IRIN GULUWWIN INYAS A KAN SHEHU TIJJANI
DAGA INA MATSALAR TAKE ?(5)
A fitowa na hu'du na wannan rubutu mun fara kawo maganganun Shehu Inyass wa'danda acikinsu yake allantar da Shehu Tijjani , ta yanda yake jingina masa halittan halittu , da rayar da su , da gudanar da rayuwarsu , kamar yanda hakan dama abune sananne wurin Sufaye masu zurfafawa acikin sufanci suna 'kudurta hakan ga dukkan wanda suke 'kudurta walittakansa , a rubutunmu na farko da na biyu mun kawo maganganun Shehu Tijjani inda yake 'kudurce hakan .
Ga wata magana ta wani 'konannen Sufi Shehu Abdul Aziz Addabbag inda yake 'kara tabbatar da wannan al'amari .
Yana cewa :
" كل ما أعطيه سليمان في ملكه ، وما سخر لأبيه داود ، و أكرم به عيسى ، أعطاه الله تعالى و زيادة لأهل التصرف ( الأولياء) من أمة محمد ، فإن الله سخر لهم الجن و الإنس والشياطين و الريح والملائكة ، بل و جميع ما في العوالم بأسرها ، ومكنهم من القدرة على إبراء الأكمه و الأبرص و إحياء الموتى "
"Dukkan abunda aka baiwa Annabi Sulaiman acikin mulkinsa , da abunda aka horewa babansa Annabi Dawud , da abunda aka karrama Annabi Isa da shi , to Allah ya bawa Waliyyai masu jujjuaya al'amuran halittu ( 'Ku'dubai) na al'ummar Annabi Muhammad dukkan wa'dannan ababe har da ma 'kari akan haka .
Saboda su waliyyan Allah ya hore musu gudanar da Aljanu , da dukkan jinsi na Mutane , da gudanar da She'danu , da iska , da Mala'iku , kai da ma dukkan halittu da ke cikin dukkan duniyoyi baki 'dayansu , kuma Allah ya basu iko alan warkar da makafi , da kutare , da rayar da matattu "
(الذهب الإبريز ، ٤١٧)
Acikin wannan bayanai na wannan Sufi zamu ga cewa ya tattara komai ya baiwa waliyyai ; babu wani aiki da zakace akwai wani Allah daban da yake tsayuwa da su , a'a waliyyai sune suke komai , kamar dai yanda Shehu Tijjani ya ce _ kamar yanda muka kawo a rubutunmu na farko da na biyu _ : a duk inda Allah yake abun bauta , to wannan waliyyin shine yake a madadin Allah a wurin ; shine mai halittawa , shike kashewa , shike rayaswa , shike azurtawa , shike talautawa , duk wanda ya yi wata bauta to shi ya bautamawa !!
A yau zamu cigaba da kawo wani sashe na zantukan Inyass , inda acikinsu yake allantar da Shehu Tijjani kamar yanda a rubutunmu na baya muka fara kawowa .
Yana cewa : Dukkan arzi'ki da halittu suke samu daga gareshi ne , sawa'un arzi'kin wanda ake iya gani ne a zahiri , da ma wanda yake a 'boye , saboda hakane aka soyantar da Shehu Tijjani azuciyar halittu , wanda mu hakan garemu wajibine "
Ga nan maganarsa da lafuzzansa :
"فمنه ترى الأرزاق حسا و باطنا ## لذا حبب المكتوم فهو لنا فرض "
( طيب الأنفاس ، حرف الضاد )
A wani wurin kuma ya ce : waliyyai Arifai ( wa'danda suka gano cewa komai Allah ne ) da ma dukkan 'bangarori na waliyyai ; masu gudanar da halittu da sauransu , dukkansu arzi'kinsu yana hannun Shehu Tijjani ne , don hakan ina ro'konka da ka tsaftace zuciyata kuma ka goge min ita .
Ka cika min zuciyata da saninka , da kuma sanin sirrika da hikima , saboda ni na yi watsi da dukkan wani kishiya daga barinka , saboda haka kaima ka yi watsi da kowa sa'banin ni "
( طيب الأنفاس ، حرف الذال )
Acikin wannan magana tashi yana tabbatar da cewa hatta waliyyan da suke gudanar da halittu _ a bisa 'kudurinsu _ , to suma Shehu Tijjani shine ke gudanar da su , wato shine Ogan kowa da kowa kenan ; su dukkan halittu mutane da Aljannu , da Mala'iku da Dabbobi da tsirrai da sama da 'Kasa da komai da kowa , dukkansu suna 'kar'kashin wa'dannan waliyyai , shi kuma Shehu Tijjani yana saman wa'dannan Waliyyan yana sarrafasu !!
