Skip to main content

 IRIN GULUWWIN INYAS A KAN SHEHU TIJJANI

DAGA INA MATSALAR TAKE ?(4)
A rubutunmu na baya mun yi bayanin ha'ki'kanin 'kudurin Shehu Inyass na 'kudurcewassa ga allantuwar wasu halittu da ma allantuwar komai , ta yanda yake dacewa da Shehu Tijjani acikin wannan 'kuduri . A wannan rubutun kuma zamu kawo wani sashe ne na maganganunsa inda yake allantar da Shehu Tijjani ta hanyar jingina masa ubangijintaka ; na jujjuya al'amuran halittu , da rayar da su , da azurtasu , da shigar da su wuta ko Aljanna .
Idan ba mu mantaba mun kawo maganganun Shehu Tijjani a rubutunmu na farko da na biyu a 'kar'kashin wannan matashiyar (DAGA INA MATSALAR TAKE ) , inda yake tabbatar da cewa Waliyyi Halifa shike halittan halittu , kuma shike rayar dasu , kuma shike a madadin Allah a wurin dukkan halittu . To wannan matsayi da Shehu Tijjani ya ajiye wannan waliyyin akansa shine matsayin da Inyass ya ajiye Shehu Tijjanin akansa shi yasa ya jingina masa dukkan wa'dannan ayyuka na ubangijintaka .
Ga maganganunsa nan kamar haka :
" واصطراف الإمام كان عميما ## فيه عمري الخضراء و الغبراء
كم أتى بالغيث المريع ببجدب ## سودت من محولها الخرقاء "
" Jujjuyawar Shehu Tijjani ga al'amuran halittu gamamme ne ; na rantse muku korayen tsirrai da busassu duk suna cikin gudanarwassa .
Sau da yawa yana saukar da mamakon ruwan sama a 'kasar da tayi ba'ki saboda fari "
(جامع الدواوين ، تحفة أطايب الأنفاس : ٩٧)
A wani wurin kuma ya ce : al'amuran dukkan halittu suna cikin tafin hannun Shehu Tijjani ne ; shine yake gudanar da iska mai ni'ima ga mutane , kuma shike jarabtarsu da iska mai 'dauke da guba .
Ga nan maganarsa kamar haka :
"أمر كل الوجود في كف شيخي ## منك ريح السموم منك النسيم "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١٠٢)
A wani wurin kuma yake cewa : duk abunda Shehu Tijjani ya nufaci faruwarsa to nan take abun yake faruwa .
Ga nana maganarsa kamar haka :
"أنتم مهما تشاؤو ## نه يكن كل بادي "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١٢٥)
A wani wurin kuma yake cewa : tun sanda Shehu Tijjani ya kasance to shine yake azurta dukkan halittu .
Ga nan maganarsa anan :
" أبو العباس مذ كانا ## ممد الكل تجاني "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١٢١)
A wani wuri kuma ya ce : Daga Shehu Tijjani ne dukkan alheri suke kwararowa , kuma duniya gaba 'dayanta tana cikin dam'karsa ne , kuma shine yake bayarwa ga wanda yaga dama , kuma shike hanawa ga wanda yaga dama.
Ga kalmominsa nan kamar haka :
" فمنه يفيض الفيض و الكون قبضة ## له منه منع إن يشأ و عطاء "
( طيب الأنفاس ، حرف الهمزة )
Wannan al'amari na azurta dukkan halittu da Inyas ya ce Tijjani ne yake yi , zaka samu kusan dukkan Malaman Tijjaniyya da sukayi rubutu akan Tijjaniyya duk sun tabbatar da hakan ; cewa Tijjani ne yake azurta halittu tun farkon halittan duniya har zuwa tashin duniya shine yake 'dauke da ciyarwa da shayarwa da gudanar da dukkan halittu hatta tsirrai da 'kwari dukkansu arzi'kinsu yana a hannunsa .
Shaikh Muhammad Nazifi ya fa'di haka tun a mu'kaddimarsa a littafinsa "ya'kutatul faridah " , yana cewa :
" و إني كنيته أبا الفيض إنه ## يمد جميع العالمين بفيضه
من أول نشأة العوالم كلها ## إلى النفخ يسقي كل فرد و ذرة "
( الياقوتة الفريدة ، ٢)
Ga nan shima Inyass ya 'kara da cewa :
"ممد الأقطاب من بدء الخلائق ل ## لأخرى به نال أصغار و كبار
لذا لهذا أنت في نعم ## كما يقول لهذا دارك النار "
