Ibnu Rushdi da magabatansa cikin 'yan Falsafa masu dangantuwa ga Muslunci, duk kokarinsu shi ne samar da daidaito tsakanin Falsafa da Muslunci (التوفيق بين الفلسفة والإسلام). Suka yi ta dauko Nassoshin Addinin Muslunci suna dora su bisa ma'ana ta Falsafa, wato ra'ayoyin su Aristotle.
To kamar haka, da na duba irin kokarin makarantar Shaikh Sharif Saleh, a cikin Tijjaniyya, sai na ga shi ne kokarin samar da daidaito tsakanin Sufanci da Addinin Muslunci (التوفيق بين التصوف والإسلام). Sun yi rubuce-rubuce don nuna Sufanci shi ne hakikanin Martabar "Ihsani" a cikin Addini, kamar yadda ya zo a Hadisin Jibril (as). Alhali duk wanda ya kalli hakikanin Sufanci, tun karni na 4 zuwa yau, zai tabbatar da cewa; Sufanci wani taron wasu Akidu ne da "Duqus" da aka harhado daga Falsafa da wasu Addinai, irin Kiristanci da Addinan India, kamar Addinin Hindu da Addinin Buda.
To wannan makaranta ta su Prof. Maqari, ganin yadda babu yadda za a yi mai hankali da imani, wanda ya fahimci hakikanin sakon Musulunci ya yarda cewa Sufanci Muslunci ne, wannan ya sa suke ta kokarin kwaskwarima ma wasu tarkacen da suke cikin Sufancin.
Amma idan kana so ka tabbatar da hakikanin Sufanci, musamman Tijjaniyya, to ka saurari irin su marigayi Shehu Maikano na Ghana, wato Baba kenan, da sauran shehunan Ghana, da irin su Dan-Anti a nan Nigeria.
Amma ni dai a fahimtata, kamar yadda Falsafa ba ta da gindin zama a Muslunci, duk da kokarin su Ibnu Rushdi na nema mata gindin zama, to haka shi ma Sufanci, a yadda yake a cikin littatafan shehunai, da yadda su Dan-Anti suke bayyana shi, babu yadda zai hadu da Addinin Muslunci.
Don haka muke kira ga makarantar Shaikh Sharif Saleh, dole ne sai sun fito sun yaki Tijjaniyya da gaske, don su Dan-Anti sun fito suna tona asirin Tijjaniyyar, kamar yadda take a bisa hakika.
Comments
Post a Comment