IRIN MUNANAN MAGANGANUN INYAS IBRAHIM KAULAHA
DAGA INA MATSALAR TAKE ?(3)
A rubutunmu na farko da na biyu mun yi bayanin yanda a'kidar allantar da wasu halittu da ma allantar da dukkan komai take da asali acikin 'dari'kar Tijjaniyyah , ta hanyar kawo wani sashe na zantukan Shehu Tijjani wa'danda acikinsu yake tabbatar da wannan munanan a'kidu na kafirci .
zamu kasa zantukan Inyass akan wa'dannan miyagun a'kidu zuwa kamar haka :
- maganganunsa akan yiwuwar allantuwar bawa
- maganganunsa akan allantakar komai
-maganganunsa akan allantakar ShehuTijjani .
A wannan rubutun zamu tattauna ne akan matashiya biyu na farko , a rubutunmu na gaba kuma sai mu tattauna akan matashiya na 'karshe .
Shehu Ibrahim ya gudana a magudana na manya _ manyan jagorori na addinin allantar da halitta cikin Sufaye da waninsu , ta yanda yake 'kudurce cewa lallai bawa yakan iya 'ketare matsayi na bautantaka sai ya haye matsayi na allantaka ; ta yanda shi zai ha'de da Allah saboda tsananin bauta , ko kuma Allah ya sauko cikin jikinsa sai ya zama Allah .
Yana cewa :
" هل الله عاجز أن يتكلم على لسان ناطق فيقول على لسانه : أنا الله ؟ إذا غاب العبد عن كل الموجودات ، وتجلى الحق فيه وصار لسانه الذي ينطق به ، و يده التي يبطش بها و سمعه الذي يسمع بها و بصره الذي يبصر بها و رجله التي يمشي بها : الله ينطق على لسان هذا : أنا الله " ، ليس الإنسان هو المتكلم ، وليس الإنسان هو الله ، إنما الله هو المتكلم . و هذا غاية التوحيد ، من وصل إلى هذا المقام برئ من الشرك تماما . وقبل هذا عبد لم يخلص من الشرك "
( توسعة العرفان ، ٨)
Acikin wannan zance Shehu Inyass yana tabbatar da cewa lallai akwai wani yanayi da bawa zai shiga wanda Allah zai bayyana acikin jikin wannan bawan har ya zama Allah zai ringa magana a bisa harshen wannan bawa , kamar dai yanda muke gani aljani yana bayyana ajikin 'Dan Adam ya ringa magana a bisa harshensa .
Sannan kuma ya 'kara da cewa ; duk wanda ya kai ga wannan mataki to shine ya dace da cikakken Tauhidi ya rabu da shirka .
A wurin su Ibrahim Inyass da magabatansa akan wannan addini na allantar da halitta ,kamar su : Al'afif ( Alfajir ) Attilmisany , Ibnul Farid , Ibnu Araby Alhatimy , Shailh Ahmad Attijany ; duk wanda yake gani akwai banbanci tsakanin Allah da halitta to wannan Mushriki ne , Tauhidi a wurinsu shine ka 'dauki komai a matsayin Allah !!
Saboda hakane suke aibanta tauhidin da Annabawa suka tabbatar da shi na bauta da bawa zai yi ga mahaliccinsa shi ka'dai , sai suke kiran wannan tauhidi da cewa : tauhidin gama_gari ; saboda shi wannan tauhidin yana rabewa tsakanin mai bauta da wanda ake bautamawa . Su a wurinsu kowa Allah ne .
Shehu Ibrahim ya fayyace 'karara cewa dukkan wanda baya ganin cewa komai Allah ne to babu shakka mushirikine , kuma irin wannan shirka it ace mafi 'boyuwar shirka wacce ba kowa yake ganeta ba . mai Tauhidi shine wanda ya ha'de dukkan halittu wuri 'daya ya 'daukesu a matsayin ababen bauta !!
yana cewa alokacin da yake bayanin matakai na shirka :
" و شرك أخفى : من يرى غير الله تبارك و تعالى . و بالحقيقة لا شيئ غيرالله "
" Akwai shirka mafi 'boyuwa : itace wanda yake ganin wani abu sa'banin Allah . Maganar gaskiya itace : babu wani abu wanda ba Allah ba "
( توسعة العرفان ، ٥)
A wani wurin kuma yana magana akan lafazin kabbara " الله أكبر " ( Allah shine mafi girma ) , sai yake cewa : Gama_garin mutane sune suke ganin hakan ( cewa Allah shine mafi girma akan komai ) , amma su ke'bantattu wa'danda suka san Allah su basa fa'dan haka , saboda su awurinsu komai Allah ne ; don haka babu maganar ma ace Allah shine mafi girma akan komai , saboda ai babu abunda ba Allah ba !!