Shehu Tijjani shine yake azurta dukkan waliyyai 'kudubai ( sune waliyyan da sufaye suke cewa _wai_dukkan halittu a 'kar'kashin kulawarsu suke ) , daga wurinsa manya da 'kananansu kowa yake samun rabonsa . Kuma ya tsayu da wannan al'amari tun daga farkon fara halitta har zuwa tashin 'kiyama .
Saboda hakane idan yaga dama sai ya ce ga wannan : kai aljanna zaka shiga " , kamar yanda kuma zai ce da wancan : kai kuma wuta zaka shiga "
(تحفة أطايب الأنفاس ، ٨٦)
A wani wurin kuma ya ce :
" ومنه استمد الكل من سائر الناس "
"Daga Shehu Tijjani ne dukkanin Mutane suke samun arzi'kinsu "
(طيب الأنفاس ، حرف السين )
A wani wurin kuma cewa ya yi : a ranar 'kiyama bayan an tattaro dukkan halittu a farfajiyar 'kiyama , sai Shehu Tijjani yazo akan mimbari na haske , sai wani mai shela ya shelantawa dukkan halittun da suke filin 'kiyama cewa : Shehu Tijjani shine mai azurtaku kuma shine mai kiyayeku "
Ga nan maganarsa kamar haka :
" بمنبر النور يؤتى الشيخ منقذنا ## يوم القيامة يرقى دون مريات
فعند ذا ينادى ذاك قدوتكم ## ممدكم بفيوضات العنايات "
( تحفة أطايب الأنفاس، ٨٢)
Hakanan yana cewa : dukkan al'amuran halittu suna hannun Shehu Tijjani ne , saboda haka shine ya zantar da faruwan dukkan ababen da suka gabata , kuma ba zai gusheba yananan yana zantar da gudanar komai .
Ga zancen nasa nan :
"لشيخي تصريف و نعم المصرف ## مضى منه ما يمضي و دام التصرف .
فالأمر له إذ يضارع جده ## ومصدر أمداد له و التعرف "
( طيب الأنفاس ، حرف الفاء )
A wani wuri kuma ya ce : Shehu Tijjani shine wanda yake amadadin Allah , kuma shine ruhin dukkan halittu , kuma shine ma'kagin dukkan halittu .
shine yake sanya wal'kiya ta haskaka , kuma shike sanya tsawa ta yi rugugi , kuma shike saukar da ruwan sama , kuma shike tsamo halittu "
Ga zancen nan nasa da haruffansa :
" خليفة الله رمز الكون روح جمي ## ع الخلق و هو لأصل للوجودات
مبرق البرق و مرعد الرعود و ممط ## ر المزون و منقاذ البريات "
( طيب الأنفاس ، حرف التاء )
Ya nanata cewa Shehu Tijjani shike rayar da halittu a wurare mabanbanta a cikin wa'ko'kinsa , a wani wurin ga abunda yake cewa :
"إمام جواد ناصح و هو واهب ## يهب و يعطي منه عاش عائش "
"Shehu Tijjani shine jagora mai kyauta , mai ingantawa , kuma shine mai bayar da baiwa , kuma shine mai bayarwa , duk wanda kaga ya rayu to daga gareshi ne ( shine ya rayar da shi ) "
(طيب الأنفاس ، حرف الشين )
A wani wurin kuma ya ce : jiragen ruwa da sansani na duniya dukkansu daga Shehu Tijjani suke ( shine ya halittasu )
Ga nan maganarsa :
كتمت في حضرات الحق ليس سوى ال ## مختار يدريك لا إنس و لا ملك
لكن تجليت للأكوان جملتها ## إذ أنت أنت و منك الفُلْكَ و الفَلَكُ "
( طيب الأنفاس ، حرف الكاف)
A dukkan wa'dannan maganganu na Inyass yana tabbatar da cewa ; dukkan abunda kake gani na halittu masurai da marasa rai , manyansu da 'kanana , duniya gaba'dayanta da halittun da suke cikinsu , dukkansu Shehu Tijjani ne ya haliccesu , kuma shike gudanar da su .
A wani wurinma ya 'kara da cewa : Shehu Tijjani shine Ruhin Allah ( wato rayuwar Allah tana a hannunsa , iyazan billah !! ) , ga nan maganarsa kamar haka :
" و هو الجامع الذي يجمع الأنوا ## ر و هو الخليل وهو الكليم
و هو روح الإله و حبيب ## الله عمري ما حاز هذا أريم "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١٠١)
Arubutunmu na gaba zamu cigaba da Kawo irin wa'dannan miyagun zantuka nasa wa'danda suka 'kunshi allantar da Shehu Tijjani ta hanyar danganta masa ubangijintaka ; halittawa da gudanarwa da azurtawa ga halittu .
zamu yawaita Kawo irin wa'dannan maganganu daga gareshi domin mutane su tabbatar cewa lallai fa da gangan yake fa'din maganganun , kuma abunda yake 'kudurtawa kenan har zuciyarsa.
Rubutawa Malam Abu Ahmad Ateeq.

