Ilimin Mantiq (Logic) ilimi ne da Malamin Falsafan nan na Kasar Girka (Greece) ya kirkiro, wato Aristotle, tun kafin haifuwar Annabi Isa (as) da kusan shekara 300. Saboda haka ne suke kiransa da Malamin Farko (المعلم الأول). Bayansa kuma sai Abu Nasr Al- Farabiy ya zo ya reraye shi, don haka suke kiransa da Malami na Biyu (المعلم الثاني). To bayan bacewar littatafan Farabiy sai Ibnu Sina ya zo ya tattaro shi daga abin da ya tsinta daga gare shi.
Shi ya sa Shaikhul Islami ya ce: wannar magana tana nuni a kan jahilcin mai ita game da Shari'a, da kuma jahilcinsa ga rashin fa'idar Mantiq din, balle kuma wanda ya ce: Farilla ne na aini. Bacin wannar magana abu ne sananne da ba ya bukatar wani nazari. Saboda ga nan Sahabban Manzon Allah (saw), su suka fi kowa cikan Ilimi da hankali da cikan Imani da hikima, alhali a cikinsu babu wanda ya san wani abu -wai- shi Mantiq. To don haka ta yaya za a ce: -wai- koyonsa wajibi ne, kuma har a ce: ba a aminta da ilimin mutum har sai ya san Ilimin Mantiq, ko a ce: da shi ake auna ilmomi?!
Sun fadi wannar magana ce fa alhali su 'Yan Falsafar ba su yi imani da abin da Allah da Manzonsa suka wajabta ko suka haramta na Shari'a ba, kuma shi malamin nasu Aristotle Mulhidi ne mai inkarin Addinai, amma a hakan za su zo suna wajabta wa mutane abin da Allah da Manzonsa ba su wajabta ba, kuma abin da Mulhidi ne ya kirkira, wanda ba shi da wata fa'ida ta a zo a gani.
Comments
Post a Comment