Kamar yadda Addinin Muslunci yake matsakaici a tsakanin Addinai, haka Mazhabar Salaf Ahlus Sunnati wal Jama'a yake matsakaici a tsakanin sauran kungiyoyi. Salaf Ahlus Sunna a tsakiya suke a dukkan babuka na Addini.
Salaf Ahlus Sunna matsakaita ne a babin Tauhidi, tsakanin masu guluwwi da masu jafa'i.
Haka a babin matsayin Manzon Allah (saw), tsakanin masu guluwwi da masu jafa'i, da tsakanin masu sakaci (tafridi) da masu zakalkalewa (ifradi).
Haka a babin raddi ga 'yan bidi'a, sun kasance tsakanin masu guluwwi da jafa'i, da kuma masu sakaci da tafridi.
Haka suke a tsakiya a kowane babi. Wannan shi ne WASADIYYAR AHLUS SUNNA.
Saboda haka idan za ka yaki guluwwin Sufaye a game da Annabi (saw), to wajibi ne ka girmama Annabi (saw), bai halasta ka yi jafa'i wa Annabi (saw) ba, da sunan raddi wa guluwwi.
Idan za ka yi raddi wa 'yan bidi'a bai halasta ka zalunce su ba, ko ka yi amfani da irin uslubinsu na cin zarafi. Saboda ka'idar Ahlus Sunna ita ce: ba ya halasta ka yi raddin barna da barna. Ana raddin barna ne da gaskiya da ilimi da adalci, ba da jafa'i da wauta da jahilci ba.
Saboda haka, duk wanda ya fito da sunan bin Sunna, yana jafa'i, da aikin wauta da jahilci, to ba hanyar Salaf yake bi ba, kawai jahilcinsa yake yi, amma yana zaton kyakkyawan abu yake yi. Balle wanda zai yi jafa'i wa Annabi (saw), da sunan kare Tauhidi, ko raddi wa 'yan bidi'a, ko raddi wa guluwwi game da Annabi (saw).
Akwai wasu matasa guda biyu da suka shahara da rashin mutunci wa mutane a social media da sunan bin Salafiyya, har suka isa ga jafa'i wa Annabi (saw), lallai abin da suka yi abin Allah wadai ne.
Abin da suka yi ya zama jafa'i ne saboda rashin ladabi wa Annabi (saw) da gangan, don cusa haushi wa mutane. Alhali kowa ya san dukkan abin da Allah ya kore wa Annabi (saw) a dunkule ne, don ya yi nuni ga ladabi. Allah ya kore masa sanin gaibi, da mallakar amfanarwa da cutarwa, ya gargade shi a kan shirka. Amma duka a dunkule, ba tate da kaskantarwa ba. Amma su kuma sun zo suna Tafsili mai dauke da rashin ladabi da kaskantarwa. Har dayansu yake cewa: Annabi ko sule biyar ba shi da shi a duniya da lahira!
Me ya sa ba ka takaita a kan lafuzan Nassoshin ba, ta hanyar girmamawa?
A takaice, wannan salo na raddin barna da barna hanya ce ta 'yan bidi'a, ba shi da alaka da hanyar Salaf. Kamar yadda yin abu don cusa wa mutane haushi yana daga cikin aikin banza da bawa zai yi hasararsa. Balle kuma jafa'i wa Annabi (saw), wannan kam ya fi muni a kan guluwwin masu guluwwi.
Don haka Manhajin wadancan fandararru guda biyu, wadanda suka mayar da wauta da jahilcinsu ya zama shi ne Manhajin Salafiyya, Manhaji ne na 'yan bidi'a, da wajaba a yake shi.
Saboda haka Manhajin Ahlus Sunna game da Annabi (saw) Manhaji ne matsakaici, tsakanin guluwwin Sufaye da jafa'in wadannan mabarnata da sunan Salafiyya.
Comments
Post a Comment