Comments

Popular posts from this blog

Magungunan Musulunci Fitowa Ta farko

HABBATUS-SAUDA: Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa. FA'IDOJINTA: Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki. Tana vuvvugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu. Tana maganin kuturta. Tana amfani wajen rage majina. Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura. Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar. Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma. Hakanan mun tato sinadaranta mun zuba a wani magani mai suna (TASIRI DAGA ALLAH), don haka za ku iya neman wannan magani. ARRAIHAN/XOXXOYA Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America. Allah (S.W.T) yana cewa: " ﻓﺄﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺮﺑﻴﻦ * ﻓﺮﻭﺡ ﻭﺭﻳﺤﺎﻥ ﻭﺟﻨﺔ ﻧﻌﻴﻢ " Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare sh...

amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan

  MAGANIN RIKICEWAR JININ HAILA : TAMBAYA TA 2282 ******************* Assalam, malam dan Allah sakaye sunana. Yaya aiki? Malam nice nake amfani da maganin tazarar haihuwa wato implan yanzu wata na hudu kenan, to kwanan nan se ya fara min wasa da al'ada ta, se nayi sati biyu ya dawo wannan karon kam ma bekai sati daya ba ya dawo, naga yadan zubo se kuma ban gani ba kuma a wannan rana ina azumi shin malam menene hukuncin sallah ta da azumi na? Shin wannan jini ya zama na ciwo ne ko kuma? Domin an bani magani a asibiti domin ya gyara min. Malam ayi hakuri zanso a tura min amsar ta nan. Nagode. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Su kwayoyi ko alluran tazarar haihuwa sukan yi kokarin chanza yanayin halittar Mace ne daga ainahin ginin farko wanda Ubangiji ya halicceta akansa. Don haka dole arika samun matsaloli marassa adadi. Mafiya yawan Matayen dake shiga wannan tsarin sai, sun sha fama da rikicewar jinin Al'ada. Wasu ma ciwuka da jinyoyi kala-kala a sassa...

Haila

  Haila Bayanin menene haila Kalmar (Haila) a larabci Tana nufin Kwararar wani abu da gudanar shi Ma’anar (Haila) a shari’a Wani jini ne da yake fita daga mahaifar mace, a wasu lokuta sanannu, ba tare da wani dalili ba. Siffar Yadda Jinin Haila Yake Baqi ne wuluk, kamar wanda aka qona, warinsa bai da daxi, mace tana jin xumi mai tsanani idan ya zo. Shekarun Fara Jinin Haila Babu wasu shekaru qayyadaddu na fara al’ada, wannan ya danganta ne da savanin xabi’ar mace da inda take rayuwa da yanayin wajen, don haka duk lokacin da mace ta ga jinin haila to haila ce. Tsawon Lokacin Haila Haila ba ta da wani lokaci, sananne, cikin mata akwai masu yin kwana uku, akwai masu kwana huxu. Galibin haila dai kwana shida ne ko bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Hamnatu ‘yar Jahshin – wanda ta kasance tana yin haila kwanaki masu yawa –  “Ki yi haila kwana shida, ko bakwai, da ilimin Allah, sannan ki yi wanka”  [Abu Dawud ne ya rawaito shi] Mas'aloli 1 - A qa'ida ma...