Da ya zama wannan shine 'kudurinsa _ duk da cewa shima yana ganin halittun duniya a 'kar-kashin gudanarwassa suke , kamar yanda zamu yi rubutu akan haka a rubutunmu da zasu zo nan gaba _ sai ya zage yana addu'a na neman bu'kata zuwa ga Shehu Tijjani tuddan shine babban Allah cikin Alloli masu yawa !!
A wani wurin kuma cewa ya yi : Da albarkatun Shehu Tijjani dukkan Mutane da Aljannu suka rabauta "
Ga nan maganarsa kamar haka :
"بفيضك فاز الإنس و الجن كلهم "
( طيب الأنفاس ، حرف النون )
A wani wurin kuma ya ce : Shehu Tijjani shine masoyina , shine wanda albarkatunsa suka game dukkan 'kasa ta Allah , Shehu Tijjani shine maka'daici matattarin komai "
Ga nan maganarsa :
"حبيبي أبو العباس من عم فيضه ## جميع بلاد الله فالفرد جامع "
( طيب الأنفاس ، حرف العين )
A wani wurin kuma cewa ya yi : Shehu Tijjani shine yake tafiyowa da kowa abunda yake buri , kuma shine yake tausasawa ga halittu "
Ga nan maganar tasa :
" وللشيخ تيسير المنى و التلطف "
( طيب الأنفاس ، حرف الفاء )
A wani wurin kuma ya ce : Daga Shehu Tijjani ne nake samun rabautuwa , kuma shine yake bani riba , kuma shike biya mini burace _ buracena , kuma shine yake tseratar da zukata , kuma shine yake samar da jin da'di ga halittu "
Ga nan maganarsa :
"فمنه أنال الفوز و الربح و المنى ## و منه نجاة النفس ، منه الرفوه "
( حرف الهاء )
Da yake Inyass ya riga ya 'kudurta cewa dukkan al'amura na halittu suna hannun Shehu Tijjani ne , hakan ya sa a wani wuri sai yake ro'kon Shehu Tijjani da ya ke'beshi daga sauran halittu ta yanda zai maida duka dararensa ( Inyass) su zama ranar juma'a a gareshi , saboda Shehu Tijjani shine mai iko akan komai , kuma dukkan nasara daga gareshi take .
Ga nan maganarsa kamar haka :
" فصير ليالي جمعة دون كلفة ## فإنك سلطان ومنك نجاح "
( طيب الأنفاس ، حرف الحاء)
A wani wurin kuma cewa ya yi : Shehu Tijjani shine ruhin dukkan halittu , kuma shine turkensu ( shi ke ri'ke da su ) , kuma shine mai azurtasu . Shine makai'daici kamar yanda kakansa Annabi Muhammad ya ka'daitu "
Ga nan maganarsa :
"روح الوجود و قطبهم و ممدهم ## كا لجد طه المصطفى بتفرد "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١١٤)
A wani wurin kuma ya ce : Shehu Tijjani shine ruhin dukkan halittu baki 'dayansu ; dukkan Mutane sun shiga cikin hakan , sawa'un masu 'dabi'ar nufatan ayyukane , da ma masu tsururutan ayyakan "
Ga nan maganarsa :
" و أنت الروح للكون جملة ## فسيان همام ومن كان حارثا "
( طيب الأنفاس ، حرف الثاء)
Wa'dannan maganganu na Inyass duka sun 'kunshi 'kudurinsa dangane da Shehu Tijjani na allantar dashi ta hanyar jingina masa dukkannin ma'ana ta ubangijintaka ( Rububiyyah ) ; halittawa , gudanar da al'amura da mallaka da kashewa da rayaswa ...
A rubutunmu na gaba zamu kawo maganganunsa inda acikinsu ya ke tabbatarwa 'karara cewa Shehu Tijjani shine Allah .
Rubutawa Malam Abu Ahmad Ateeq.
Comments
Post a Comment