: أما أنا فأتمنى إمرة العراق، والجمع بين عائشة بنت طلحة وسكينة بنت الحسين، وقال عبد الله بن عمر: «أما أنا فأتمنى المغفرة» قال: فنالوا كلهم ما تمنوا، ولعل ابن عمر قد غفر له".
حلية الأولياء وطبقات الأصفياء (1/ 309)، (2/ 176)، وتاريخ دمشق لابن عساكر (40/ 267)، (58/ 219)، وسير أعلام النبلاء ط الرسالة (4/ 141)، (4/ 431).
"Mus'ab da Urwatu da Abdullahi bn Zubair (ra) (duka su 3 'ya'yan Zubair bn Auwam (ra) ne), da Abdullahi bn Umar (ra) sun hadu a Hijru Isma'ila (a jikin dakin Ka'aba), sai suka ce: kowa ya fadi burinsa, sai Abdullahi bn Zubair (ra) ya ce:
"Amma ni Khalifanci nake buri".
Sai Urwatu ya ce:
"Ni kuma ina burin a dauki ilmi a wajena".
Sai Mus'ab ya ce:
"Ni kuma ina burin sarautar Iraqi, kuma in auri A'ishatu bnt Dalha, da Sukaina bnt Hussain".
Sai Abdullahi bn Umar (ra) ya ce:
"Amma ni kuma ina burin samun gafarar Allah ne".
Sai Abuz Zinad ya ce: kuma dukkansu kowa burinsa ya cika, ya samu abin da yake so, shi kuma Abdullahi bn Umar (ra) da fatan Allah ya gafarta masa".
Wadannan duka manyan mutane ne, mutum biyu a cikinsu Sahabban Annabi (saw) ne, su ne Abdullahi bn Umar (ra) da Abdullahi bn Zubair (ra), su kuma Urwatu bn Zubair da Mus'ab bn Zubair suna cikin Tabi'ai ne.
Dukansu 'ya'yan Zubair (ra) su uku kowa Allah ya cika masa burinsa a zahiri, saboda abin da suke buri abu ne da zai iya bayyana wa mutane a nan duniya.
Shi Abdullahi bn Zubair (ra) ya zama khalifa, daga baya aka kashe shi, Abdul Malik bn Marwan ya zama khalifa a bayansa.
Haka shi ma Mus'ab ya zama Gomnan Iraqi a lokacin khalifancin yayansa Abdullah bn Zubair (ra), kuma ya auri wa'dannan mata guda biyu, wadanda babu kamarsu a wannan lokaci, wajen kyau da daukaka a cikin mata, su ne A'ishatu 'yar Sahabi Dalhat bn Ubaidillah (ra), da Sukaina 'yar Sahabi jikan Annabi (saw) Husaini bn Aliyu bn Abi Dalib (ra).
Shi kuma Urwatu bn Zubair ya zama babban malamin hadisi a zamanin Tabi'ai, shi ya sa ba za ka iya iyakance sunansa a cikin littatafan hadisi ba, saboda yawan ruwaito hadisai.
Duka abin da ya gabata babbar alama ce da take nuna shi ma Abdullahi bn Umar (ra) Allah ya cika masa burinsa, saboda nasa burin ya fi girma da falala, kuma ya fi nuna bukatuwa zuwa ga Allah (T).
MU MA BABBAN BURINMU A DUNIYA SHI NE; SAMUN GAFARAR ALLAH DA YARDARSA. YA ALLAH KA CIKA MANA BURINMU.
Comments
Post a Comment