Ga maganarsa kamar haka :
" أما العارفون فلا سوى عندهم حتى يكون الله أكبر كنه "
"Amma su masana Allah ai su basa ganin akwai wani abu wanda ba Allah ba ballantana kuma ace wai Allah ne mafi girma sama da komai "
( توسعة العرفان ، ١٠)
Inyass ya 'kara tabbatar da wannan mummunan a'kida a matsayin itace tsantsan Tauhidi , ga shi nan yana cewa :
" الله قادر على أن ينطق بلسان آدمي : أنني أنا الله . و إذا حصل الفناء عرف العبد ألا شيئ إلا الله تبارك و تعالى ، فهناك التوحيد الخالص الذي هو مطلب الرجال "
" Allah mai iko ne akan ya yi magana ta harshen Mutum sai ya ce : Nine Allah " .
Idan fana'i ya samu ga bawa ( saukowan Allah acikin jikin bawa ) , to bawan zai gane cewa babu wani abu wanda ba Allah ba . To anan ne bawa zai samu tsarkakakken tauhidi , kuma irin wannan tauhidinne mazaje suke nema "
( جواهر الرسائل : ٦٠/٣)
Anan Inyass ya tabbatar da abubuwa uku :
caku'dewar Allah da bawansa ; wanda hakan shine hanyar da bawa zai kai ga ganin komai a matsayin Allah , sai kuma 'daukan hakan a matsayin tsantsan tauhidi .
A wani wurin ya 'kara tabbatar da cewa lallai fa Allah yana bayyana acikin sifa ta 'Dan Adam , yana cewa :
" بل ربما يكون رب العلمين في صفة رجل "
( جواهر الرسائل ، ١٠/٢)
Inyass ya kawo maganar Tijjani domin ya 'karfafi maganarsa akan cewa tauhidi shine 'daukan komai a matsayin Allah , sannan kuma Allah yana bayyana acikin jikin halittu .
Ga nan maganarsa kamar haka :
" الشيخ التجاني يقول في جواهر المعاني : حقيقة التوحيد لا تدرك ، لأنك ما دمت تقول موجود و الله موجود فثَمّ اثنان ، أين التوحيد ؟
Ha'ki'kanin tauhidi ba'a iya ganeta ; saboda matsawar kana ganin cewa akwai wasu halittu samammu daban , sannan kuma akwai Allah samamme daban , to kenan akwai ababe biyu kenan , to ina tauhidin yake ? "
(جواهر الرسائل ، ٦٠/٢)
Shehu Ibrahim ya yayata wannan a'kida tasu ta 'daukan komai a matsayin Allah a wurare masu yawa acikin littattafansa kamar yanda muke ganin misali akan haka cikin wa'dancan maganganu nasa , ga nan wasu zantukansa da yake 'kara tabbatar da hakan :
" و الكون حقيقة ما فيه شيئ إلا الله تبارك و تعالى "
"maganar gaskiya it ace : babu komai a duniya sai Allah "
(جواهر الرسائل ، ٥٨/٢)
Hakanan yana cewa :
" ما لم يفن العبد في ذات الله تبارك وتعالى لم يكمل إيمانه "
"matu'kar bawa bai 'kare ba acikin zatin Allah ba , to imaninsa ba zai cika ba "
( جواهر الرسائل ، ٥٩/٢)
Wa'dannan maganganu na Inyass dukkansu sauna tabbatar da a'kidarsu ta allantakar dukkan halittu da 'daukan hakan a matsayin tsantsan tauhidi , tare da 'daukan dukkan wanda yake 'kudurce banbanci tsakanin Allah abun bauta da halittu bayi masu bauta , a matsyin mushrikai mahajubai gama-gari .
A rubutunmu na gaba zamu kawo maganganunsa wanda acikinsu yake allantar da Shehu Tijjani.
Rubutawa Malam Abu Ahmad Ateeq
Comments
Post a Comment